hukuncin hoto

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

hukuncin hoto

from nuramuhd3 on 04/12/2015 12:38 PM

hukuncin hoto a muslinci Annabi s.aw. yana cewa : “Wadanda suka fi kowa tsananin azaba ranar alkiyama su ne masu suranta mutane kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 5950, a wani hadisin kuma yana cewa : “Duk mai suranta mutane yana cikin wuta” kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2110. Saidai malaman wannan zamani sun yi sabaniakan wacce irin sura ake nufia cikin wannan hadisin, shin Photograph zai shiga ciki, ko kuwa ? 1. Akwai wadanda suka tafi akan cewa kowacce irin sura da ake yi ta shiga ciki, don haka bai halatta a dau kowanne irin hoto ba, in ba na lalura ba kamar Pasport ko hoton da ake bukata saboda tabbatar da wani abu . 2. Ya halatta a dauki photo graph, saboda ya zo a wasu hadisan da sukeharamta daukar sura cewa : “Su ne wadanda suke kwaikwayon halittar Allah” kamar yadda ya zo a Bukhari a lamba ta : 5610, Shi kuma photo grapp babu kwaikwayon halittar Allah a cikin shi, saboda inuwa ce kawai ake dauka, don haka sai ya halatta, tunda ba sura ce ta hakika ba, sai ya zama daidai yake da mudubi, kumababu sabani wajan halaccin amfani da mudubi, saboda ganin sura . Zance mafi inganci shi ne rashin yawaitadaukar hoto, saboda hotuna na daga cikin hanyoyin da suka jawo aka bautawa wasu,sannan kuma dalilan wadanda suka haramta Photograpp suna da karfi, fita kuma daga sabanin malamai yana da kyau . Don neman karin bayani duba Alminhajj na Nawawy 1481 da kuma Fataawallajna Adda’ima mai lamba ta : 5807, da fataawa Ibnu-uthaimin lamba ta : 151. Allah ne mafi sani .

Reply

« Back to forum