ADDININ GASKIYA (1)

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Oldest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

ADDININ GASKIYA (1)

from nuramuhd3 on 04/26/2015 11:42 PM

ADDININ GASKIYA (1)(SAHABBAN MANZON ALLAH(SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAMA) DA ALAYENSA)Bismillahir Rahmanir Raheem. Wa Sallallahu ‘alan Nabiyyil Kareem, Wa ‘ala alihi wa Sahbihi wa man tabi’ahum bi ihsanin ila Yaumid-Din.ABIN DA AKE NUFI DA “SAHABI”:A harshen larabci idan aka ce “Sahib” yana daukar ma’anar: Aboki, Mabiyi, Wanda ya danfaru da mutum, ya lazimceshi, ko kuma wanda ya gamu da mutum.A ma’ana ta shari’a kuwa idan aka ce “Sahabi”, ana nufin:( WANDA YA GAMU DA ANNABI (SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAMA), YA YI IMANI DA SHI, YA KUMA MUTU A CIKIN ADDININ MUSULUNCI).Kenan ba za’a kira mutum “Sahabi” ba, sai ya cika sharuda guda uku:SHARADI NA DAYA: Gamuwada Annabi (Sallallahu alaihi wa sallama):Wannan gamuwa tana baiwa mutum daraja ta kasancewarsa “Sahabi”, sawa’un sun gamu kuma ya zauna da Ma’aiki zamani mai tsawo, ko kuma sau daya ne kurum gamuwar ta kasance. Idan dai har ya hadu da shi ko yaya ne, kuma ya cika ragowar sharudan da zamu ambata, to ya zama Sahabi.Akwai wata fahimta ta wasu malamai da suke ganin ba za’a ce wa mutum “Sahabi” ba, har sai ya dauki lokaci mai tsawo tare da Ma’aiki (SallalLahu alaihi wa sallama).Sai dai wannan fahimta ta sabawa ma’anar kalmar “Sahib” a harshen larabci; domin kuwa harshe bai bayyana irin wannan bambancin ba.Don haka, abin da ya fi rinjaye shine: ko da sau dayane tak gamuwar ta kasance to za’a kira mutum “Sahabi”.Wannan shi ya sanya don malamai su kara fito da ma’anar “Sahabi” fili, sabaninwaccan fahimtar sai suka ce Sahabi shine:“DUK WANI DA YA GAMU DAANNABI, KO DA SAU DAYA NE TAK, KO DA BASU YI IDO HUDU BA, KAMAR MAKAHO”.Daga nan suka kawo ragowarsharudan.Misalin wanda ba su yi ido hudu da Ma’aiki ba, amma kuma sun gamu daga cikin Sahabbai shine: Abdullahi bnUmmi Maktum (Allah ya karamasa yarda), shi makaho ne, bai taba ganin Ma’aiki da idanuwansa ba, amma kuma sahabi ne shi, saboda ya hadu da Annabi SallalLahu alaihi wa sallama.A takaice wannan sharadi ya nuna mana cewar wadanda suka riski zamanin Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama), amma ba su gamu da shi ba, suka ci gaba da zama a garuruwansu, kamar wasu da suke Sham ko Misra, ko Yaman… da sauransu…Ko kuma wadanda suka yi Imani da shi, suka kamo hanya don su yi mubaya’a, kafin su karaso Madina Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama) ya yi wafati, wadannan ba za’a kirasu “Sahabbai” ba. Ana kiran irin wadannan mutanen: “Mukhadhramun”; wato wadanda suka rayu a zamanin da aka aiko Ma’aiki, suka rayu har bayan wafatin Ma’aikin, amma basu samu darajar zama “Sahabbai” ba.SHARADI NA BIYU: IMANI:Dole mutumin da ya gamu da Ma’aiki (SallalLahu alaihi wa sallama) ya zamo ya yi Imani da shi, sa’annan ya samu siffa ta Sahabi.Wannan sharadi na biyu, wato yin Imani da Ma’aiki SallalLahu alaihi wa sallama ya fitar da Kafirai wadanda suka hada zamani da fiyayyen halitta, Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama), wadannan ba za su shiga cikin Sahabbai ba.Hakama wadanda suka gamuda shi, amma ba su yi imani da shi ba sai bayan wafatinsa, suma ba za a kidaya su cikin Sahabbai ba.Sannan Imanin dole ya zamoingantacce; don haka munafukai da suka