ina ALLAH yake2

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

ina ALLAH yake2

from nuramuhd3 on 04/26/2015 09:54 PM

An kavo daga Nafi’u daga Abdullahi xan Umar (R.A) ya ce: Lokacin da Manzon Allah (S.A.W) ya rasu, sai Sayyadina Abubakar ya ce: “Ya ku mutane idan kun kasance Muhammadu shi ne Ubangijin da kuke bautawa, to, Muhammadu ya mutu. Idan kun kasance Allah (S.W.T) kuke bautawa, to Allah wand ayake sama ba zai mutu ba”. Sai Abubakar (R.A) ya karanta aya ta 144 cikin Ali-Imrana wadda take tabbatar da cewar Annabi (S.A.W) zai mutu. Abu Sa’id Addarimi ya fitar da hadisin a cikin littafinsa na Raddu alal-Jahmiyya shafi na (44 – 45).Wani hadisi da malamai sukafi kafa hujja da shi, shi ne hadisin wani Sahabi mai suna Mu’awiyya bin Hakam Assulamiy, wanda yake buqatar ’yanta baiwarsa. Sai Annabi ya ce ya zo da baiwar, lokacin da ya kawo tagaban Annabi (S.A.W) sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da baiwar: “A ina Allah yake?” Sai ta ce: “Yana sama”.Sai Annabi (S.A.W) ya ce mata: “Ni wane ne?” Sai ta ce: “Kai Manzon Allah ne”. Sai Annabi ya ce da Mu’awiyya ka ’yanta ta dominita mumina ce”. Allah Akbar! Wato wannan hadisi yana nuna mana cewar yarda da tabbatar da cewa Allah yana sama, yana daga tabbatar imanin mumini. Saboda haka, Imam Sa’id –Darami cikin Raddu al-Jahmiyya yake cewa: “Idan mutum bai yardacewar Allah yana sama ba, toshi ba mumini ba ne, ko da waye kuwa. Domin ’yantawa bai tabbatar ba ga wannan baiwa har sai da aka tabbatar da imaninta na cewar Allah yana sama”. Wannan hadisi na Jariya kamar yadda malamai suke kiran sa. Imam Bukhari ya fitar da shi cikin littafin Juz’ul Qira’a Khalfal Imam. Imam Muslim, Nisa’i da Ibn Khuzaima duk sun rawaito shi da jingine mai inganci.An karvo hadisi daga Usamatu ibn Zaid ya ce: “Na ce da Manzon Allah (S.A.W) ya Manzon Allah na ga kama azumin wani wata fiye da sauran watanni sai dai watanRamadan”. Sai Annabi ya ce: “Wane wata ne?” Sai na ce: “Watan Sha’aban”. Sai Annabiya ce: “Shi ne watan da ake xaukaka ayyukan bayi zuwa ga Ubangijina Talikai a cikinsa. Saboda haka ya sa nake son a xaukaka aikina, ina mai Azumi”. Imam Ahmad da Nasa’i suka rawaito da jingine mai kyau.Saboda haka wannan hadisi hujja ne domin ana xaukaka ayyukan bayi zuwa sama ake nufi wajen Allah. Haka nan hadisin Mi’iraji wanda na kawo a babin da ya wuce shi ma hujja ne.DALILAI DAGA MAGABATA NA GARIAqidar Ahlus Sunna wal Jama’a shi ne kafa hujja daga littafin Allah da sunnar Manzon Allah (S.A.W) a bisa fahimtar magabata na gari. Domin Annabi ya ce: “Fiyayyen mutane su ne waxanda na rayu da su, sai waxanda suka bi su, sai waxanda suka biyo waxanda suka bi su”. Ma’ana su ne sahabbai, tabi’ai da kuma tabi’ut tabi’ina. To waxannan su ne ajin farko na magabatana gari. Kuma ga hujja daga Alqur’ani da take nuna mana wajabcin koyi da abin da suka yi ijma’i a kansa. Allah yana cewa: “Kuma wanda ya sava wa Manzo daga bayan shiriya ta bayyana a gare shi,kuma ya bi wanin muminai, za mu jivintar masa