hukuncin jan carbi

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

hukuncin jan carbi

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:06 AM

jan carbi ba bidi’a ba ne, saboda duk da cewa babu shi a zamanin Annabi s.a.w. hakan ba zai saya zama bidi’a ba, saboda wanda yake amfani da shi baya nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, yana amfani dashi ne, don ya kiyaye adadin zikirinsa. Yin amfani da ‘yan yatsu shi ne yafi, saboda hadisi ya yi nuni cewa : za’a ba su dama su yi magana, ranar alkiyama, kamar yaddaTirmizi ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a hadisimai lamba ta: 3486, don hakaza su yi maka shaidar abin da ka yi na alkairi, sabanin carbi. Sannan sau da yawa zaka ga mutum yana jan carbi amma hankalisa yana wani wajen, sabanin idan da hannu yake yi. Jan carbi yakan iya sanya wasu su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne. Annabi s.aw. yana yin tasbihi da hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya inganta, saidai wasu malaman suna cewa in ya yi da hagu ma yayi, tare da cewa yi da dama shi ne ya fi. Saidai duk da dalilan da sukagabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, balle ace ya zama bidi’a, ga shi kuma ba’a samu wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi da hannu shi ne yafi .Don neman Karin bayani duba : Majmu’ul fataawa 22187. da Lika’ul maftuh na Ibnu-uthaimin 330. Allah ne mafi sani

Reply

« Back to forum