a ina ALLAH yake

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

a ina ALLAH yake

from nuramuhd3 on 04/26/2015 09:48 PM

GODIYA TA MUSAMMANNa yi godiya ga Allah (S.W.T) da ya qaddari na zamo cikin Musulmi, har na rayu cikin Musulunci tare da yin xan wani abu a cikinsa. Ba tare da alfahari ba, ina godiya ga Annabin Rahama (S.A.W) da ya bayyana komai filla-filla ba tare da voye wani abu ba a cikin Manzanci.Ina kuma qara godiya ga magabata na gari – sahabbaida waxanda suka biyo su da kyautatawa, waxanda a cikin bincikensu ne, na tsakuro abin da na gabatar a wannanxan qaramin littafi.Ina godiya ga dukkan malamai na addini da na boko waxanda da hasken karantarwarsu ne na dubo duk abin da na rubuta. Godiya ta musamman ga Malam Abdullahi Saleh Pakistan, shugaban Jama’atu Izalatil Bidi’a wa Iqamatis Sunnah na Jihar Kano, kuma Limamin Masallacin Tudun Murtala, wanda ya karanta littafin daga farko har qarsheya kuma yi gyare-gyare a cikinsa.Haka kuma ina godiya ga xan’uwa Imam Ja’afar Mahmud Adam, Darakta na Makarantar Usman bin AffanGadon Qaya, wanda shi ma ya karanta littafin kafin a buga, ya kuma bayar da shawarwari masu muhimmanci.Godiya ga Alhaji Ibrahim Xanyaro wanda da taimakonsa ne littafin ya zama yadda yake a yanzu. Wato shi ya xauki nauyin buga littafin. Allah ya saka masa da alheri, amin.A qarshe ina godiya ga dukkan abokaina da suka ba ni qwarin gwiwa da shawarwari har littafin ya zama haka.MA’ANAR IMANI DA ALLAHImani wani abu ne wanda zuciya take qudurta shi, harshe yake furta shi, aiki yake tabbatar da shi. Haka nan Imani da Allah yana nufin qudurcewa da tabbatarda kaxaita Allah (S.W.T) a cikin sanin Shi ne Ubangiji Mahaliccinmu, mai rainonmu (Tauhidin Rububiyya). Haka kuma yana cikin Imani da Allah kaxaita shi da bauta Shi kaxai ba tareda yi masa kishiya ba wato (Tauhidin Uluhiyya). Sannan yana daga cikin Tauhidi ko Imani da Allah yin Imani da siffofinSa da sunayenSa Maxaukaka waxanda suka tabbata a cikin littafinSa Alqur’ani da waxanda Annabi(S.A.W) ya tabbatar masa.Saboda haka Tauhidi ya kasu kashi uku kamar haka:1. Tauhidur Rububiyya: Shi ne kaxaita Allah a ayyukanSa Shi Allah. Shi ne mai azurtawa, mai rayawa, mai kashewa, mai rainon mu. Kuma wanda halitta da iko duk a hannunSa suke. Babu mai waxannan ayyuka sai Shi. Domin Allah yana cewa: “Allah ne mai halitta dukkan komai, kuma Shi ne wakili a kan komai”. (Zumar: 62).Hatta mushirikai sun tabbatar da wannan Tauhidi domin sun yi imanin Allah nemai halitta. Allah yana cewa: “Ka ce wane ne yake azurta ku daga sama da qasa? Shin ko kuma waye yake mallakar ji da gani, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga cikin mamaci, kuma ya fitar da mamaci daga mai rai, kuma wane ne yake shirya al’amari?” To, za su ce “Allah”. To ka ce: “Shin ta ba za ku yi taqawa ba?” (Yunus: 31).2. Tauhidul – Uluhiyya: Shi nekaxaita Allah da bauta, a ayyukan bawa. Ma’ana, Allah Shi ne wanda yake abin bautawa ba tare da haxa shi da kowa ba a cikin bauta. Ba a haxa Allah cikin bauta kamar addu’a, neman tsari, Salla, Azumi, Hajji da sauransu. Domin Allah Mai Tsarki yana cewa: “Ka ce, Ni, mutum ne kawai kamar ku, ana yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lallai ne abin bautawarku, abin bautawa guda ne, saboda haka wandaya kasance yana fatan haxuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na qwarai kuma kada ya haxa kowa ga bauta wa Ubangijinsa”. (Kahfi: 110).Haka nan Allah yana cewa: “Allah ya shaida cewar lallai ne babu abin bautawa face Shi, kuma mala’iku da ma’abota ilmi sun shaida. Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai hikima”. (Ali-Imran: 18). Saboda haka duk wanda ya yi shirka, to ya haxa Allah da wani cikin bauta. Kuma Tauhidin Uluhiyya ya rushe, saboda makomarsa hasara ne. domin Allah ya ce: “Kuma mun yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waxanda ke gabanka: Lallai idan ka yi shirka, haqiqa, aikinka zai vaci, kuma lallai za ka kasance daga masu hasara”. (Zumar: 65).Amma Tauhidin Uluhiyya ba a yi tarayya da kafirai da mushirikai ba, kamar yadda ake tare a cikin Rububiyya. Maxaukakin Sarki ya ce: “Lallai su (kafirai) sun kasance idan an ce musu Babu abin bautawa, face Allah”. Sai su xora girman kai. Kuma suna cewa: “Shin mu lallai masu barin gumakanmu ne, saboda maganar wani mawaqi, mahaukaci”. (Saffat: 35 – 36).3. Tauhidul Asma’i Wassifati: Shi ne Imani da sunayen Allah da siffofinSa waxanda Allah (S.W.T) ya ambata a cikin littafinsa Alqur’ani ko kuma waxanda AnnabinSa (S.A.W) ya ambata a cikin hadisansa ingantattu, kamar yadda suka zo ba tare da korewa, ko kamantawa ba. Haka nan ba tare da misaltawa ko gogewa ba. Domin Allah ya ce: “Wani abu bai kasance tamkar kamarsa ba”. (Shura: 11). Haka ya sake cewa: “Sannan kada ku bayar da waxansu misalai ga Allah. Lallai ne Allah yana sani, kuma ku ba ku sani ba”. (Nahli: 74).Saboda haka Allah yana da sunaye da dama kuma yana da siffofi waxanda suka dace da shi. Lallai mun yi imani daabin da ya zo daga Ayatul Kursiyyu da Suratul Ikhlas damafi yawan surorin Makka da suke maganar sunayen Allah da siffofinsa. Haka surorin Madina, kai mafi yawan Alqur’ani yana magana a bisa haka. Misali, farkon suratul Fatiha – “Bismillahir Rahmanir Rahim”. Ma’ana: “Da sunan Allah mai Rahama, mai Jinqai”. A nan mun fahimci Allah ya ambaci kansa yana da sunaye, mai Rahama, mai Jinqai.Haka nan cikin siffofi Allah yanuna mana cewa yana gani yana zance, yana ji da sauransu. Misali, Allah ya ce:“Ya kuma kasance mai ji ne mai gani”. (Nisa’i: 134). Kumaya ambaci kanSa cewar mai gafara ne: “To lallai ne Allah ya kasance mai gafara mai jinqai”. (Nisa’i: 129). A cikin surori da dama Allah ya ambaci cewar yana da haquri, yana afuwa da sauransu. To, yana daga cikin siffofinsa cewa YA DAIDAITA A KAN AL’ARSHINSA wato daidaito wanda ya dace da shi. Tsira ya tabbata a gare Shi.IMANI DA AL’ARSHIKafin mu kawo hujjojin da ke tabbatar da cewa Allah ya daidaita a kan Al’arshi. Tilas ne mu nusar da cewa, wajibi ne mutum ya yi imani da Al’arshi, amma shin menene ake nufi da Al’arshi? Kuma waxanne hujjoji ne suka tabbatar da wanzuwarsa?Al’arshi wani bigire ne a saman sammai duk inda Allah (S.W.T) ya ambata cewar ya daidaita a kansa. Kuma Shi Al’arshi, Allah ya halicce shi kafin halittar sama da qasa, Subhanahu wa Ta’ala. Kuma Allah ya tabbatar da Al’arshinSa a wurare da dama a cikin Alqur’ani kamar inda ya ce: “Kuma Shi ne wanda ya halicci sammai da qasa a cikin kwanaki shida, kuma Al’arshinSa ya kasance a kan ruwa”. (Hud: 6).Kuma hadisan Annabi (S.A.W) sun tabbatar da Al’arshi kamar hadisin Imranibn Hussain ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku karvi bushara banu tamin”. Sai suka ce: “Ka yi mana bushara, to ka ba mu”. Sai fuskar Manzon Allah (S.A.W) ta nuna vacin rai. Daga nan sai mutanen Yemen suka zo sai ya ce: “Ku karvi bushara mutanen Yemen”. Sai suka