kasance azamanin Manzon Allah SallalLahu alaihi wa sallama, irinsu Abdullahi bn Ubayyi bn Salul, ba zasu shiga cikin lissafin sahabbai ba, domin kuwa a zahiri ne suke bayyana cewa su musulmi ne, amma a boye ba haka bane.SHARADI NA UKU: DAWWAMA A CIKIN MUSULUNCI HAR MUTUWAWato Ya zamo wanda ya gamu da Ma’aiki SallalLahu alaihi wa sallama, ya kuma yiImani da shi, ya ci gaba da rike addinin musulunci har zuwa mutuwarsa, bai yi riddaya bar musulunci ba.Wannan sharadi ya fitar da jama’ar da suka yi ridda, wadanda Sayyidina AbubakarSiddik (Allah ya kara musu yarda) ya yi fama da su a farkon halifancinsa.Wadansu daga cikin wadannan jama’a da suka yi ridda, sun gamu da Ma’aki (SallalLahu alaihu wa sallama), kuma sun karbi musulunci a lokacin da yake a raye, sai dai bayan rasuwarsa sun fita daga addinin Allah, don haka ba zasu zamo cikin lissafin Sahabbai ba.FADAKARWA GUDA BIYU:1- Ridda itace: Mutum ya zo da wani abu da zai fitar da shi daga addinin musulunci, da furuci, ko kudurcewa, ko aiki. sawa’un ya yi hakan ne don izgilanci ga addini, ko don bijirewa, ko kuma kudurce hakan ya yi. Daga cikin misalan ridda: ya yi musun cewa akwai Allah, ko ya musa wani daga cikin manzanni, ko karyata su, ko ya halalta abin da aka haramta shi a Ijma’in malamai, ko ya haramta abinda yake halal ne a Ijma’i, ko ya yi niyyar cewa zai kafurta nan gaba. [Duba Minhaj na Nawawi: 1/427].2- Adadin Sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama) da suka halarci “Bai’atur Ridhwan” mutum Dubu daya da Dari Hudu ne (1400). Adadin wadanda Ma’aiki ya fita da su don bude Makka kuma sun kai, Dubu Goma (10,000). Wadanda suka halarci hajjin ban kwana tare da shi kuwa sun kai Dubu Dari, da Dubu Ashirin da Hudu (124,000). Wannan itace shahararriyar maganar malaman Sirah.ADDININ GASKIYA (2)(SAHABBAN MANZON ALLAHSALLALLAHU ALAIHI WA SALLAMA DA ALAYENSA)Ci gaba …Allah Mai girma da daukaka a cikin Kur’aninsa Mai tsarki ya yi bayanin girman daraja da tsarkaka ta mahaifar Manzon rahama, wato garin Makkah mai alfarma.Kamar yadda kuma ya yi bayanin siffofin Sahabban Annabi (SallalLahu alaihi wa sallama) a cikin AlKur’ani maigirma, da yadda siffofin nasusuke a cikin Attaura da Linjila. Yo Dama kuma ai hankali ba zai taba karbar cewa a bayyana girman daraja da matsayi na gari, amma kuma a kasa bayanin daraja da girma na abokin zama dahulda.Idan ya zamo bigiren da aka aiko Manzon karshen zamaniyana da wata kebantacciyar daraja, to lallai kuwa wadanda suka fi cancantar su samu matsayi da daraja kebantacciya sune Sahabbansa, wadanda suke tare da shi, dare da rana, (Allah ya kara musu yarda).Idan mutum ya taba zama dawani malami, mai kima, ya dauki karatu a wajensa, to yana daga cikin abin da al’ada ta gudana akai shine idan ana so a kwarzanta wannan mutumin, a bayyanakimarsa, da falalarsa, a lokacin da ake bayar da tarihinsa akan bayyana cewa har ya dauki karatu ma a wajen malami wane. Sai zaman da ya yi tare da wannan malamin ya zamo cikin abubuwan da suke karawa mutumin nan girma da kwarjini a wajen jama’a.To ina ga wanda malaminsa, da karatunsa duk a gaban fiyayyen halitta ya dauke shi?Lallai daukakar ta wuce a kwatantata! Lallai girman ya kai matuka! Lallai albarkar ta yawaita!Don haka kasancewarsu “Sahabbai” kadai daraja ce da ta kera duk wani aiki da zaka iya tunanin ambato shi, hakan ne ma ya sanya wannan siffa ta “Sahabi” takelazimtar duk wanda ya samu