adn daskiya 3

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

adn daskiya 3

from nuramuhd3 on 04/26/2015 11:37 PM

ADDININ GASKIYA (3)SAHABBAN MA’AIKI SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAMA DA ALAYENSAAlhamdu lilLah, Wassalatu Wassalamu ala rasulilLah, Wa ala Alihi wa Sahbihi, wa man tabi’ahum bi ihsanin ‘ila yaumid deen.A baya na yi alkawarin kawo bayanin irin girman kirari da yabo, da siffofi masu haske da Allah Mai girma da daukaka ya baiwa abokan zaman Ma’aiki (SallalLahu alaihi wa sallama), sai dai kafin wannan na tabo jijjige na biyu na unwanin wadannan maqalolin nawa wato alayen Ma’aiki (SallalLahu alaihi wa sallama).Ina kuma fatan a yanzu In sha’Allah babu wani abu da ya rage da zai shige mana duhu game da abin nufi da wadannan jama’a guda biyu (SAHABBAI DA ALAYE).DON HAKA, Yanzu zan shiga kai tsaye cikin abin da na yi alkawari, zan kuma dauki fitattun ayoyin alkur’ani da suka kunshi yabo da kirari gawadannan manyan bayin Allah na yi bayaninsu dalla-dalla, zan bi salon bayanin siffofin Sahabbai a karkashin kowace Aya da zan kawo, idan akwai munasaba zan kawo hadisai da maganganun malaman musulunci.Zan bayar da karfina bisa bayanin siffofin Sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama) ne kamar yadda Allah ya gaya mana su; domin da sanin siffofinsune zamu iya gane bambanci tsakaninsu da wasunsu (kamar Munafukan zamanin Manzon Allah), wadanda wasu jama’a, marasa adalci, masu fama da ciwon zuciya da tsatsarta suke ta kokarin sai sun gwamutsa tsakaninsu, sun basu hukunci guda daya, alhali Allah Madaukakin sarki da kansa ya riga ya sanya iyaka tsakaninsu, ba mai gane hakan kuwa sai wanda Allah ya datar, ya yalwata masa kirjinsa, ya bude basirarsa, ba wanda gilli da hassada, datsatsa suka cika zuciyarsa ba,suka hana shi sakat, ba shi son ya ji an ambaci wani abunasu na arziki, shi wannan duk yadda zaka yi dashi ba zai taba ganin haske ba, sai wani ikon Allah.( ﻭﻣﻦ ﻟﻢ ﻳﺠﻌﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻪ ﻧﻮﺭﺍً ﻓﻤﺎ ﻟﻪ ﻣﻦ ﻧﻮﺭ )KIRARI DA YABO DA ALLAH YA YI WA SAHABBAN MA’AIKI A KUR’ANI:NA KASA AYOYIN KASHI UKU:1- Ayoyin da suka yi yabo da kirari ga jumullar Sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama).2- Ayoyin da suka yi yabo da kirari ga Sahabban Ma’aiki dasuke dauke da wata siffa, KAMAR MUHAJIRUN, DA ANSAR.3- Ayoyin da suka yi yabo da kirari ga wasu jama’a daga cikin Sahabban Manzon Allah(SallalLahu alaihi wa sallama)saboda nuna bajintarsu ta halartar yake-yake tare da Ma’aiki.NA FARKO: AYOYIN DA SUKE YABO DA KIRARI GA JUMULLAR SAHABBAN MA’AIKI SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAMA:Aya Ta Daya:fadin allah madaukakin sarki:ﻣﺤﻤﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﻣﻌﻪ ﺃﺷﺪﺍﺀ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻜﻔﺎﺭ ﺭﺣﻤﺎﺀ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﺗﺮﺍﻫﻢ ﺭﻛﻌﺎً ﺳﺠﺪﺍً ﻳﺒﺘﻐﻮﻥ ﻓﻀﻼ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺿﻮﺍﻧﺎ، ﺳﻴﻤﺎﻫﻢ ﻓﻲ ﻭﺟﻮﻫﻬﻢ ﻣﻦ ﺃﺛﺮ ﺍﻟﺴﺠﻮﺩ، ﺫﻟﻚ ﻣﺜﻠﻬﻢ ﻓﻲﺍﻟﺘﻮﺭﺍﺓ ﻭﻣﺜﻠﻬﻢ ﻓﻲ ﺍﻹﻧﺠﻴﻞ ﻛﺰﺭﻉﺃﺧﺮﺝ ﺷﻄﺄﻩ ﻓﺂﺯﺭﻩ ﻓﺎﺳﺘﻐﻠﻆ ﻓﺎﺳﺘﻮﻯ ﻋﻠﻰ ﺳﻮﻗﻪ ﻳﻌﺠﺐ ﺍﻟﺰﺭﺍﻉﻟﻴﻐﻴﻆ ﺑﻬﻢ ﺍﻟﻜﻔﺎﺭ، ﻭﻋﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻭﻋﻤﻠﻮﺍ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﺎﺕ ﻣﻨﻬﻢ ﻣﻐﻔﺮﺓﻭﺃﺟﺮﺍً ﻋﻈﻴﻤﺎً ).Ma’ana:([Annabi] Muhammadu Manzon Allah ne kuma wadanda suke tare da shi (masu) tsanani ne a kan kafirai, kuma masu tausayin junansu ne, za ka gansu sunaruku’i suna sujjada suna neman falala da yarda daga Allah, alamominsu suna cikinfuskokinsu na gurbin sujjada,wancananka misalinsu kenana cikin Attaura. Misalinsu kuma a cikin Linjila kamar shuka ce da ta fitar da tsakinta, ya karfafata, suka kuma yi kauri, suka daidaita a kan itatuwansu, har take baiwa manoma sha’awa; donkuma su fusata wadan da suka kafirta da su. Allah ya yiwa wadan da suka yi Imani, suka yi ayyuka na gari daga cikinsu alkawarin gafara da kuma lada mai girma). [Fath: 29].Allah Madaukaki ya bayar da misalin Annabi da Sahabbansa a cikin Attaurar Annabi Musa da Linjilar Annabi Isa.Misalinsu a cikin Attaura zahiri ne kamar yadda muka gani.Misalinsu kuwa a cikin Linjilaan misalta su da shuka wadda a farkonta take farawa rarrauna,’yar siririya, dan yaro ma zai iya tsige ta, saboda tsananin rauninta, bayan nan kuma sai ta yi ta yin tsiro tana fidda ressa, daga nan ta zo ta yi kauri ta yi karfi, ta yi kyau har tana kayatar da manoma, masanashuka.To haka Annabi SAW ya kasance da shi da Sahabbansa, a farkon musulunci sun kasance ‘yan kadan, masu rauni, bayan nan suka rika habaka, adadinsu na karuwa, har suka kai matsayin da suka kai, gaba dayan tsibirin larabawa ya rissina wa wannan addini, daga nan kuma ya fantsama zuwa dukkan fadin duniya. [duba: Adhwa’ul Bayan: 7/398].YADDA ALLAH MADAUKAKI YA SIFFAITA SAHABBAI A WANNAN AYA:A wannan ayar Allah ya yi bayanin wasu siffofi masu fantsamar haske na Sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama)kamar haka:1- MASU TSANANI NE BISA KAFURAIA wajen yakarsu, da nuna ba su tare da su, da gaba da su, wato suna fishi domin Allah, suna ki domin Allah. Mutum daga cikin Sahabbai yakan yaki Iyayensa ko ‘ya’yansa, ko‘yan uwansa na jini, ko wasu danginsa na kusa, duk dan daukaka kalmar Allah.Mun sani kuma SAHABBAN MANZON ALLAH LALLAI SUNSIFFANTU DA WANNAN SIFFA.2- MASU JIN KAN JUNANSU NESuna so da kaunar junansu saboda Allah. Ma’aiki ya bayar da labarin yadda muminai suke tausayawa junansu yake cewa: (Zaka samu muminai a wajen soyayya, da tausasawa, da jinkan junansu kamar misalin gangar jiki guda ne, idan wata gaba tana jin radadin ciwo, sai gaba dayan gangar jikin ta dauka tare da wannangabar tana taya ta jimami, ta hanyar rashin barci, da yin zazzabi). [Bukhari: 6011, Muslim: 2586].3- MASU YAWAN BAUTAR ALLAH NE:Zaka gansu suna ruku’i, suna sujjada. Aliyu (Allah ya kara masa yarda) yace: “Hakika ban ga wanda ya yi kama da Sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama)a