guziri

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

guziri

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:47 AM

Tarbiyya1بسم الله الرحمن الرحيموالصلاة والسلام على عبدالله ورسوله نبينا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين(A). YADDA AKE YIN MURAJA’AR ALQUR’ANIAlqur’ani yana bukatar muraja’a kuma idan mutum ba ya yin muraja’a zai iyamanta duk abin da ya haddace, saboda shi al-qur’ani kamar rakumi ne idan ka rike akalarsa sai ya bika, idan kuma ka sake shi sai ya gudu, don haka idan mutum ya haddace alqur’ani yana da babban aiki akansa na yawan maimaita abin da ya haddace, kamata ya yi ka dinga hada hadda da muraja’a a lokaci daya don kar kana haddace wani wuri na baya yana rushewa, daga cikin hanyoyin muraja’a akwai:– Idan zai yiwu ka kasa al-qur-ani gida uku, kashin farko daga Suratu Annas zuwa Ankabut, kashi na biyu daga Suratul Kasas zuwa Yunus, kashi na uku daga Suratu Attaubah zuwa Baqara.– Idan ka haddace izu ashirin, kar ka cigaba sai ka yi kamar wata kana maimaitashi, wannan zai taimaka wajan karfafa haddarka.– Idan ka haddace izu arba’in, kar ka cigaba sai ka yi kamar wata biyukana maimaita shi, wannan zai sa haddarka, ta yi kwari.– Idan ka haddace al-qur’ani gaba daya ka yi kokari ka matsawa kanka, wajan yin bitar wani bangare na al-qur’ani kullum, kamar izu biyu kulum ko makamancin haka, duk kuma ranar da ba ka yi ba, ka yi kokari ka rama.(Duba : khuduwatun ilassa’adah 195-196)(B). KA’IDOJIN HADDACE AL-QUR’ANI– Ya wajaba Dalibi ya rinka yin hadda a wajan malami saboda ya dinga gyara masa.– Ka da Dalibi ya dinga haddace abu mai yawa, musamman farkon fara haddarsa, saboda wannan zai jawo ya yi hadda mara karfi, ya kamata ya dinga yi daidai yadda zai iya yin muraja’a sosai, don ya inganta haddarsa.– Idan dalibi zai fara hadda ya fara daga suratu Annas saboda ta fi sauki.– Ya rinka yin hadda da al-qur’ani iri daya, saboda zaisa shi ya dinga tuna gurin da kowacce aya ta ke, da kuma tuna inda kowanne shafi ya ke karewa.(Duba : khuduwatun ilassa’adah 200-201)(C). ADALCI YA KASU KASHI BIYU :1. Adalci wajan mu’amala da Allah 2. Adalci wajan mu’amala da bayinSa.– Adalci wajan mu’amala da Allah shi ne :1. ka bauta maSa yadda ya kamata.2. Ka da ka ce za ka yi jayayyada Shi a cikin siffofin da ya kebanta da su.3. Ka gode maSa shi kadai a cikin ni’imar da ya baka.4. Kada ka yi amfani da ni’imarSa wajan saba masa.5. Kada ka yiwa kowa cikakkiyar godiya sai Shi.6. Ka da ka bautawa kowa saiShi .– Adalci wajan mu’amala da bayinSa shi ne :1. Yin mu’amala da su da abin da kake so su yi maka mu’amala da shi.2. Ajjiye kowa a matsayinsa, ka sanya babba daga cikin musulmai ya zama babanka, matsakaicinsu kuma ya zamadan’uwanka, karaminsu kuma ya zama kamar ‘Da a wajanka, don haka sai ka girmama babanka, ka karrama dan’uwanka, ka ji tausayin danka.YI NAZARI DON KA GA GWARGWADON ADALCINKA.