fsl 6

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

fsl 6

from nuramuhd3 on 04/02/2015 10:46 AM

FASALI SHIDAA CIKIN (JININ HAIHUWA) DA HUKUNCINSANifasi da shine: jinin da mahaifa take fitarwa yayin haihuwa, ko a lokacin haihuwa ko bayan ta, ko kafin ta da kwana biyu ko ukuShaikhul Islam Bn Taimiyya yace: Amma idan ta ganshi a yayin da take haxuwa a cikin haihuwa, to, nifasi ne, kuma ba’a iyakance shi da kwana. Biyu ko uku ba”. abinda yake nufi shi ne haihuwa ta biyo shi, idan ba haka ba, to, ba nifasi bane, malamai sun yi savani a bisa cewa shin yana da iyaka ne a mafi qarancinsa ko mafi yawansa?Shek Taqiyyuddeen ya faxa a cikin Risalarsa (shafi na 27): Nifasi bashi da haddi a mafi yawansa, da za’a kaddara cewa mace ce ta ga jini fiye da kwana arba’in ko sittin ko saba’in ya yanke, to, nifasi neSai dai idan ya zarce, to ya zama jinin cuta, sai a iyakance shi da kwana arba’in, wanda shi ne galibin abin da ya zo a Shari’ah. Sai nace: Abisa wannan idan jininta ya qaru a bisa kwana arba’in kuma ya zamo tana iyaka da yankewar sa bayan (kwana arba’in xin) ko kuma alamomi suka nuna yana kusa da yankewa to, sai ta saurara har sai ya yanke, idan bai yanke ba sai tayi wankanta yayin cikar kwana arba’in domin shi ne mafi rinjaye.Sai dai idan ya dace da lokacin hailarta sai ta zauna hr lokacin hailarta ya qare, idan kuma ya yanke bayan wannan, to, abinda ya kamata shi ne ya kasance kamar al’ada gareta, sai tayi aiki da lissafinsa a gaba, idankuma ya zarce, to, ita mai istahadaha ce tana komawa ga hukuncin mai istahadha da ta gabata. Kuma da zata yitsarki da yankewar jinin. To, ita mai tsarki ce koda kafin kwana arba’in ne, sai ta yi wanka ta yi sallah tayi azumi,kuma mijinta ya tara da ita, sai dai idan yankewar ta kasancce qasa da wuni guda,to, babu hukunci a gare shi, (ya faxe shi a cikin al-Mugniy).Nifasi baya tabbata sai idan ta haife abinda halittar mutum ta bayyana a cikinsa, da zata haife wani abu wanda halittar mutum bata bayyana a cikinsa ba to, jininta ba nifasi bane, jinin cuta ne sai hukuncinta ya kasance hukunci mai istahadah. Mafi qarancin lokacin da halittar mutum take bayyana a cikin sa shi nekwana tamanin daga xaukar ciki. Galibinsa kuma shi ne kwana casa’in, Majd Bn Taimiyyah yace: “Idan taga jini a bisa gurbin haihuwa gabaninsa ko bayansa kada ta damu, ta kame daga yin sallah da azumi, sannan idanal’amari ya, yaye a gareta bayan haihuwa bisa savanin zahiri sai ta dawo, ta riskar idan kuma al’amarin bai yayeba sai hukuncin zahir ya zarce ba tare da komawa ba. (an ciro shi daga gare shi a cikin sharhin iqna)Hukuncin Nifasi:Hukuncin Nifasi kamar hukuncin haila ne dai-dai da,dai-dai sai dai a cikin abubuwan da za suzo: na farko: iddad ana lura da saki bada Nifasi ba, domin cewa idan saki ya kasance kafin haihuwa to idda ta qare da haihuwa ba da nifasi ba, idankuma saki ya kasance bayan haihuwa ne, to, sa ta saurari komowar haila kamar yadda ya gabata.Na biyu: lokacin ILA’I., ana lissafinsa daga lokacin haila, ba’a lissafinsa da lokacin Nifasi.ILA’I, shi ne mutum yayi rantsuwa a bisa daina yin jima’i da matarsa har abada ko zuwa wani lokaci da ya wuce watanni, huxu, iddan ya rantse, kuma ta nemi shi da yin jima’i (da ita yaqi) sai abashi lokaci tsayin watanni huxu daga lokacin da ya rantse, idan lokacin ya cika sai a