cikinku ba: sun kasance suna wayar gari, kawunansu a tsefe, jikkunansu sun yi kura, sun kwana cikin sujjadada tsayuwar dare, aikinsu shine tsayuwar dare da yawan sujjada, idan suka mike kai kace akan garwashin wuta suke sabodatunawa da karshensu, tsakanin goshinsu ya yi kamar gwiwoyin tumakai saboda tsawaita sujjada, idan suka ambaci Allah sai idanunsu su kawo ruwa su cika da hawaye, su kadu kamar yadda iska take kada bishiya a ranar da ake iska mai tsananin karfi”. [Duba: “Al-Hilyah” ta Abu Nu’aim: 1/76, da “Nahjul Balaga” huduba ta 97].4- SUNA YIN DUKKAN AYYUKANSU DON NEMAN FALALAR ALLAH, WATO ALJANNA, DA KUMA YARDARSA:Ba suna yinsu ne don wani abin duniya ba, wannan kuwa siffa ce ta badini, ba wanda ya isa ya san hakan sai mahaliccinsu shi kadai, domin kuwa aiki ne na zuciya, gashi Allah ya shedi zukatansu yadda suke, don haka ba wanda ya isa ya bayar da wani labari akasin hakan a karba.5- SABODA YAWAN SALLAH IDAN MUTUM YA DUBA FUSAKURSU ZAI GA HASKEN GURBIN SUJJADA:Domin kuwa idan mutum ya inganta badininsa ga Allah, to sai Allah ya kyautata zahirinsa ga mutane, su rika ganin yana ta haske da annuri.6- ADADINSU KADAN NE A FARKON MUSULUNCI, AMMA DAGA BAYA, SUKA RIKA HABAKA, SUKA YI YAWA HAR SUKA KAI MATSAYIN DA SUKA KAI:Don haka duk masu cewa Sahabban Ma’aiki wasu ‘yan tsiraru ne kawai, da basu fi a kirge su a tafukan hannu biyu ba, sun ci karo da abin da Allah yake gaya mana na misalin Muhammadu da Sahabbansa a cikin Linjila. Sannan suna nuna mana cewar Ma’aiki ya gaza wajen baiwa wadanda suke tare da shi kyakkyawar tarbiyar da tadace. (WAL’IYAZU BILLAH!!)7- SUNA CUNKUSAWA KAFIRAI HAUSHI DA BAKIN CIKI:Ko yaushe kafirai ba su son jin labarinsu, ko a fadi wani ci gaba nasu, sunayensu ma kawai suna tayar musu da hankali.Don haka ne ma Imam Malik ya bayar da fatawar cewa Shi’awa Rafida, masu kin Sahabban Ma’aiki (SallalLahualaihi wa sallama) kafurai ne,saboda suna bakin ciki da sahabban Ma’aiki, babu mai yin bakin ciki da su kuwa sai kafuri. (Allah ya kiyashe mu!).Abu ‘Urwatuz Zubairi ya ruwaito cewa: Mun kasance a majalisin Imamu Malik bn Anas, sai aka yi maganar wani mutum da yake kushe Sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama)sai Imamu Malik ya karanto wannan ayar, har ya kai inda Allah yake cewa: ( ﻟﻴﻐﻴﻆ ﺑﻬﻢ ﺍﻟﻜﻔﺎﺭ ) daga nan yace: “Duk wani mutum da zai wayi gari a zuciyarsa yana jin wani bakin ciki kan daya daga Sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama)to ya shiga cikin wannan ayar). [Tafsirin Kurdubi: 16/297].Ya zo a hadisin Abu Sa’idil Khudri Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallama)yana cewa: (Akul Kada ku soma zagin Sahabbai na! domin kuwa na rantse da Sarkin da raina yake hannunsa, da dayanku zai bayar da sadakar zinaren da girmansa ya kai kwatankacin dutsen Uhud, to ladan da zai samu ba zai kai kwatankwacin ciyarwar da daya [daga Sahabbai na] zai yi na Mudu guda daya, ko rabinsa ma ba). [Bukhari: 3673, Muslim: 2541].