FIYAYYEN MAI BA DA TARBIYYA

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

FIYAYYEN MAI BA DA TARBIYYA

from nuramuhd3 on 04/27/2015 12:20 AM

بسم الله الرحمن الرحيم(1). FIYAYYEN MAI BA DA TARBIYA, MA’AIKI (SAW) YA KASANCE IDAN YA YI UMARNI DA ABU, YAKAN ZAMO KAN GABA WAJEN AIWATAR DA SHI, YAKAN HADA:UMARNI, DA AIKI:a). Ranar Sulhun Hudaibiya, bayan an kammala yarjejeniyar sulhu da kafurai,an yarda da cewa musulmai zasu koma Madina, ba zasu yi umara ba har sai shekara ta kewayo, Ma’aiki (SAW) ya umarci Sahabbansa (RA) da su yi aski ko saisaye don su sauke ihraminsu a wannan wurin ba tare da sun shiga Makka ba, sai ya zamo ba su yi gaggawar aikata hakan ba; saboda abubuwan da suka faru sun yi musu nauyi… Ma’aiki (SAW) ya shawarci matarsa Ummu Salamah (RA) game da hakan, sai ta ceya fita ya sanya wanzaminsa ya yi masa aski, ba tare da yakula kowa ba… a lokacin da Sahabbansa (RA) suka ga haka sai nan da nan suka bi umarnin da ya yi musu, kowaya aikata yadda Ma’aiki (SAW) ya aikata.b). A yakin Khandaq, lokacin da ake aiki, Ma’aki (SAW) bai zauna ya zuba musu ido ba da kansa ya rika aiki tare da Sahabbansa (RA), don ya nishadantar da su wajen aikin, sannan kuma su yi koyida shi. Wannan ya koyar da cewa idan muka yi umarni dakyakkyawan aiki mu rika kokarin aiwatarwa daidai iyawarmu. Haka nan idan muka yi hanin mummunan aiki, muma lallai mu guje shi.MISALI: IDAN MUKA UMARCIYARO DA YIN SALLA, YA SAME MU A KAN GABA WAJEN KOKARIN AIKATAWA, TO LALLAI ZAI YI KOKARIN KOYI DA MU… IDAN MUKA CE MASA BUSA SIGARI BA KYAU YA GANMU DUMU-DUMU MUNA YI, TO LALLAI ZA’A FADI BA NAUYI, ZAI DAINA KIMANTA MAGANARMU…(2). FIYAYYEN MAI BA DA TARBIYYA, MA’AIKI (SAW) YAKAN ZABURAR DA SAHABBANSA (RA) WAJEN AYYUKAN BIYAYYA, YAKAN YIMUSU TAMBAYOYI DON NISHADANTAR DA SU DA KARA MUSU KAIMI:An karbo daga Abu Hurairah (RA) yace: Ma’aiki (SAW) yace: (Yau kuwa waye ya tashi da azumi a cikinku?) SaiAbubakar (RA) yace: Nine. Sai Ma’aiki (SAW) ya kara cewa: (To waye kuma ya bi jana’iza a cikinku?) Sai Abubakar (RA) ya ce: Nine. Sai ya kara cewa: (To waye kuma ya ciyar da miskini a cikinku?) Sai Abubakar (RA) yace: Nine. Sai ya kara cewa: (To waye kuma ya je duba maras lafiya a cikinku?) Sai Abubakar (RA) yace: Nine. Daga nan Annabi (SAW) yace:(Mutumin da zai hada wadannan [ayyuka na alherin] lallai ZAI SHIGA ALJANNA). [Muslim: 1028].Duba mazaje don Allah! Ya Allah ka kara mana kaunarsu, ka bamu ikon yin koyi da su!Mu duba kyawun wannan hanya ta tarbiya daga fiyayyen mai ba da tarbiya: BIBIYAR WADANDA AKE TARBIYYANTA DA DAMUWA DA LAMURANSU… wanda ya ‘dan gaza a zaburar da shi, wanda kuma ya yi bajinta a bashi lambar girma da yabo: ‘… ZAI SHIGA ALJANNA’ Mu duba himma kasaitacciya ta wadanda ake tarbiyyanta (Sahabbai RA)… mu duba rigengeniyarsu wajen biyayya ga Allah… musamman AS-SABIQUNAL AWWALUN, wanda Abubakar(RA) yake can kololuwar mataki a cikinsu… (Ya Allah ka kara yarda a gare su gaba daya).