8 -13 n i a muslinci

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

8 -13 n i a muslinci

from nuramuhd3 on 04/02/2015 10:14 AM

NEMAN ILIMI A MUSULUNCI8yake gabaninsa kuma sau biyu, wanda yake kafin shi kuma sau ]aya, domin wannanshi zai sa ya haddace sosai.Kuma ya kamata kar ]alibi ya samu yankewa wajen karatu, saboda wannan yana jawomatsala warin neman ilimi, ya cigaba da cewa malaminmu Burhanuddin yana cewa:na samu rinjaye akan abokaina saboda ni ban ta~a yankewa ba wurin neman ilimi. (37)Kuma Hammad bin Ibrahim Al-ansari yana cewa:أخدم العلم خدمة المستفید وأدم درسھ بفعل حمیدوإذا ما حفظت شیئا أعده ثم أكده غایة التأكیدكي لایزول ثم علقھ كي تعود إلیھ وإلى درسھ على التأبیدMa’ana: Ka yiwa ilimi hidimar mai amfana, ka dawwama wurin yin karatu da aiki abingodewa. Idan ba ka haddace abu ba ka maimaita shi, sannan ka}arfafa shi mutu}ar}arfafawa. Don kar ya gushe, sannan ka rubuta shi don ka dawo zuwa gare shi har abada.(38)6. JURE WAHALA DA KUMA HA{URI.Neman ilimi ba ya yiwuwa sai da wahala kuma duk wanda ba zai iya jure wahalaba, zai yi wuya ya iya neman ilimi yadda ya kamata, dole]alibi sai ya yi ha}uri dasanyi da zafi da damina, da halin malaminsa, saboda zai iya yiwuwa ya ha]u damalami mai fa]a, ko wata rana ya je bai same shi ba, ko ya da]e yana jiransa,kuma sai yayi ha}uri da talauci, saboda neman ilimi ba zai bar shi ya nemi ku]iyadda ya kamata ba, har ma}ila ya ga sa’oinsa sun fi shi wadata, to amma idan yayi ha}uri sai ka ga Allah (s.w.t.) ya ]aukaka shi,]aukakar da tafi ta mai }u]i damai sarauta, IBNUL JAUZI (39) ya fa]a a cikin littafin Saidul kha]ir cewa yanatuna lokacin da yake neman ilimi da kuma wahalar da ya sha, har sai da ya kaicewa yana zama a bakin}orama da wainarsa yana jikata yana ci saboda ta bushe,yana yi yana shan ruwa, wasu kuma mutanansa suna neman ku]i, yake cewa gashi yanzu na yi ilimi, kuma nafi su daraja da alfarma a wurin mutane, kumarayuwata tafi rayuwarsu. (40)Kha]ibu Albagdadi ya fa]a a cikin tarjamar Bukhari cewa: (umar bin Hafs Alash}ar ya ce sun ta~a neman Bukhari kwanaki da yawa a basara suka rasa shi,-alokacin sun je nemam iliminhadisi- sai suka same shi a wani gida tsirara duk abinda yake da shi ya }are, sai muka tara masa ku]i muka sai masa tufa ya rufeal’aurarsa, sannan mu ka cigaba da neman hadisi) (41)Kuma Imamu al-bukhari yana cewa (na ta~a fita zuwa Adam bn Iyas a As}alan saiku}ina su ka }are har na koma ina cin ciyawa, ba kuma wanda na bawa labari, arana ta uku, sai wani ya zo yabani jakar dinare, ya ce ka ciyar da kanka dawannan) (42)(37) duba Ta’alimil muta’alim na Zarnuuji tah}i}in Marwan {ubani 101(38) duba Ta’alimil muta’alim na Zarnuuji tah}i}in Marwan {ubani 102(39) yana ]aya daga cikin manyan malaman musulunciwa]anda ba wanda ya ka su yawan rubucerubuce,ya mutu a shekara ta 597 H.(40) Duba saidu alkha]ir shafina 150-151(41) Duba tarik bagdad na kha]ib Al-bagdadi 213 da kuma khu]wat ilassa’adah 72-73(42) Duba [aba}at Asshafiiya 2227 da kuma khu]wat ilassa’adah 73NEMAN ILIMI A MUSULUNCI9Kuma malamai suna cewa –yawanci- gwargwadon wahalar da mutum ya shagwargwadon ilimin da zai samu, kamar yadda wani malami yake cewa:بقدر الكد تكتسب المعالي ومن طلب العلا سھر اللیاليتروم العلى ثم تنام لیلا یغوص في البحر من طلب اللآليومن رام العلى من غیر كد أضاع العمر في طلب المحالMa’ana: Da gwargwadon wahala ake samun