ﺃﻭﻟﺌﻚ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻭﺣِﺰْﺑُﻪ ﻭﻟﻮﻻﻫﻢُ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻣﺴﻠﻢﻭﻟﻮﻻﻫﻢُ ﻛﺎﺩﺕ ﺗَﻤِﻴﺪ ﺑﺄﻫﻠﻬﺎ ﻭﻟﻜﻦ ﺭﻭﺍﺳﻴﻬﺎ ﻭﺃﻭﺗﺎﺩُﻫﺎ ﻫﻢُﻭﻟﻮﻻﻫﻢُ ﻛﺎﻧﺖ ﻇﻼﻣﺎً ﺑﺄﻫﻠﻬﺎ ﻭﻟﻜﻦ ﻫﻢُ ﻓﻴﻬﺎ ﺑُﺪُﻭﺭٌ ﻭﺃَﻧْﺠُﻢ[ ﻣﻴﻤﻴﺔ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ]Allah ya kara mana son Sahabban Manzon Allah, ya hada mu tare da su ranar Kiyama.FADAKARWA:Ina so a wannan ayar da kuma ayoyin da bayaninsu zai zo (In sha’Allah) mu mayar da hankali sosai wajen lissafo siffofin da AllahMadaukaki da kansa ya baiwa Sahabbai abokanen zaman Ma’aiki (SAW); domin daga baya zamu zo mu duba mu gani, shin wadannan siffofi sun yi daidai da na Munafukai da wasu masu ciwon zuciya suke so su gwamutsa su, ko kuma sun yihannun riga da su?Kada kuma mu manta masanin abin da yake na bayyane da na boye shine ya yi bayanin wadannan siffofi da Kansa (JALLA JALALUH!)AYA TA BIYU DA TAKE BAYANIN GIRMAN KIRARI DA YABO DA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA YI WA SAHABBAN MA’AIKI SAW, ITA CE FADIN ALLAH MAI GIRMA:( ﻛﻨﺘﻢ ﺧﻴﺮ ﺃﻣﺔ ﺃﺧﺮﺟﺖ ﻟﻠﻨﺎﺱ ﺗﺄﻣﺮﻭﻥ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ﻭﺗﻨﻬﻮﻥ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﻭﺗﺆﻣﻨﻮﻥ ﺑﺎﻟﻠﻪ ).(Kun kasance al’uma mafi alheri da aka fitar wa mutane: kuna umarni da [aikata] alheri, kuma kuna hani ga mummunan aiki, kuma kuna yin Imani da Allah). [Al Imran: 110].Sahabban Ma’aiki (SAW) sune farkon wadanda suka shiga karkashin wannan ayar, saboda gare su aka fara fuskantar da maganar, Sahabbai sune mafi alheri dafalala fiye da duk wani karni da ya biyo bayansu; saboda Manzo shine fiyayyen manzanni, shiriyar da suke kai, babu wasu kafinsu da suke kan irinta.Ma’aiki SAW yace: (Mafi alheri cikin mutane sune jama’ar da suka rayu a karnin da nake). [Bukhari: 2652, Muslim: 2533] Wato Sahabbansa (RA).SIFFOFIN SAHABBAI (RA) DA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA BAYYANA A WANNAN AYAR:Dalilin da ya sanya Sahabbai da mabiyansu suka samu wannan yabo mai gwabi daga Ubangiji shine kasancewarsu:1) MASU UMARNI NE DA AIKATA ALHERI: Babban Umarni da aikata alheri shine umarni da Kadaita Allah da bautarsa shi kadai babu abokin tarayya, da kuma kiran jama’a zuwa addinin musulunci ta hanyar yada shi zuwa dukkanin sassa na duniya.(ZAN BADA ‘YAR GUNTUWARSURAR HAKAN DAGA BAYA).2) MASU HANI NE GA MUMMUNAN AIKI: Farkon abin da ya fi muni shine shirka, sannan kuma duk wani abu mummuna da shari’a ta yi hani a kansa.Al’ummun da suka gabata sun kasance sun yi sakaci sosai da wannan aikin mai girma, har Allah ya La’ance su, kamar yake cewa: (Sun kasance ba su hana junansu mummunan aikin da suka aikata. Hakika abin da suke aikatawa ya munana!). [Ma’idah: 79].Wadannan siffofi guda biyun farko (Umarni da abu mai kyau, da hani ga mummuna aiki) amfanuwar wasu ne, ba amfanin mai yinsu bane a asali, kenan Sahabban Ma’aiki sun samu kyakkyawartarbiya daga ma’aiki, wanda ya nuna musu