(D). ABUBUWA GUDA GOMA SUNA KARIYA DAGA SHAIDANIbnul kayyim yana cewa : bawa yana samun kariya daga Shaidan da abubuwa guda goma :1. Neman tsari da shi kamar yadda Allah ya yi umarni da hakan a al’qur’ani.2. Karanta kula’uzai guda biyu.3. Karanta ayatul kursiyyu4. Karanta suratul bakara.5. Karanta ayoyi biyun karshena suratul bakara.6. Karanta ayoyi uku na farkon suratul Gafir.7. Karanta Laa’ilaha illallahu wadahu laa shariikalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa alaa kulli sha’in kadeer, sau dari.8. Yawan ambaton Allah9. Yin alwala lokacin sallah.10. Barin kallo da zancen da ba shi da amfani, da abincin da ya wuce bukata, da barin cakuduwa da mutane, sai gwargwadon bukata.(E). HAKURI YA KASU KASHI UKU1. Hakuri akan biyayya ga Allah, sau da yawa mutum zai ji wahala da nauyi wajan aikata wasu daga cikin abubuwan da Allah ya umarce shi da su, kamar yin alwala da kuma sallar asuba a lokacin tsananin sanyi, da fitowa sallar azahar a lokacinda ake tsananin zafi, dole sai ya yi hakuri da juriya kafin yaiya aikatawa.2. Hakuri wajan barin abin daAllah ya hana, sau da yawa zuciyar mutum za ta ji tana sha’awar abin da Allah ya haramta, duk wanda ya yi hakuri ya bar abin da Allah ya hana, to zai ba shi mafi alkairinsa a Lahira, wanda yabar giyar duniya mai wari Allah zai shayar da shi giyar lahira mai kamshi, wanda ya bar matan banza masu kwailin aduniya Allah zai aura masa matan aljanna tsarkaka, kyawawa masu manyan ido, wadanda wani namiji kafin shi bai taba taba su ba, idan ‘yan aljanna su ka shiga aljanna mala’iku za su shiga wajansu, su ce musu ” Amincin Allah ya tabbata a gare ku, saboda hakurin da kuka yi (akan abin da Allah yaumarta da barin abin da Allah ya hana) ” Suratu Arra’ad aya ta 243. Hakuri akan musifu da bala’o’in da Allah ya jarabceka da su, duniya gida ne na jarrabawa, duk lokacin da farin ciki ya sameka sai kagodewa Allah ka samu lada, idan bakin ciki ya sameka ka yi hakuri saikasamu lada, dole ne mutum ya yi imani da kaddara komai dacinta, kuma imaninsa ba zai cika basai ya yarda da ita. Allah yana jarrabar mutum gwargwadon imaninsa, Annabi tsira da amincinAllahsu tabbata a gare shi yana cewa “wadanda aka fi jarrabasune Annabawa, sai kuma wadanda suke bin su wajan nagarta, haka dai zuwa wadanda suke bi” Tirmizi da Ibnu Hibban.Ka zama mai hakuri akan duka wadannan guda ukun, Allah yana cewa : “Ana cikawa masu hakuri ladansu ba tare da kidayawa ba” Suratu Azzumar aya ta 10(F). GINSHIKAN GODEWA NI’IMAR ALLAH GUDA BIYAR NEIbnul kayyim yana cewa : godiya ga Allah ta ginu ne akan ginshikai guda biyar :1. Kaskantar da kai ga wandaya yi maka abin,wato Allah.2. Nuna soyayya gare shi.3. Yin furuci da ni’imar da ya yi maka.4. Yabonsa da ni’imar da ya yi maka.5. Kar ka yi amfani da ni’imarta sa wajan abin da yake ki.Yin furuci da ni’imar Allah yana daga cikin abubuwan da su ke kara yawan ni’imomin da Allah ya yi maka, wani daga cikin magabata yana cewa : “Godewa ni’ima yana kare maka ni’imar da kake ciki, sannan kuma yana farauto ni’imar da ba ka cikinta”. Dukkan wani abu da kake amfana da shi a rayuwarka ta yau da kullum wani bangare ne na na’imomin Allah, Allah yana cewa : “Idanda za ku kirga ni’imomin Allah, da ba ku iya kidaye su ba” (Suratul Ibrahim aya ta 34).Shin ka kan yi amfani da gabobinka wajan abin da Allah yake so, ko kuma ka kan saba masa da su, an tambayi JUNAID (daya daga cikin magabata) cewa me akenufi da godewa ni’imar Allah sai ya ce shi ne : “RASHIN YIN AMFANI DA NI’IMARSA WAJAN ABIN DA YA HANA”Abin da yake taimakawa wajan gode ni’imar Allah shi ne kallon na kasa da kai a wajan abin duniya, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: “KU DIN GA KALLON NA KASA DA KU, DOMIN HAKANSHI ZAI SA KU KI WULAKANTA NI’IMAR DA ALLAH YA YI MUKU” Tirmizi ne ya rawaito.