(3). FIYAYYEN MAI BA DA TARBIYYA, MA’AIKI (SAW) YA TARBIYYANCI SAHABBANSA (RA) SU NEMI BABBAN MATSAYI… YAKAN ZABURAR DA SU DON SU KARA KAIMI A AYYUKAN ALHERI:An karbo daga Sahl bn Sa’d as-Sai’idi (RA), Ma’aiki (SAW) a ranar [yakin] Khaibar yace: (Wallahi! gobe zan baiwa wani mutum tutar [yaki], shi [wannan mutumin] yana son Allah da Manzonsa, kuma Allah da ManzonSa suna sonsa, Allah zai bude [garin] a hannunsa).Da yake tarbiyyar makarantar Manzon Rahamane, kuma ya ba su tarbiyya tayin rigengeniya matukar aikin alheri ne… Wannan maganar ta ja hankulan gabadayan Sahabbai (RA)… dominkuwa kwana suka yi cir suna tattauna ta … KO WANENE ZAI RABAUTA DA WANNAN BABBAN MATSAYI A CIKINMU!Da aka wayi gari da duku-duku, dukansu suka dunguma zuwa wajen Ma’aiki(SAW) KOWA YANA SO A NUNA SHI DON YA JAGORANCI YAKI. Sai yace: (Ina Aliyu bn Abi Dalib?) Sai aka ce da shi: “Ya Ma’aikin Allah! Ai yana can yana ta fama da ciwon ido”. Sai yace:(A kirawo shi). Aka zo da shi, sai ya yi masa tofi a idanunsa, ya yi masa addu’a. Nan da nan ya warke kamar bai taba ciwo ba. daga nan ya bashi tuta. Sai Aliyu (RA) yace: “Ya Ma’aikin Allah! Kana so na yi ta yaki da su har sai sun zamo kamarmu? Sai yace: (Jeka a nutse! ka shiga fagensu, daga nan ka yikiransu zuwa musulunci, ka fada musu abin da ya wajabaa kansu na hakkin Allah. domin kuwa na rantse da Allah! shiriyar mutum daya tilo shi ya fi maka alheri fiye da samun jajayen rakuma = dukiya mai tsananin girma da kima=). [Bukhari: 7/544].Allahu Akbar! Kun ji bayanai na Manzo mai tausayin al’umarsa, ba wai a yi ta yaki shi ya damu da shi ba… A’a, a samu a tserar da su daga shiga wuta.BAYAN NAN KUMA:* Daukakar himmar wadanda ake tarbiyyanta… jan hankulansu wajen nemanmanyan matsayi… sanya su yin rigingeniya bisa ayyukan alheri… GOBE ZAN BAIWA WANI MUTUM TUTA… ALLAHDA MANZONSA SUNA SONSA, SHIMA YANA SUNSU.* Dimbin falalar Aliyu (RA)… ingantacciyar shaida gare shidaga bakin farin jakada.* Mahimmancin kira zuwa addinin Allah, da shiriyar da mutune zuwa gare shi… shine ake musabaka dominsa ….ﻟﻤﺜﻞ ﻫﺬﺍ ﻓﻠﻴﻌﻤﻞ ﺍﻟﻌﺎﻣﻠﻮﻥ .… ﻭﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻓﻠﻴﺘﻨﺎﻓﺲ ﺍﻟﻤﺘﻨﺎﻓﺴﻮﻥ(4). FIYAYYEN MAI BA DA TARBIYYA, MA’AIKI (SAW) YAKAN JA HANKALIN SAHABBANSA (RA), YA NUSAR DASU ABIN DA YA FI MAHIMMANCI…IDAN SUKA YI MASA TAMBAYA, YA GA CEWA AKWAI ABIN DA YA FI DACEWA SU SANI, YANA BASU AMSA DA ABIN DA YA FI DACEWA:Anas (RA) ya ruwaito cewa wani balaraben kauye ya yi wa Annabi (SAW) tambaya yace: “Ya Ma’aikin Allah! Yaushe ne tashin alkiyama?”. Sai Ma’aiki (SAW)yace da shi: (Ko me ka yi tanadi [na aiki] don fuskantarwannan ranar?). Sai yace: “Kaunar Allah da Ma’aikinSa”.Sai yace: (To kana tare da wadanda kakaunace su [a can])…WAI! ME SUKE JI HAKA?! Ai kuwa Sahabbai (RA) basu taba jin kalmar da ta yi musumatukar dadi irin wannan ba, kamar yadda hausawa kecewa: su zuba ruwaa kasa su sha… murna da farin cikin jin wannan amsa ta Manzon rahama (SAW)… ‘KANA TARE DA WADANDA KA KAUNACE SU’.Anas (RA) yace: “Ni kam ina kaunar Annabi (SAW), da Abubakar, da Umar, kuma ina fatan na kasance tare da su, saboda kaunarsu da nake; duk da dai na sanban yi aiki irin nasu