wannan gagarumar falalar. Idan ka leka littattafan tarjamar daidaikunsu, zaka samu cewa siffa ta farko da ake ambatowa ga kowanne daya daga cikinsu shine cewa: “SAHABIN MA’IKI NE SHI”.Bayan wannan falala ta kasancewarsu Sahabban fiyayyen halitta, Allah Madaukakin sarki da kansa ya yi musu yabo da kirari a cikin littafinSa Mai girma, wannan yabo kuwa zai ci gaba da binsu har a nade kasa.Ayoyin da suka zo a cikin Kur’ani suke bayanin girman falalar wadannan jama’a da yabo da kirari garesu za’a iyakasa zaka iya kasasu kashi biyu:1) Ayoyin da suka yi yabo a garesu a dunkule.2) Ayoyin da suka yi yabo filla-filla.Za mu duba wasu daga cikin wadannan ayoyin, mu yi bayanin ma’anoninsu a takaice, amma kafin nan, zanfara da matashiya:MATASHIYA:Lokacin da aka aiko Fiyayyen halitta (SallalLahu alaihi wa sallama), wadanda suka yi Imani da shi a Makka yawancinsu marasa karfi ne, don haka kafirai suka dora musu karan-tsana, suka yi ta zaluntarsu. Su kuwa Sahabban Ma’aiki na farko suka daure, suka yi ta hakuri,daga karshe ma aka kore su daga garuruwansu, aka kwace dukiyoyinsu, duk da haka saboda neman yardar Allah suka hakura da duk wata tsangwama da aka yi musu, suka bar garinsu da gidajensu, da dukiyoyinsu, suka yi hijira, ba don komai ba sai don su marawa addinin Allah da ManzonSa baya, ba wai don cimma wata bukata tasu ta duniya ba, kamar yadda Allah Madaukaki ya ce:( ﻳﺒﺘﻐﻮﻥ ﻓﻀﻼ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺿﻮﺍﻧﺎً ﻭﻳﻨﺼﺮﻭﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ. ( ﺍﻟﺤﺸﺮ: 8 )Bayan sun isa garin Madina, sai ya zamo musulunci yana samun daukaka, yana kara karfi, ya fara kafa turakunsa.Sai wasu jama’a saboda tsoron karfin wannan addini,wasu kuma saboda hassada da bakin cikin zamowarsa karfen kafa gare su (Saboda ya toshe musu wasu abubuwa na jin dadi da suke tunanin a baya zasu samu badon zuwan musuluncin ba, kamar yadda Abdullahi bn Ubayyi bn Salul ya kasance ana daf da a nada shi ya zamo sarkin ‘yan Madina, ana cikin haka, katsam! Ma’aiki ya iso wannan gari mai hasken albarka, sai wannan ya dagula masa lissafi). Irin wadannan mutanen sai suka shiga rigarmusulunci da niyyar zasu yi masa zagon kasa, su wadannan jama’a su ake kira “Munafukai”.Musulunci ya samu gindin zama a Madina, ya kuma yi karfin da a baya bashi da shi.Ta daya bangaren kuma sai ya zamo yana fama da kalubale ta bangarori uku, maimakon kalubale ta bangare daya da ya yi fama da shi a Makka, wadannan bangarorin sune:1- Kafurai sun ci gaba da sanya kafar wando daya da duk wata da’awa ta musulunci, suka kullaci komai nasa, suka ci gaba da bin duk wani salo na dakile shi, da aibata shi, da hana jama’a sauraron da’awarsa.2- Yahudawa, wadanda suke zaune a garin Madina, hassada ta ci ta cinyesu, bayan kuma dalilin da ya sanya suka tare a wannan gari mai albarka shine sun karanto a littattafansu cewa shine garin da Annabin karshen zamani zai yo hijira zuwa gare shi. Yahudawa a Madina Kashi uku ne: A) Banu Kainuka’. B) Banu Kuraizah. C) Banun Nadheer.3- Munafukai, wadanda suka shiga rigar musulunci, suke yi masa zagon kasa, ayyukan wadannan munafukan na zagon kasa ya bayyana kuru-kuru a yakin UHUD da kuma yakin KHANDAK, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ba da labarisu da siffofinsu a wasu surori na Kur’ani, wanda nangaba zamu tabo manya-manyan siffofin, mu bayyanabambancin Sahabi da Munafuki, ba kamar yadda wasu suke