daukaka, duk wanda ya nemi ]aukaka saiya raya darare. Kana neman ]aukaka amma kake bacci da daddare? Ai duk wanda yakke sonlu’ulu’u dole sai ya yi nitso a cikin ruwa. Duk wanda ya nemi]aukaka ba tare da wahala ba,to ya ~ata rayuwarsa wurinneman abin da ba zai yiyu ba. (43)Wani kuma yana cewa:أرى لك نفسا تشتھي أن تعزھا فلست تنال العز حتي تذلھاMa’ana:Na ga kana sha’awar ]aukaka kanka, to ba za ka samu]aukaka ba har sai ka}as}antar da kanka.Wasu suna cewa, ilimi]aukaka ne ba }as}anci a cikinsa, amma ba’a samunsa sai da}as}ancin da ba ]aukaka a cikinsa.FARAWA DA ABIN DA YA DACE DA [ALIBI[alibi ya fara da matakin da ya dace da shi wurin neman ilimi abu ne maimahimmacin gaske, saboda idan ya fara littafin da ya wuce matakin karatunsa, bazai fahimce shi sosai ba, kamar yadda malamai su ke cewa: WANDA BAIKYAUTATA TUSHE BA, TO ZA A HARAMTA MASA ISA INDA YAKE SOYA KAI, (44) wasu kuma sunacewa: DUK WANDA YA NEMI ILIMI TASHI[AYA, SAI ILIMI YA TAFI YA BAR SHI TASHI [AYA.(45)Babban malamin nan Bakr Abu-zaid yana cewa: neman ilimi ya kasance a garinmubayan makarantar allo da haddace Al-qur’ani, ana yin sa a masallatai, kuma yakasu gida uku akwai na masufarawa da na ‘yan tsaka-tsaki,da kuma wa]anda suka yi zurfi a ciki.Ya cigaba da cewa ga wanda zai karanta tauhidi kamata yayi ya fara da usulasthalatha, da kitabu attauhid, wanda kuwa zai fara karatu a nahwu kamata ya yi yafara da Ajruumiyya sai mulhatul-i’irab, sai alfiyar Ibnu malik tare da sharhinta naIbnu A}il. (46)A hadisi kuwa kamata ya yi ya fara da arba’una annawawiyya, sai Umdatualahkam, sai bulugul maram,sai munta}a, daga nan har yashiga kutubus sitta.(47)A fiqhu kuma kamar a}asarmu Nigeria ana farawa da kawa’idi (~angaren da yadangancin fiqhu) sai akdhari,sai ishmawi sai iziya, sai risala, sai irshad assaliku,(askari) sannan sai muktasarul khalil.(43) duba Ta’alimil muta’alim na Zarnuuji tah}i}in Marwan {ubani shafi na 90(44) Duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na Ibn Jama’a 144(45) Duba hilyatu [alibil ilmi na Bakar Abuzaid shafi na 25(46) kamar ana Nigeria kumaana faraway da nahwu Al-wadih(47) Duba hilyatu [alibil ilmi na Bakar Abuzaid shafi na 25-27NEMAN ILIMI A MUSULUNCI10Idan ]alibin ilimi ya bi littattafai mataki mataki, sai ka ga ya samu ilimi mai kwari,amma idan ya fara daga sama, to sai ka ga ba ya fahimtar ilimin yadda ya kamata,ko kuma ya fahimce shi ba daidai ba, kamar yadda hakan yake faruwa ga wasudaga cikin ]aliban ilimi.LADUBAN [ALIBIN ILIMI1. SIFFANTA DA [ABI’U MASUKYAU, DA KARE MUTUCIN ILIMINSA.Ya kamata ]alibin ilimi ya siffanta da ]abi’u masu kyau, kamar sakin fuska, dayiwa mutane sallama da ha}uri da mutane, da ba wa kowa ha}}insa gwargwadoniyawarsa, da kuma tausasa musu, da aiki wurin biya musu bu}atu, da tausasawamatalauta, da son makusanta – musamman iyayansa da iyalansa- da ma}ota, darashin yin amfani da kalmomin da ba su dace ba , lokacin da yake magana da su,soboda tausasawa a cikin magana yana ha]a zuciyoyin da suka rabu.Kuma ya yi }o}ari wurin kare mutuncin iliminsa, kar ya shigar da kan sa inda zai}as}anta, indai ba hakan ya zama dole ba, da kuma guraran da za a tuhume shi, kokuma abin da yake a fili mutane za su ga ba shi da kyau, koda kuwa a ~oye maikyau ne, idan kuma ya zama dole sai ya aikata irin wa]annan abubuwan to yasanar da wanda ya gan shi tahanyar bayyana