cewa ka so wawaninka abin da kake so wa kanka, don haka domin wasunsu su amfana da shigacikin addinin musulunci, suma su samu wannan tsira da rabauta da su suka samu na yin Imani da Allah da ManzonSa – don hakan ne suka mike suka yi tsayuwar daka wajen isar da sakon Allah, da yada shi, tun Manzona duniya, har bayan wafatinsa (SAW).3). MASU IMANI NE DA ALLAH: su kansu sun siffantuta kamala, saboda sun yi Imani da Allah wanda shi yake basu damar aikata duk abin da Allah ya yi Umarni dashi, domin kuwa ba zaka kira wani zuwa hanyar tsira ba, sai kaima ka zama shiryayye. Wannan siffa kuwa raddi ne ga mushrikai, da suke bugar kirji kafin a bude Makka cewasune masu shayar da alhazai, kuma masu raya Masallacin Ka’ba, Allah yace:(Yanzu kun mayar da shayar da alhazai, da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda yayi Imani da Allah da ranar lahira, kuma ya yi Jihadi saboda Allah? Ai ba za su taba zama daya ba a wurin Allah) [Taubah: 19].KADAN DAGA CIKIN JAN AIKIN DA SAHABBAI SUKA YINA YADA ADDINI BAYAN WAFATIN MA’AIKI (SAW):1- Manzon Allah (sallalLahu alaihi wa sallama) yana yin wafati, sai yawancin wadanda suka karbi musulunci a tsibirin larabawa suka yi ridda, bayan kuma Ma’aiki bai yi wafati ba sai da yawancin garuruwan tsibirin larabawa suka rissina suka mika wuya ga addinin musulunci. Abin da zai nuna hakan shine masu Sirah sun bayyana yawan wadanda suka yi hajjin ban kwana tare da shi da cewa adadinsu ya zarta mutum dubu dari.2- Farkon jan aikin da Abubakar Siddiq (RA) ya fuskanta shine: yakar ‘Yan ridda, Allah ya bashi nasarar ganin bayansu, kwarjinin addinin musulunci ya dawo. Bayan cikin gida ya gyaru, saiya juya waje, domin ci gaba da isar da sakon Ma’aiki SallalLahu alaihi wa sallama. Wanda tuni Ma’aiki SAW ya fara shimfidar hakan ta hanyar tura wasiku zuwa dukwani Sarki cikin sarakunan kafirci, yana kiransu zuwa addinin musulunci.Abubakar Siddiq (RA) ya kasarindinar musulunci kashi biyu: Kashi na daya suka doshi kasar Iraq a karkashin jagorancin Khalid bnil Waleed, sun samu nasarar bude kudancin Iraq a lokacin. Kashi na biyu kuma sun nufi kasar Sham da jagorancin Yazeed bn Abi Sufyan, da Shurahbeel bn Hasanah, da Mu’awiya, da Amru bnil As, sun samu nasarar bude Sham a yakin “Yarmuka” wanda ya faru a lokacin da Abubakar Siddiq (RA) shi kuma ya yi wafati.3- A zamanin Umar bnil Khattab (RA) [13 – 23 AH]:Mu’awiya (RA) ya yaki Rumawa, ya bude Jazeerah, da Armeniya, da Azrabeejan.‘Iyadh bn Ganam ya shiga gumurzun yaki har yakai (Bahr Qazween) (Wanda kogine da kasashe biyar a yanzu suke kewaye da shi: Russia, Iran, Azrabejan, Turkumanistan da Kazakhastan).Amru bnil As ya bude Misra, a lokacin har rundunar musulmai sun kai gefen kasar Libiya suka shiga Tripoli, da Barqah.A can Iraqi kuma Sa’d bn Abi Waqqas ya jagoranci bude garuruwan da suka ragu, bayan ya yi kaca-kaca da rundunar farisawa a yakin Qaadisiyyah, ya murkushe gaba dayan jagororinsu. Musulmai suka ci