BID’AH (SHIMFIDA) (1)

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

BID’AH (SHIMFIDA) (1)

from nuramuhd3 on 04/27/2015 12:16 AM

BID’AH (1)Bismillahir Rahmanir Raheem. Wa Sallallahu ‘alan Nabiyyil Kareem, Wa ‘ala alihi wa Sahbihi wa man tabi’ahum bi ihsanin ila Yaumid-Din.Na lura ko yaushe akan tattauna game da abin da ya shafi “Bid’ah”, a lokuta da dama kuma tattaunawar takan yi zafi. Don haka na dauki alwashin komawa ga littattafan malamai magabata, don na yi tsinkayegame da maganganunsu game da wannan maudu’i mai matukar mahimmanci a rayuwar duk wani musulmi, wanda mutum yakan so ya samo bakin zaren don ya gyara addininsa.Gyaran addini kuwa shine kashin baya, kuma kan gaba wajen mahimmanci, don musulmi ya aiwatar da ibadakarbabbiya, wadda Allah zai yi masa tanadin ladarta zuwaranar gamuwa da shi; dominkuwa kamar yadda malamai suka ambata, Ibadar mutum ba zata zamo karbabbiya ba, sai ta hada sharuda guda biyu:1) Ikhlasi (Wato tsarkake niyya) ya zamo don Allah shi kadai aka yi ta, ba don waninsa ba.2) Biyayya ga Ma’aikin Allah, wato ya zamo ana bin koyarwarsa wajen duk wata ibada da za’a aiwatar.To maganar da ake yi game da ‘Bid’ah’ ya shafi sharadi nabiyu ne.Tattaunawa game da “Bid’ah”takan yi zafi, saboda wasu daga cikin masu magana a kanta, sukan kasa yin bincike na ilimi, sai ya zamo abin ya koma kai hari da musayar maganganu tsakanin bangarori masu mabambantan tunani, alhali kuwa malamai Rabbaniyyun tuni sun rigaya sun yi cikakkun bayanai game da ita. Maganar da nake son yi game da “Bid’ah” zai dauki salo na yin fida dalla-dalla, saboda a fahimci inda aka dosa, ina fatan jama’a za’a jure karanta abin da zan rubuta, duk da na san zai yi tsayi.Zan dogara wajen wannan binciken akan littattafan da malamai magabata masu zurfin ilimi wadanda suka kebance littattafan nasu musamman don magana game da ‘Bid’ah’, Sannan kuma uwa-uba komawa i zuwa littafin Allah, da Hadisan Ma’aiki (SAW) da maganganun Sahabbai (RA), da kuma littattafan da suka yikarin haske da bayani mai fadi game da BID’AH ko da kuwa ba a kanta kadai suka takaita ba, wato littattafan bangaren Akida.Ba zan iya daukar alkawari na lokaci da zan rika yin ‘Posting’ ba, saboda halin yauda kullum, kuma yanzu ne nafara wannan binciken, ba kuwa wani abu ne ya ja hankali na ba, sai ganin cewaakwai bukatuwa zuwa gare shi, saboda yawan tattaunawa da ake yi, har ta zamo abin da mai jajayen kunnuwa yake kira ‘CONTROVERSIAL ISSUE’.Don haka ina fata jama’a za’a yi hakuri idan an samu tsaiko, amma in Allah ya yarda zan yi iya kokari yadda zan iya, da fatan Allah ya bamu fahimta, ya sa mu yi karatu da idon basira da kuma niyyar isa zuwa gaskiya, domin kuwa ya zo a cikin doguwar wasiqar da Umar bnil Khattab (RA) ya turawa Abu Musal Ash’ari (RA) yana fadin cewa:ﻭﻣﺮﺍﺟﻌﺔ ﺍﻟﺤﻖ ﺧﻴﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻤﺎﺩﻱ ﻓﻲ ﺍﻟﺒﺎﻃﻞ“komowa bisa turbar gaskiyata fi alheri da mutum ya zarce kan batanci da yake kai”. [Duba: Ma’rifatus Sunanwal Athar na Baihaqi: 15/395.da I’lamul Muwaqqi’in na Ibnul Qayyim: 1/94].BID’AH (2)Kafin na shiga maganar ‘BID’AH’ kai tsaye, zan so