nema karfi da yaji suyi kwado su cakudasu ba, alhali babu mahada; kowanne dayansu akwai bayaninsa a littafin Allah.Da yake wannan kashin na karshe (Wato munafukai) a zahiri suna nuna cewa suna tare da musulmai, suna rayuwa tare da su, wasunsu ma a boye suke ba a san cewa munafukai bane, sai wasu suka cakuda su da Sahabbai, suka kasa bambancesu.Akwai sinfi guda uku a cikin musulmai:NA FARKO: Wadanda aka riga aka sani yakinan cewa muminai ne, Allah ya yi bayaninsu. Wadannan sune Sahabban Ma’aiki (SallalLahualaihi wa sallama) da sannu zamu yi bayanin siffofin da Allah Madaukaki ya basu.NA BIYU: Wadanda aka sani yakinan cewa munafikai ne, wadannan ba za’a taba lissafa su cikin Sahabbai ba, su ma zamu kawo siffofinsu yadda Allah ya yi bayaninsu.NA UKU: Wadanda akwai rudani a kansu, wato babu bayanin ajin da za’a sanya su.(Kashi biyun farko babu matsala ko kadan a kansu, domin kuwa duk wanda aka tabbata yana daya daga cikinsu, to yanke za’a danganta shi zuwa kashin da yake.Matsalar kawai ta takaita ne a kashi na karshe, wadanda ba’a sansu ba, alhali kuma munafukai ne, to wadannan babu wani da zai iya yanke hukunci kai tsaye a kansu a kuma karba sai Nassi daga Kur’ani ko Hadisi.Siffofin da zamu yi bayaninsuna Sahabbai, wato muminai, da siffofin da zamu yi bayani na munafukai su zasu bamu damar gane wadanda aka samu rudani a cikin lamarin na su.Dadin wannan addinin namukenan, babu wani abu da akayi inda-inda cikin bayaninsa, don haka duk wanda ya shigacikin rudani to shi ya ruda kansa, ko kuma bai zurfafa bincike a Kur’ani ba. AlKur’ani Mai girma shine babban alkalinmu a cikin irinwannan hali, da kuma hadisan fiyayyen halitta (SallalLahu alaihi wa sallama).Don haka, duk wanda zai kawo wani rudu a irin wannan matsayin, ka nemi ya kawo maka bayani kuru-kuru daga Kur’ani ko Hadisi, idan ya kawo maka nassi maigamsarwa to babu makawa ayi aiki da shi, idan kuwa ya kama kame-kame, to kada ma ka bata lokacinka wajen sauraronsa.A DUNKULE:Allah Madaukaki ya bayyana Sahabbai, Muminai, ya yi bayanin siffofinsu. Ya kuma yi bayanin munafukai, ya bayyana siffofinsu.Munafuki ba Sahabi bane, saboda Allah ya bambance su inda yake cewa:( ﻭﻳﺤﻠﻔﻮﻥ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﺇﻧﻬﻢ ﻟﻤﻨﻜﻢ ﻭﻣﺎﻫﻢ ﻣﻨﻜﻢ ( ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ: 56 )A wannan Aya Allah ya yi bayanin cewa Munafukai sukan yi rantsuwa cewar suna cikin Sahabban ManzonAllah (SallalLahu alaihi wa sallama), bayan kuma sam basu cikin Sahabban ManzonAllah.(NAN GABA ZAMU DUBA SIFFOFIN DA ALLAH YA BAIWA SAHABBAI (ALLAH YAKARA MUSU YARDA), DA KUMA KIRARI DA YABO DA YA YI MUSU, MU YI BAYANINCEWA DUK WANDA ALLAH YA YARDA DA SHI TO HAR ABADA BA ZAI DAWO KUMA YA YI FUSHI DA SHI BA, MU KAWO DALILAI AKAN HAKANIN SHA’ALLAH).FADAKARWA GUDA BIYU:1- Surorin da Allah ya ambaci muminai da kuma munafukai a Kur’ani sun hada da: Baqara, da Ali Imran, da Nisa’, da Ma’idah, da Ankabut, da Ahzab, da Fath, da Qitaal, da Hadeed, da Mujadalah, da Hashr, da Munafiquun … Haka yawancin surorin da suka sauka a Madina.2- Malaman ULUMUL QUR’AN sun ce:(Duk wata Sura ta Kur’ani da aka ambaci Munafikai a cikinta to wannan sura Madaniyya ce, sai suratul Ankabut ita kadai ita ce Makkiyyah).Sun ce kuma: (Duk wata Surata Kur’ani da aka yi muhawara da ma’abota littafi[Yahudawa da Nasara] to wannan sura Madaniyya ce).Na san za mu iya riskar dalilin hakan.

Reply

« Back to forum