gaba da kutsawa iyakokin kasar Iran, suka bude Khurasaan, da Ahwaz, da yankin Farisa, suka kara nausawa kudanci har sai da suka kai Makran da kuma kan iyakar garin Sind (Pakestan). Suka kuma nausa gabas har sai da suka bude Sijistaan (Afganistan). (Wannan duk a zamanin Umar RA) kenan.Mu’awiya (RA) ya nemi izini daga Umar (RA) ya kutsa cikin kogi, don yakar wadanda garuruwansu suke haure, amma Umar ya hana saboda hadarin da yake tattare da hakan.4) A zamanin Halifa Usman bn Affan (RA) an kara bude Khurasan, da Armeniya, da Azrabejan saboda sun nuna kiriniya da bijirewa. A zamaninsa kuma a ka bude: Ray, da Hamzan, da Dabristaan, da Jurjan, aka karasa bude gaba dayan Iran. Aka halaka sarki na daular Farisa wato Yazdajirdu bayan ya karade duniya yana ta guje-guje.A can Sham kuwa ‘yan garuruwa ne kadan suka ragu wadanda suke karkashin daular Rumawa suma Mu’awiya (RA) ya karasa bude su.A zamanin Usman (RA) har wayau ya bayar da izinin a kutsa ta kan kogi don yin Jihadi, ba tare da bata lokaci ba, sai Mu’awiya (RA) ya sanya tsarin rindina kashi biyu: Masu Jihadi a lokacin Zafi, da Masu Jihadi a lokacinsanyi, ya yi wannan tsarin ne don a ci gaba da yakar Rumawa ba yankewa. A shekara ta (27 Ah) ya samu nasara a kan Rumawa har saida ya isa kasar Qustantinia = Constantinople (Istanbul) ya kewayeta.A garin Akka da take hannun Israel a yanzu Mu’awiya ya gina ma’aikatar kera Jiragen ruwan yaki (Naval fleet), kuma aka ci nasarar kera babban jirgin ruwan yaki na farko a musulunci, manufarsa itace kutsawa kasashen turawa kamar su Cyprus da take kudu maso gabashin turai, da Arwaad datake kusa da garin (Tarsus) tacikin Syria.A Misra kuma rindinar musulunci ta ci gaba da nausawa yamma, tana kutsawa kasashen Afrika, karkashin jagorancin Abdullahi bn Sa’d bn Abi Sarh, inda ya karya rindinar Rumawa da jagorancin (Gregorius), ya bude garuruwa arewacin Africa har ya dangana da garuruwan kasar Moroco.5). A lokacin Aliyu bn Abi Talib (RA) saboda fitina da ta kunno kai a garuruwan musulmai, ba a samu an ci gaba da bude-bude ba, tun da sai gida ya gyaru sannan za’a gyara waje.WADANNAN BUDE-BUDEN DUK ANSU SAHABBAN MA’AIKI NE SUKA JAGORANCE SU KUMA DUKA-DUKA AN YI SUNE A CIKIN SHEKARU 25 KACAL. WADANNE IRIN MUTANE NE ZASU IYA KWATANTA IRIN WANNAN MURGUJEJEN AIKIN? KUMA IDAN AN BUDEGARI FA, BA WAI SHIKE NAN BA, A’A AKWAI MALAMAI A CIKIN SAHABBAI DA AKE TURA SU GARURUWA, SU KUMA AIKINSU SHINE SU KARANTAR DA MUTANEN GARIN AL’AMURAN ADDININMUSULUNCI. MAYAKA NE, KUMA MALAMAI NE; TA HAKA ADDININ MUSULUNCI YA YI YADUWAR DA BAI TABA IRINTA BA.LALLAI ALLAH YA YI GASKIYA:(Kun kasance al’uma mafi alheri da aka fitar wa mutane: kuna umarni da [aikata] alheri, kuma kuna hani ga mummunan aiki, kuma kuna yin Imani da Allah). [Aal Imran: 110].Allah ya saka musu da alheri,ya kara yarda a gare su, ya bamu ikon yin koyi da koyarwarsu, ya hada fuskokimmu tare da su a aljanna. Ameen Ya rabbal ‘Alameen.

Reply

« Back to forum