masa abin da ya sa ya yi haka, donkar mutane su kafa hujja da wannan su }i yin amfani da iliminsa, kamar yaddaAnnabi (s.aw.) lokacin da akagan shi da safiya ya bayyanawa mutum biyun da suka gan shi cewa Safiya ce (48)-wato matarsa- don kar ayi zaton koda wata macendaban ya tsaya.kuma ya dinga tuna girma da]aukakar da Allah (s.w.t.) ya yi masa, don kar yawula}anta iliminsa a abin da bai taka kara ya karya ba,]aya daga cikin magabatayana cewa:ولم أبتذل في خدمة العلم لأخدم من لاقیت لكن لأخدماولوأن أھل العلم صانوه صانھم ولو عظموه في النفوس لعظماMa’ana: Ban yiwa ilimi hidima ba don na yiwa wanda na ha]u da shi hidima, na yine don a yi min hidima. Da masu ilimi za su kiyaye shi da ya kiyaye su, da sun girmama shi a cikinzukatansu, da an girmama shi. (49)Kuma duk wasu ]abi’u marasa kyau ya yi }o}ari ya bar su kamar hassada da zaluncida girman kai, da rowa da kwa]ayi, da son a yabe shi daabin da bai yi ba, da rashinganin laifukansa sai shagala da laifin wani, da }arya da cinnaman mutum da sauran]abi’u marasa kyau. Ya dinga tuna cewa ilimin da Allah (s.w.t.) ya ba shi amana ne,kuma wanda ya ba shi zai iyakwacewa, sannan kuma zai tambaye akan abin da ya yida ilimin, don haka sai ya yi}o}ari wurin godewa wanda ya ba shi wannan ilimin, dafatan Allah (s.w.t.) ya ba mu dacewa. (50)2. KAR YA JI KUNYAR AMFANUWA DAGA NA {ASA DA SHI.(48) Bukhari hadisi na 2035, da Muslim 2175(49) Ma’ana da mutane sun girmama shi, wanda ya fa]i wannan wa}ar shi ne Aliyu bn Abdulazizal-jurjani, ya mutu a shekara ta 392 H. duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na IbnJama’a 34(50) Duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na Ibn Jama’a shafi na 40NEMAN ILIMI A MUSULUNCI11[alibin ilimi kar ya ji kunyar amfanuwa da duk wanda ya san wani abun da bai saniba, wasu daga cikin magabata sun kasance suna amfanuwa da na }asa da su, Humaidy]aya daga cikin ]aliban Shafi’i yana cewa, na yi tafiya da Shafi’i daga makka zuwaMisra, na kasance ina fa’idantuwa da shi a fiqhu, shi kuma yana fa’idantuwa da ni ahadisi, Shafi’i yana cewa da]aya daga cikin ]alibansa watoAhmad bn Hanbal: (ka fini sanin ilimin hadisi, idan hadisi ya inganta a wurinku ka ba mu labari, don na yi aikida shi) (51)3. HA{URI DA TALAUCINeman ilimi yawanci yana tafiya tare da talauci, saboda]alibin ilimi ba zai samulokaci isashshe ba na neman ku]i, amma idan ya yi ha}uri da }uncin rayuwa, sai kaga Allah (s.w.t.) ya bu]a masa, kuma ya rage masa yawan burirrika, Shafi’i yanacewa (ba wanda zai nemi wannan ilimin da mulki ko girma kuma ya ci nasara, ammawanda ya neme shi da}as}anci da }uncin rayuwa, dayiwa malamai hidima, shi nezai ci nasara) (52)Imamu Malik kuma yana cewa (ba wanda zai cimma abin da yake so a cikin wannanilimin, har sai talauci ya cutar da shi, kuma sai ya fifita shi –ilimin- akan komai)(53)Kha]ibul-bagdadi kuma yana cewa (an so ]alibi ya zama gwauro idan zai iyadaurewa, don kar ha}}o}in aure da neman abinci su shagalar da shi daga }arasaneman ilimi) (54)Sannan kuma kar ya rin}a cinabinci da yawa, saboda yawan cin abinci da yawa yanasa yawan shan ruwa, hakan kuma yana kawo yawan baccida kasala da da}i}anci,kamar yadda yake sabbaba wasu cututtuka a jikin mutum, wani mawa}i yana cewa:فإن الداء أكثر ما تراه یكون من الطعام أو الشرابMa’ana: Yawancin cutar da kake gani, asalinta daga abinci ne ko abin