(MADARIJUSSALIKIN 2244)(G). MUNANAN MUSIBUN DA ZUNUBAI SUKE JAWOWA (1)Allah madaukaki yana cewa : “Babu wata musiba da za ta same ku, face sai ta kasance daga abin da hannunku ya aikata ne” suratu Asshuraa aya ta 30. Zunubai suna jawobala’oi da yawa, wadanda suke cutar da zuciya da jiki, aDuniya da Lahira, ba wanda ya san adadinsu sai Allah, daga cikinsu akwai :1. Haramta samun arziki, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : “Bawa ana haramta masa arziki saboda zunubin da ya aikata”Ibnu majah ne ya rawaito kuma Albani ya inganta shi.2. Haramtawa mutum samunilimi Abdullahi dan Mas’ud yana cewa: (Ina saran mutum zai iya manta ilimin da ya sani saboda zunubin da yake aikatawa) kuma Imamu Shafi’i yana cewa:ﺷﻜﻮﺕ ﺇﻟﻰ ﻭﻛﻴﻊ ﺳﻮﺀ ﺣﻔﻈﻲ** ﻓﺄﺭﺷﺪﻧﻲ ﺇﻟﻰ ﺗﺮﻙ ﺍﻟﻤﻌﺎﺻﻲﻭﻗﺎﻝ ﺍﻋﻠـﻢ ﺑﺄﻥ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻧـﻮﺭ ** ﻭﻧﻮﺭﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﺆﺗﺎﻩ ﻋﺎﺻــﻲMa’ana:Na kai karar munin haddata wurin waki’u (malaminsa ne)# sai ya shiryar da ni zuwa barin zunubai.Kuma yace ka sani ilimin haske ne # hasken Allah (s.w.t.) ba’a bawa mai sabo1. Haramtawa mutum aikata alkairi, saboda zunubi kamarabinci ne mai cuta a ciki, wanda idan ka ci guda daya, to zai iya hanaka cin wani mai dadi, Al-fadlu bn iyadh yana cewa :”Duk sanda ka ga ba ka iya tsayuwar dare to katabbatar zunubai ne su ka dabaibaye ka”(H). MUNANAN MUSIBUN DA ZUNUBAI SUKE JAWOWA (2)1. Fuskantar wahalhalu iri iri a cikin rayuwa, da cijewar abubuwan da suke gabansa, daya daga cikin magabata yana cewa ” Na kan sabawa Allah, sai inga danshin sabona halayyar abin hawana da matata” kuma Ibnu seerin yana cewa lokacin da wani bakin ciki ya dame shi “Wannan bakin cikin ya sameni ne, saboda wani zunubi dana aikata shekaru arba’in da su ka wuce”Allah madaukaki yana cewa : “Babu wata musiba da za ta same ku, face sai ta kasance daga abin da hannunku ya aikata ne” (Suratul Zukruf ayata 30).Zunubai suna jawo bala’oi dayawa, wadanda suke cutar dazuciya da jiki, a Duniya da Lahira, ba wanda ya san adadinsu sai Allah. Saboda ba za’a dora maka wani ya dinga cutar da kai ba, sai idan akwai wani zunubi da kaaikata, ka san zunubin ko ba ka san shi ba, wani daga cikin magabata ya hadu da wani mutum sai ya aibanta shi, sai ya ce masa : jira ni nashiga gida na fito, sai ya shiga gida yayi sallah ya tubazuwa ga Allah, bayan ya fito sai mutumin ya ce masa: me ka yi, sai yace : na tuba zuwa ga Allahn da ya dora ka akaina.2. Samun duhu a cikin zuciya,Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa ” Idan mumini ya yi zunubi, ana yin bakin digo a zuciyarsa, in ya tuba ya nemi gafara sai a cire idan yacigaba sai wannan bakin ya karu” Ibnu majah ne ya rawaito kuma Albani ya kyautata shi.

Reply

« Back to forum