na yi fadakarwa guda hudu:1). Mutumin da kai tsaye yake da damar tabbatarwa ko korewa game da abin da ya shafi “Bid’ah” shine malamin da Allah ya hore masa ilimi na Qur’ani da sanin tafsiran magabata, da Usuluddin, da Hadisi, da Lugar larabci, da fannin Usulul Fiqh, da Maqasidush Shari’ah. Idan mutum bai lelleka wadannan bangarorinba, to zancensa game da wannan maudu’i zai iya zamowa bashi da ma’auni mai karfi, kuma bashi da nauyin da ya kamata ya samu.Wanda ya ke da ido a cikin wadannan fannonin shi zai iya yanke ya gano ‘Bid’ah’ da abin da ba ‘Bidi’a’ ba. Idan bahaka ba to sai dai mai magana ya dogara bisa maganganun malamai magabata masu zurfin sani cikin tabbatar da hakan ko korewa.2). Akwai littattafai da magabata suka rubuta su musamman game da ‘Bid’ah’,daga cikinsu:i. ( ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻭﺍﻟﻨﻬﻲ ﻋﻨﻬﺎ ﻻﺑﻦ ﻭﺿﺎﺡ )Al- Bida’u wan-Nahyu ‘Anha –Na Ibnu Waddhah. (Abu Abdillahi, Muhammad bn Waddhah, al-Qurdubi al-Maliki. Ya rasu a shekara ta 287, ko 289 H).ii. ( ﺗﻠﺒﻴﺲ ﺇﺑﻠﻴﺲ ﻻﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ )Talbisu Iblisa – Na Ibnul Jawzi (Abul Faraj, Abdurrahman bn ‘Aliy bnil Jawzi al-Hambali, ya rasu a shekara ta 597H).iii. ( ﺍﻟﺒﺎﻋﺚ ﻋﻠﻰ ﺇﻧﻜﺎﺭ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻷﺑﻲﺷﺎﻣﺔ )Al-Ba’ithu ‘ala Inkaril Bida’ – Na Abu Shamah (Abdurrahman bn Isma’il bn Ibrahim ash-Shafi’i, ya rasu ashekara ta 665 H).iv. ( ﺍﻻﻋﺘﺼﺎﻡ ﻟﻠﺸﺎﻃﺒﻲ )ALi’tisaam- Na Shadibi (Abu Is’haq Ibrahim bn Musa al-Maliki, ya rasu a shekara ta 790 H).v. ( ﻣﻔﺘﺎﺡ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻓﻲ ﺍﻻﻋﺘﺼﺎﻡ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ ﻟﻠﺴﻴﻮﻃﻲ )Miftahul Jannah fiLi’tisami bis-Sunnah – Na Suyudi (Jalalud deen as-Suyudi ash-Shafi’i, ya rasu a shekarata 911 H).3). Littafin da ya fi kowane mahimmanci a cikin wadanda na ambato, da ma wadanda ban ambato su ba a nan shine littafin (AL’itisam – Na Shadibi). Domin kuwa duk wanda yake so ya fede biri har wutsiya game da maganar BID’AH lallai ne ya sanya wannan littafi cikin manyan littattafai na kan gaba da zai koma musu. Kuma ya kamata a ce duk wani dalibin ilimi ya mallaki wannan littafin…Sai dai wani hanzari ba gudu ba, shi wannan littafin a gaskiya, ba kowane mai koyon larabci bane zai daukeshi ya karanta ya kuma fahimci hakikanin inda marubucinsa ya sa gaba cikin bayaninsa, dole mai karatunsa ya zamanto ya gutsuri kadan daga cikin ilimummukan (Tafsir, Hadisi,Luga, Usulul Fiqh, Maqasidush-Shari’ah).Shehun Malami (Imamush-Shadibi) ya rasu ne kafin ya kammala wannan littafin nasa.4). Idan muka yi duba a hankali zamu ga cewa malaman mazhabar Malikiyya magabata, suna cikin wadanda suka ciri tuta na zamowa kan gaba, sannankuma suka tsananta bincike game da maganar “Bid’ah” da kuma ba da mahimmanci kwarai da gaske game da hakan; wannan kuwa ya samo asali ne tun daga tarbiyyar da Imamu Malik ya bayar ga almajiransa.Bayan wannan ‘yar karamar shimfida da na yi, a gaba Insha’Allahu zan shiga bayanigadan-gadan game da Bid’ah”. Ya Allah ka san raunin da muke fama da shi, ka tallafa mana gaba daya!!!

Reply

« Back to forum