tilasta masa saduwa da ita ko ya saketa. Wannan lokaci idan nifasi ya wuce wamace, ba’a lissafi ga miji ana qarawa a bisa watanni huxu gwargwadon lokacin sa bavanin haila, shi lokacinsa tana lissafi da shi ga miji.Na uku: Balaga tana tabbata da haila bata tabbata da nifasi, domin ba zai yiwu ba ga mace ta xauki ciki har sai ta kai lokacin yin inzali, saboda haka abkuwar balagayana ga yin inzali wanda ya gabaci xaukar ciki.Na huxu: shi jinin haila idan ya yanke sannan ya dawo to hailar ce ( ta dawo) bisa yaqini. Misali a al’adarta ta kasance kusan takwas (take yi) sai taga haila kwana huxu,sannan ta yanke kwana biyu,sannan ta dawo a rana ta bakwai da ta takwas to, wannan jinin da ya dawo haila ce bisa yaqini kuma hukunci haila ya tabbata a gare shi: Amma shi jinin nifasi idan ya yanke kafin kwana arba’in sannan ya dawo a kwana na arba’in, to, akwai shakka a cikinsa, don haka ya wajaba a gareta ta yi sallah tayi azumin farilla a lokacinsa. Kuma abinda ya haramta ga mai haila ya haramta gareta, banda abubuwan da suka wajaba, kuma bayan tsarkinta sai ta rama abinda ta aikata shi a cikin wannan jini. Daga abinda ya wajaba mai haila ta rama shi. Wannan shine mashahuri a gurin faqihai dahanabila.Amma abin da yake dai-dai shi ne idan jini ya dawo mataa lokacin da zai yiwu ya kasance nifasi ne, to nifasin ne, idan ba hak ba kuwa to, haila ne, idan kuma ya zarce mata to, zai iya zama istahadha ne, Wannan shi nemafi kusa da abinda aka ciro shi a Al-muguniy daga Malik yace: Idan taga jini bayan kwana biyu ko kuma uku, yana nufin daga yankewarsa, to, nifasi ne, idan ba haka ba kuwa to haila ne.Wannan shi ne haqiqar zavinShaikhul Islam Bn Taimiyya. Babu wani abu a cikin jini wanda za’a yi kokwanto a cikinsa a yadda ake gani sai dai mutane suna savani a cikinsa gwargwadon Iliminsuda kuma fahimtarsu. Qur’ani da Hadisi a kwai bayanin komai a ciknsu. Allah bai wajabtawa wani mutum yin azumi ko yin xawfi sau biyu ba, sai dai idan ya kasance an sami rauni a na farkon ta yadda baza a iya riskarsa ba sai an rama. Amma yayin da bawa ya aikata abinda zai iya aikatawa daga cikin abinda aka kallafa masa gwargwado iyawarsa, to, ya kuvutar da zimmarsa, kamar yadda Allah Ta’ala ya ce:“Allah baya xorawa wata nimfashi sai abinda zata iya”(1)kuma yace:“Kuji tsoron Allah gwargwadon iyawarku”(2) Bambanci na biyar a tsakanin Haila da Nifasi: ita mai haila idan ta sami tsarki kafin cikar kwanakin da ta saba, to, ya halatta mijinta yasadu da ita ba tare da wani qi ba.Amma mai nifasi idan ya sami tsarki kafin kwana arba’in an qi mijinta ya sadu da ita a bisa mashahuriyar magana a wata mazahaba. Amma abin da yake shi ne dai-dai ba’a karhanta mijinta ya dadu da ita ba wannan shine abin da jamhurun malamai suka faxa, domin karhanci hukunci ne na shari’ah wanda yake buqatar da lili na shari’ah, kuma a cikin wannan mas’ala babu wani dalili na shari’ah face abinda imam Ahmad ya rawaito shi game da matar Uthman Bn Abil Ass cewa ita ta je wajens akafin ta cika kwana arba’in da haihuwa, sai yace: Kada ki kusance ni” Wannan al-amari baya nuna lazamta karhanci domin yanaiya kasancewa shi yana tsoron cewa ita bata tabbata da samun tsarkinta ba, ko kuma (yana tsoron) jini yana iya motsawa (ya dawo) ko daisaboda wani dalili da shi ya sami. Allah shi mafi sani.

Reply

« Back to forum