ce: “Mun karva”. Sai Annabi ya ba su labarin wannan halitta yadda aka fare ta. Ya ce: “Allah ya kasance kafin komai, kuma Al’arshinSa tana kan ruwa”. Imamul Bukhari da Muslimu suka rawaito da lafazi mai kyau.Saboda haka wannan hadisi yana nuna mana lallai akwai Al’arshi tun da Annabi (S.A.W) ya yi mana bayaninsa. Saboda haka wajibi ne mu yi imani da kasancewarsa. Allah kuma yace: “Mai rahama Ya daidaita a kan Al’arshi”. (DH: 5). Haka nan Allah ya sake ambatar Al’arshi a cikin Suratul – Furqan a ya ta (59). Inda ya ce: “Wanda ya halitta sammai da qasa da abin da yake a tsakaninsu, a cikin kwanuka shida, sannan ya daidaita a kan Al’arshi, mai Rahama, sai ka tambayi mai ba da labari game da shi”.Ubangiji mai Tsarki ya kuma cewa: “Kuma kana ganin mala’iku suna masu tsayuwa da haqqoqin da aka xora musu daga kewayen Al’arshi suna tasbihi game da gode wa Ubangijinsu”. (Zumar: 75).Tunda mun tabbatar cewa akwai Al’arshi, kuma kamar yadda muka bayyana a babinTauhidul Asma’i wassifati cewar Allah ya daidaita a kanshi wannan Al’arshi, wanda yake can sama. To, za mu bayar da dalilan mu daga Alqur’ani da hadisi da kuma haxuwar malamai na gari (magabatansu da waxanda suke raye), a bisa wannan matsala.DALILAI DAGA ALQUR’ANIDalilinmu na farko shi ne Alqur’ani domin Allah (S.W.T)yana cewa: “Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah, ku bi Manzo da ma’abota al’amura daga cikinku, (shugabanni). Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa, idan kunkasance kun yi imani da Allah da ranar lahira wannanshi ne mafi kyau ga fassara”. (Nisa’i: 59).Saboda haka lallai mun yi jayayya a bisa cewar: “Shin a ina Allah yake?” Domin samun amsa ingantacciya, sai ayar ta nuna mana sai mu mayar da abin jayayyarmu zuwa ga Allah daManzonSa. Bari mu ji abin daAllah ya ce: “Mai Rahama ya daidaita a kan Al’arshinSa”. (Suratul X.H: 5). Ma’anar wannan shi ne Allah (S.W.T) ya daidaita wato yana bisa Al’arshinsa a sama. Wannan aya tana nuna mana quru-quru cewar Allah yana sama. To, a nan Allah ya tabbatar mana cewar ya daidaita a kan Al’arshinSa. Daidaito wanda ya dace da shi. Amma yaya ya daidaita? Shi ne ba mu sani ba, kuma Musulmi ba ya halarta ya tambayi yaya Allah ya daidaita a kan Al’arshi? Wato daidaito ne ba irin wanda muka sani ga abin halitta ba. Kamar a ce: “Wane ya daidaita a kan kujera ko ‘’yana kan abin hawa” da sauransu. A’a ba amisalta Allah da kowa domin ya ce: “Wani abu bai zama kamar tamkarsa ba, kuma shi mai ji ne, mai gani”. (Shura: 11).Imam Malik ibn Anas (Allah ya ji qansa), an tambaye shi a kan cewar “Allah ya ce ya daidaita a kan Al’arshi to yaya daidaiton yake?”sai Imam Malik ya ce: “Daidaito dai sananne ne, yaya ya daidaita ba a sani ba. Kuma tamaya a kan yaya Allah ya daidaita bidi’a ce…”.Mai karatu, ka sani cewar babu abin da zai gyara al’ummar nan ta qarshe sai bin da ya gyara ta farkonta. Abin da ya gyara al’ummar farkonta kuwa shi ne littafin Allah da sunnar Manzon Allah (S.A.W). domin Annabi (S.A.W) ya ce: “Na bar muku abubuwa guda biyu. Ba za kuvata ba, matuqar kun yi riqo da su. Su ne: littafin Allah da Sunnata”.To, a kan waxannan abubuwa biyu za mu gina hujjojinmu na tabbatar da cewar Allah (S.W.T) yana sama a bisa Al’arshinSa.Da farko Allah yana cewa: “Shin ko kun amince wanda yake cikin sama, ba zai iya shafe qasa tare da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza? Ko kun amince wanda ke cikin sama ba zai iya sako muku