sha.Don haka duk wanda yake cin abinci da yawa yana da wahala ya yi karatu yadda yakamata. (55)4. SAMUN MALAMI MAI TSORAN ALLAH (S.W.T.) DA TSANTSENIIdan mutum zai nemi ilimi yana da kyau ya sami malamimai kyawawan ]abi’u, maimutunci, mai kamewa, kar kuma ya ce sai malamin da ya shahara zai nemi ilimi awurin shi, saboda zai iya yiwuwa wanda bai shahara ba ya fi tsoran Allah (s.w.t.).Sannan ya sami malamin da yake da ilimi sosai, kuma wanda ya yi karatu a wurinmalamai, kar ya yi karatu wurin wanda ya yi karatu da kansa, Shafi’i yana cewa(wanda ya yi karatu daga cikin littattafai, zai tozarta hukunce-hukunce) (56)Kada ]alibi ya ce zai nemi ilimi shi ka]ai a cikin littattafai, kamar yadda ake cewa(wanda ya shiga ilimi shi ka]ai zai fita shi ka]ai) ma’anawanda ya yi ilimi ba tare damalami ba, zai fita bai san komai ba, saboda ilimi sana’a ne, kuma kowacce sana’atana bu}atar wanda ya iya ta yadda ya kamata. (57)(51) Duba littafin da ya gabata shafi na 44(52) Duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na Ibn Jama’a shafi na 81(53) Duba littafin da ya gabata shafi na 82(54) Duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na Ibn Jama’a shafi na 82(55) Duba littafin da ya gabata shafi na 83(56) Duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na Ibn Jama’a shafi na 90(57) Duba hilyatu [alibil ilmi na Bakar Abuzaid shafi na 22NEMAN ILIMI A MUSULUNCI12Galibi wanda ya yi ilimi ba tare da malami ba kuskurensa zai fi daidansa yawa, kumazai yi ~arna sama da yadda zai yi gyara, sai dai idan mutum ya yi karatu mai zurfi,kuma ya san }a’idojin neman ilimi, ya zama zai iya karanta littafi ya fahimce shi,wannan ba zai shiga cikin wanda ya yi karatu ba malami ba.5. GIRMAMA MALAMIN DA YAKE KOYA MASA KARATUKa yi }o}ari ya kai ]alibin ilimiwurin girmama malamin da ya ke koya maka karatu,saboda hakan shi zai sa ka girmama karatun da yake koya maka, ]aya daga cikin]aliban Shafi’i wato Rabi’I yana cewa: (ban ta~a shan ruwa shafi’i yana kallona ba,saboda kwarjininsa).kuma yana da kyau kar ya rin}a kiran malaminsa daga nesa, ko ya din ga ce masa kaiwane, sai dai ya ce MALAM, SHEIK, kuma ko a bayan idonsa kar ya kira sunansa batare da girmama sunan ba, ya rin}a cewa, malam ya ce, malaminmu ya fa]a damakamancin haka. (58)Kuma ya dinga }as}antar da kai gare shi, ya kuma dinga neman yardarsa, ya kumarin}a neman kusanci da Allah(s.w.t.) da yi masa hidima, akwai wani lokaci da IBNABBAS ya ri}e akalar abin hawan Zaidi bn Thabit ya ce (haka aka umarce mu, mu yiga malamanmu), kuma Imamu Al-Gazali yana cewa: (ba’a samun ilimi sai da}as}antar da kai, da kuma sauraro). (59)Kuma idan malaminsa ya yi masa abin da ba daidai ba kokuma wani hali mara kyauto ya yi ha}uri, kar wannan ya sa shi ya daina zuwa neman ilimi wurin shi, wani dagacikin magabata yana cewa, (duk wanda bai yi ha}uri da}as}anci ba wurin nemanilimi, to zai rayu cikin duhun jahilci), kuma Ibn Abbas yanacewa (Na }as}anta ina]alibi, sai na na samu]aukaka lokacin da na zama malami) (60)Kuma wani mawa}in larabawa yana cewa:إن المعلم والطبیب كلیھما لاینصحان إذا ھما لم یكرماMa’ana: Tabbas malami da likita su duka biyun, ba’a amfana da su, in dai ba’agirmama su ba.6. MALLAKAR LITTATTAFAN DA SU KA KAMATAYana da kyau ]alibi ya kula damallakar littattafai, idan yanada hali ya saye su,idan kuma ba shi da hali to ya yi haya ko