fadakarwa
[ Go to bottom | Go to latest post | Subscribe to this topic | Latest posts first ]
fadakarwa
from nuramuhd3 on 04/02/2015 10:51 AMFAXAKARWAA cikin haluluwan da ya halatta a zubar da ciki a cikinsu. Kamar yadda ya gabata ya zama wajibi a samiizinin wanda yake da cikin a game da haka: kamar miji. A nan zamu taqaita abnda muka yi nufin rubuta shi a cikin wannan maudu’i mai mihimmanci, haqiqa mun taqaita shi a bisa tushen mas’alolon xa turakunsu, idan ba haka ba kuwa ai rassanta da yankunan ta da kuma abinda yake faruwa ga mata a game da wannan, wani kogo ne da ba shi da iyaka.Sai dai mai basira yana iya dawo da rassanta zuwa ga asalanta, da yankunanta zuwa ga kulliyarta da turkenta hanyar qiyasin abu-buwa da na zartarsu ta.Ya kamata mai bada fatawa ya sani cewa shi wasixa ne tsakanin Allah da halittarsa acikin isar da abinda Manzon Allah (S.A.W.) ya ya zo da shi da bayaninsa ga halitta. Kuma (ya sani) shi abin tambaya ne game qur’ani dasunnah domin sune abbuwa guda biyu kaxai da aka qallafawa bayi fahimtarsu daaiki da su, kuma duk abinda ya savawa Qur’ani da sunnahya wajaba a mayar da shi ga wanda ya faxe shi, baya halatta a yi aiki da shi koda kuwa wanda ya faxe shi abin yiwa uzuri ne da ijtihadi, za’a bashi lada a bisa ijtihadinsa, sai dai waninsa wanda ya san cewa kuskure ne, to, bai halatta ya karve shi ba.Yana wajaba ga mai bada fatawa ya tsarkake niyyarsa ga Allah Ta’ala kuma ya nemitaimakonsa a dukkan abinda ya faru gare shi, ya roqi Allahtabbata da dacewa ga dai-dai.Yana wajaba a gare shi ya zamo bigiren qiyasin sa ya samo shi ne daga abinda yazo a cikin Qur’ani da sunnah yayi nazari ya kuma yi bincike a cikin wannan ko kuma a cikin abinda ake neman taimako da shi daga zancen ma’abota Ilimi abisa fahimtarsu ga (Qur’ani da Sunnah). Haqiqa da yawa wata mas’ala daga cikin mas’aloli tana faruwa sai mutum ma yayi bincike a kanta cikn abinda yake da ikodaga maganganun ma’abota Ilimi. Sannan ya zamao bai sami abinda ya nutsu da shi ba a cikin hukuncin ta. Kuma da yawa ma baya samun ambatonta ma gaba xaya, amma idan ya koma ga Qur’ani. Da Sunnah sai hukuncinta ya bayyana a gareshi a kusa kuma a zahiri,wannan kuwa (yana faruwa ne) gwargwadon Ikhlasi da Ilmi da fahimta.Yana wajaba ga mai bada fatawa ya bi a sannu cikin hukunci yayin rikicewar al’amura kuma kada ya yi garaje da yawa wanda yayi hukunci da garaje sannan bayan lokaci kaxan sai ta bayyana a gareshi cewa yayi kuskure a cikinsa sai yayi nadama a bisa haka. Kuma sau da yawa bashi da ikon riskar (gyaran) abinda ya bada fatawa da shi.Mai bada fatawa idan mutane suka sanshi da yin sannu-sannu da Tabbata, sai su amince da maganarsa su kafa hujja da shi. Amma idansuka ganshi mai garaje to, duk mai garaje yana da yawan yin kuskure, saboda haka sai ya zamo basu da amincewa da abinda ya basufatawa da shi, sai ya zamo saboda garajensa ya haramtawa kansa da ma waninsa abinda yake wajensa na Ilimi da dacewa.Muna roqon Allah Ta’ala ya shiryar da mu da ‘yan uwan mu Musulmi ga tafarki madai-daici kuma ya jivinci lamuranmu da taimakonsa ya kuma tsaremu daga zamewa da kiyayewarsa, lallai shi mai yawan baiwa nemai girma.Allah yayi salati da Aminci gaAnnabin mu Muhammadu (S.A.W.) da Alayensa da Sahabbansa baki xaya. Godiya ta tabbata ga Allah wanda da ni’imarsa kyawawan ayyuka suke cika

Reply