iskar guguwa ba? To za ku sani yadda (aqibar) gargaxina take”. (Mulk: 16 – 17). Waxannan ayoyi guda biyu na Suratul Mulk suna nuna mana, Allah shi ne wanda yake a saman kuma a bisa Al’arshinSa. Domin shi Al’arshi yana saman sammai duka. Kasancewar Al’arshi tana saman sammai, sai Allah ya ce: “Ko kun amince wanda yake sama…”. Yana nufin wanda yake saman sammai duka a bisa Al’arshinsa, ba wai yana cikinsama yana nufin yana cikin kowace sama ba. Domin sammai har bakwai ne, to allahyana saman sama ta bakwai da zatinSa, amma yana sane da mu da ganinSa da iliminSa (S.W.T).Haka nan lokacin da Yahudawa suke ganin sun kashe Annabi Isa (A.S) sai Allah ya ce musu ba su kasheshi ba ko gicciye shi ba. Domin Allah ya tabbatar musu da Isa (A.S) yana ina? Sai ya ce: “A’a, Allah ya xaukeshi zuwa gare Shi, kuma Allah ya kasance Mabuwayi. Mai hikima”. (Nisa’i: 158). Ma’ana, wannan aya tana nuna mana cewar Allah ya xauke Isa (A.S) zuwa gare shia sama, kuma dukkanin Musulmi sun yarda cewar yana sama, kuma zai dawo qasa. Har ma muna jiran saukowarsa, kamar yadda Hadisan Manzon Allah (S.A.W) suka nuna.Xaya daga cikin hadisan shi ne wanda Imamul Bukhari yarawaito a babin saukowar Annabi Isa: abu Huraira (R.A)ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Na rantse da wanda raina yake hannunSa, ya kusata xan Maryam ya saukomuku yana mai hukunci, kuma mai adalci…”. A nan Annabi (S.A.W) ya tabbatar mana cewar Annabi Isa (A.S) yana sama, kuma zai sauko qasa. Saboda haka lallai Annabi Isa yana wajen UbangijinSa a sama.A cikin (Suratul Faxir: 10) Allah ya ce: “Zuwa gare shi magana mai daxi ke hawa, kuma aiki ne qwarai yana xaukakarsa”. Ma’ana yana xaukarsa zuwa sama. Haka nan dai Allah ya ce: “Yana shirya al’amari daga sama zuwa qasa, sannan ya taka zuwa gare shi a cikin yini, wanda gwargwadon shekaru dubu ne daga abin da kuke lissafawa”. (Suratul Sajda: 5).A cikin (Suratul Ghafir: 36) Allah ya ce: “Kuma Fir’auna ya ce ya Hamana ka gina mini bene tsammanina za ni isa ga qofofi. Qofofin sama domin yi tsinkaya ga abin bautawar Musa. Kuma lallai ni haqiqa ina zatonsa maqaryaci”. A nan, Fir’auna kansa ya san Allah yana sama, kuma hujjar da take qara tabbatar mana da haka shi ne Allah (S.W.T) bai yi wa Fir’auna raddi game da iqirarinsa na cewar Allah yana sama ba. Fir’auna ba Musulmi ba ne, amma Allah ya tabbatar da maganarsa domin gaskiya ya faxa.Haka nan cikin (Suratul Ma’arij: 4) Allah ya ce: “Mala’iku da Ruhi (Jibril) sunatakawa zuwa gare shi”. Ma’ana suna takawa wajen Allah wanda yake bisa Al’arshi a sama.Wata hujja da ta qara fito da abin fili ita ce aya ta farko ta cikin Suratul Isra’i inda Allah ya ce: “Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da BawanSa, da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nisa, wanda Muka sanya albarka agefensa domin Mu nuna masa daga ayoyinmu. Lallai ne shi, shi ne mai ji, mai gani”. (Isra’i: 1).Isra’i shi ne tafiyar dare da Allah ya yi da Annabi daga Makka zuwa Baitul Muqadis. Sannan Mi’iraji zuwa sama inda aka ba shi salloli. Ma’ana, Isra’i kullum tare yake da Mi’iraji. Saboda hakamasu da’awar Allah ba a sama yake ba, suna iya cewar Isra’i da Mi’iraji da Buraqa duk ba su da ma’ana.An karvo daga Yunus daga Hishab daga Anas bin Malik ya ce: “Abu Zair (R.A) yana bada hadisi daga Annabi (S.A.W) cewar: “An buxe rufin xakina ina Makka, sai Jibrilu ya sauka ya xauke ni zuwa saman duniya. Lokacin da muka isa saman duniya sai Jibrilu ya ce da mai tsaron qofar saman ‘ka buxe mana qofa’. Sai ya ce: ‘Kai da wane ne?’ Sai ya ce: ‘Ni da Muhammadu’. Sai ya ce: ‘An aiko masa ya zo ne?’ Sai ya ce: ‘Na’am! Sai aka buxe musu qofa…’. A qarshen hadisin Annabi ya iske Annabawa kamar su Adam, Idrisu, Musa, Isa da Ibrahim (A.S) Bukhari ya rawaito wannan hadisi ba ya buqatarwani qarin bayani, hujja ce qarara.Gaskiya dalilai daga Alqur’animai girma suna da yawa, ba zan iya kawo su duka a cikin wannan qaramin littafi ba, domin suna da dama.DALILAI DAGA SUNNAHSunnar Manzon Allah (S.A.W)ita ce matakina biyu na kafa hujja a cikin Shari’ar Musulunci. Domin Allah ya ce: “Duk abin da Manzo ya zomuku da shi, ku riqe shi. Dukabin da ya hane ku, to ku hanu”. (Hasari: 7). Saboda haka Annabi (S.A.W) ya zo mana da sunna. Kuma Allah ya sake cewa: “Lallai waxanda suke sava wa tunaninsa (shi Annabi) su yi jiran wata azaba mai raxaxi ta same su”. (Nur: 63).Saboda haka lallai za mu kafahujjoji daga sunna na tabbatar da cewar Allah yanabisa Al’arshi. Amma ba kowa zai yarda ba, sai mai imani. Domin a cikin Suratun Nisa’i: 65 Allah ya nuna mana cewaryarda da hadisi/sunna yana cikin imani inda ya ce: “To a’aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi imani ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin daya sava a tsakaninsu, sannan kuma ba su sami wani qunci a cikin zukatansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama, sallamawa”.To, a cikin sunnar ne muka iske hujjoji da dama da ke tabbatar mana cewa Allah (S.W.T) yana sama ya daidaita a kan Al’arshi. Daidaito wanda ya dace da shi. Aqidar da ta sava wa masu cewar Allah yana ko’ina, ana nufin yana cikin qazanta ke nan. Ko kuma idan yana jikin halitta to komai ma yana iya zama Allah ke nan, a bisa ruwayarsu. Tsarki ya tabbata ga Allah a bisa abin da suke siffanta shi da su.To, bari mu ji abin da fiyayyen halitta Mustafa (S.A.W) ya ce: Abu Huraira (R.A) y a rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewar: “Idan xaya bisa ukun dare ya yi saura, Allah yana sauka a kowane dare zuwa sama ta qasa, ya ce: wane ne zai roqeNi in amsa masa. Wane ne zai tambaye Ni, in amsa masa, wane ne zai nemi gafara in gafarta masa? Imam Ahmad ya rawaito wannan hadisi da jingine maikyau da kuma lafazi mai yawa.A wani hadisi Annabi (S.A.W) yana cewa: “Shin ba za ku amince mini ba. Alhali ni ne amintaccen wanda yake sama”. Bukhari da Muslim suka rawaito shi. Kuma wata rana Annabi (S.A.W) ya raba wani abu ga sahabbansa sai wani sahabi ya ce: “Wannan rabo ba a yi adalci ba”. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Wane ne zai yi adalci don ni ban yi adalci ba. Alhalin ni neamintaccen wanda yake sama?”A lokacin da Manzon Allah (S.A.W) ya yi Hajjin Bankwana, ranar Arfa ya yi huxuba, yana cewa: “Shin na isar muku da saqo?” sai sahabbai suka ce: “Na’am ka isar”. Sai Annabi ya xaga hannayensa guda biyu zuwa sama ya ce: “Allah ka shaida”. Kamar yadda bayaniya gabata wannan hujja ta hankali domin duk muna daga hannayenmu zuwa sama ne. wani lokaci har da fuskokinmu yayin yin addu’a. Domin a aikace a nan mun tabbatar Allah yaana sama a kan Al’arshinSa.A wani hadisi ingantacce Annabi (S.A.W) ya ce: “Ku jiqan waxanda suke qasa domin wanda yake sama ya jiqanku”. Wato idan kun tausaya wa bayin Allah da kuke tare da su. Allah wanda yake sama zai tsauaya muku.Wannan hadisi Tirmizi ya rawaito shi da isnadi mai kyau.

Reply

« Back to forum