ya ara, saboda ba zai yiwu ]alibi yasamu ilimi yadda ya kamata ba sai idan yana da littafi(61).Idan ]alibi ya sayi littafi sabo yana da kyau ya bu]a shi ya san abin da yakecikinsa, ya san abin da littafinya }unsa ta yadda zai iya komawa zuwa gare shiidan wata masa’ala ta taso.7. YIN LADABI A GABAN MALAMI[alibin ilimi ya zama cikin ladabi lokacin da yake gaban malaminsa, kar ya dingakallon wani waje sai malaminsa, kar ya aikata wani abu sai sauraron darasin damalaminsa yake koyarwa, kuma idan zai yi masa tambaya ya tambaye shi cikin(58) Duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na Ibn Jama’a shafi na 92(59) Duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na Ibn Jama’a shafi na 93(60) Duba littafin da ya gabata shafi na 93(61) Duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na Ibn Jama’a shafi na 125NEMAN ILIMI A MUSULUNCI13ladabi, ya kuma saurare shi da kyau lokacin da yake ba da amsa, A[A’U bn AbiRabah yana cewa (na kan saurari mutum lokacin da yake fa]an hadisi, tare dacewa na fi shi sanin hadisin sai na nuna masa kamar bansan komai akan shi ba)kar kuma ya dinga tambayar malaminsa abin da ya riga yasani, saboda akwai ~atalokaci a cikin haka.Idan kuma zai ba wa malaminsa abu to ya ba shi da dama, idan kuma littafi netoya bu]e masa inda yake so kafin ya ba shi, idan kuma zaiyi tafiya da malami, toidan da rana ya kasance a bayansa, idan kuma da daddare ne to ya kasance agabansa, saboda ya kare shi ko da wani abu zai cutar da shi, kar ya dinga tafiya damalaminsa kafa]a da kafada, idan kuma ya ga malaminsa ya yi kuskure kar ya cemalam wannan kuskure ne ko wannan ba daidai ba ne, kamata ya yi ya ce inaganin kamata ya yi ayi kaza, ko makamancin haka(62).8. YIN ABOKAI NAGARIYana da kyau ]alibin ilimi idan zai yi abokai ya yi abokainagari wa]anda za sutaimaka masa wurin neman iliminsa, kar ya yi abokin da zai shagaltar da shi daganeman ilimi.Aboki yana da mutu}ar mahimmanci a rayuwar mutum, idan ya zama abokinkamutum ne mai himma, sai kai ma ka samu himma kamar yadda ake cewa zama dama]aukin kanwa yana kawo farin kai, haka nan idan ya zama mutumin banza sai yayi maka tasiri, Abu Musa Al’ash’ari ya rawaito hadisi daga Annabi ((s.aw.)) yanacewa (misalin aboki na gari da abokin banza, kamar misalin mai ]aukar turare ne damai hura zuga-zugi, mai]aukar turare ko dai ya shafa maka ko ka sayi turare awurinsa ko kuma ka ji kamshi mai ]adi a wurinsa, mai hura zuga zugi kuma ko ya}ona maka kaya ko ka ji wari a wurinsa) (٦٣)Kuma wani mawa}i yana cewa:إذا كنت في قوم فصاحب خيارهم ولاتصحب الأردي فتردى مع الرديعن المرء لاتسأل وسل عن قرينه فكل قرين بالمقارن يقتديMa’ana : idan ka kasance a cikin mutane, to ka yi abota da za~a~~ensu, kada ka yiabota da halakakke sai ku halaka tare. Idan kana so ka san waye mutum, to ka tambayi abokinsa, saboda kowanneaboki da abokinsa yake koyi .Wani kuma yana cewa:لاتصحب الكسلان في حالاتھ كم صالح بفساد آخر یفسدعدوى البلید إلى الجلید سریعة والجمر یوضع في الرماد فیخمدMa’ana: Kar ka aboci malalaci a duklokutansa, da yawa mutumin kirki yana lalacewane idan ya ha]u da mara kirki. Da}i}i yana saurin tasiri akan mai }o}ari, ba ka ganin garwashe idan aka sakashi a toka shi ma sai ya zamatoka.(62) Duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na Ibn Jama’a shafi na 96-105(63) Bukhari ne ya rawaito

Reply

« Back to forum