ba”. [Bukhari: 3688, Muslim: 2639].Lallai farin ciki, murna da jin dadi sun lullube sahabbai (RA); saboda SONSU da KAUNARSU ga Allah da ManzonSa, da kuma Salihan bayin Allah… KA JITARBIYYAR BABBAR MAKARANTA!Ba sanin yaushe za’a tashi alkiyama ba… abin da ya fi shi mahimmancin shine abinda muka tanada na ayyukan alheri don fuskantar wannan rana.Kaunar Allah da Ma’aikinSa (SAW) da bayin Allah na gari,mutanen kirki, rayayyunsu da matattunsu abu ne mai girman falala; domin Allah yana sakawa bawa da“KASANCEWA TARE DA SU A MASAUKI DAYA”:ﺟﻨﺔ ﻋﺮﺿﻬﺎ ﺍﻟﺴﻤﺎﻭﺍﺕ ﻭﺍﻷﺭﺽ(5). FIYAYYEN MAI BADA TARBIYYA, MA’AIKI (SAW) BAI TARBIYANTAR DA SAHABBANSA (RA) KAN MUZANTA JAMA’A BA… IDANSUKA AIKATA ABU DA YAKEBUKATAR GYARA, YA GANI, KO AKA BASHI LABARI, YAKAN NUSAR DA SU BA TARE DA KAMA SUNA BA… SABODA KWAREWA WAJEN IYA NASIHA… YAKAN CE:(ME YA SA NE WASU SUKE MAGANGANU HAKA?!…)Mutane uku cikin Sahabbai (RA) sun zo gidan Ma’aiki (SAW) suna tambayar yadda yake ibada don shine abin koyinsu, aka basu labarin yadda yake yi, sai sukaga kamar hakan ya yi kadan…Sai dayansu yace: Ni zan faratsayuwar dare, ba fasawa har abada…Na biyun kuma yace: ni kumazan rika yin azumi kullum ba cin abinci da rana…Na ukun yace: Ba zan yi aure ba har na mutu…Da aka baiwa Ma’aiki (SAW) labari, sai ya tara jama’a ya yimusu huduba yace: (Meneneya samu wasu mutane har suke maganganu haka! Bari na baku labari,ni nakan yi salla kuma na yi barci… nakan yi azumi kuma wataran na wayi gari baki bude… ina kusantar matana. Duk kuwa wanda ya kyamaci sunnata to ba shikan shiriya ta). [Bukhari: 5063, Muslim: 1401].FIYAYYEN MAI BA DA TARBIYYA! YA ISAR DA SAKO,BAI KAMA SUNA BA, BALLANTANA WADANDA AKE MAGANAR DON SU SU KUNYATA, DAGA BAYA SU RIKANISANTAR MUTUM, SABODATSORON CIN FUSKA DA MUZANTAWA.(6). FIYAYYEN MAI BA DA TARBIYYA, MA’AIKI (SAW) YA TARBIYYANTAR DA SAHABBANSA (RA) SU YI BIYAYYA SAKAKKIYA GA ALLAH DA MANZONSA (SAW)SUKADAI. WANINSU KUWA (SHUGABANNI, IYAYE… DA SAURANSU) ANA YI MUSU BIYAYYA NE MAI DABAIBAYI, DOMIN KUWA BA’A BIYEWAWANI ABIN HALITTACIKIN DUK WANI ABU DA YAKE SABO NE GA MAHALICCI. KUMA ANA YIWA ABIN HALITTA BIYAYYANE CIKIN ABU MAI KY…AU (WADDA SHARI’A TA YARDADA SHI);An karbo daga Aliyu (RA) yace: Annabi (SAW) ya tura wata rindina, ya sanya wani mutum Ba’ansare ya shugabance ta, yace su rika yi masa biyayya. Sai [waniabu ya hado su da sojojinsa] ya yi fushi da su, yace musu: ‘Ba Annabi (SAW) ya umarce ku ku yi mini biyayya ba?’ Suka ce: Eh haka ne. Sai yace:‘Yanzu ina soku hado kirare, ku rura wuta,ku shige cikinta’. Sai suka hado kiraren, suka rura wuta, da suka zo shiga sai suka yi turus gaba dayansu, wasunsu suka ce: ‘Mu famun yi imani da Annabi (SAW) ne don mu tsira daga wutar [Allah] yanzu ma shigawannan?’. Suna cikin haka har wutar ta mutu, shi kuma [shugaban nasu] yahuce. Da aka fadawa Annabi (SAW) sai yace: (Da sun shigawannan [wutar] da ba zasu fita ba har abada, ai biyayya ana yinta ne cikin abu mai kyau [da yadace da shari’a] ba cikin sabawa Allah ba). [Bukhari: 4340, Muslim: 1840].

Reply

« Back to forum