abin da ya jivinta. Kuma mu qone shida jahannama, kuma ta munana ta zamo makoma”. (Nisa’i: 115).Xaya daga cikin malamai magabata Imamul Auza’i ya ce: “Mu da Tabi’ai mun kasance muna cewa Allah (S.W.T) yana sama, kuma mun amince da siffofi”.Imamul Shafi’i cewa ya yi: “Allah (S.W.T) yana bisa Al’arshinSa a cikin sama yan akusantar bayinSa yadda ya so, kuma yana saukowa zuwasaman duniya yadda ya so”.Imamu Abu Hanifa kuwa cewa ya yi: “Duk wanda ya ceban sani ba, shin Allah yana qasa ko yana sama? To, ya kafirta. Domin Allah ya ce: “Mai Rahama ya daidaita a kan Al’arshinSa”. (Ash-shura: 10) domin Al’arshi tana saman sammai duka…”.Wannan shi ne ra’ayin malamai magabata na gari. Kuma a farko mai karatu ya karanta bayanin Imamu Malik na tabbatar da cewar Allah yana bisa Al’arshinSa.Mai karatu waxannan abubuwa da muka bayyana duka, shi ne aqidar Manzon Allah (S.A.W) ya kawo a cikin shari’arsa zahiri ba baxini ba.Kuma ita ce aqidar da sahabbai suka tafi a kanta, kuma muna fatan Allah (S.W.T) ya karvi rayukanmu akanta.Haqiqa mun yi Imani da Allah (S.W.T) yana tare da halittarSa da jinSa da iliminSa da ganinSa, yana bisa Al’arshinSa, kuma yana ganin ayyukansu. Kuma yanatsara al’amarinsu yana azurta talaka, yana xora karyayye, yana ba da mulki ga wanda ya so. Yana qwacewa daga wanda ya so. Kuma yana xaukaka wanda ya so. A hannunsa alheri yake kuma shi a bisa dukkan komai mai iko ne.Wanda ya kasance haka sha’aninsa yake. To, lallai yana tare da halitarsa a haqiqa, yana ganin su yana jin su, kuma yana bisa da su a Al’arshinSa. “Babu wani abu da ya yi kama da shi, kuma shi mai iko ne mai gani”. (Ash-shura: 11).Kuma ba za mu faxi irin abin da qungiyar Haruriyya daga cikin ’yan Jahamiyya da ire-irensu suke cewa ba. Wai Allah yana tare da halittarSa a kan doron qasa. Kuma wai yana ko’ina. Duk wanda kuwaya siffanta Allah da waxannan abubuwa, to, ya siffanta Allah da siffofin da ba su dace da Allah ba na tawaya. Wanda wasu malamai suna ganin wannan zai iya kai mutum ga kafirci!DALILAN MASU CEWAR ALLAH YANA KO’INAAkwai wata aya da masu da’awar Allah yana ko’ina suke kafa hujja da ita cewar Allah (S.W.T) yana ko’ina. Inda Allah yake cewa: “Kuma shi ne Allah a cikin sammai kuma a cikin qasa yana saninasirinku da bayyananku, kuma yana sanin abin da kuke yi na tsirfa”. (An’am: 3).To, amma manyan malamai magabata sun fassara wannan ayar da cewar: Inda Allah ya ce: “Kuma shi ne Allah a cikin sammai”. Wato ma’ana shi ne wanda yake sama bisa Al’arshinSa sai kuma ci gaban ayar ya ce: “Kuma a cikin qasa yana sanin asirinku da bayyanenku”. Wato ma’ana a qasa yana sanin asirinku da abin da kuke bayyanawa duk da kasancewarSa yana sama.Saboda haka wannan aya ba hujja ba ce a wajensu, illa maraddi take yi musu.Haka nan suna kafa hujja da aya ta 84 a cikin Suratul Zukhruf inda Allah ya ce: “Kuma shi ne wanda ake bautawa a sama, kuma abin bautawa a qasa, kuma shi nemai Hikima Masani”. Wannan aya ba tana nufin Allah yana sama kuma yana qasa ba, a’a, tana nuna manahalittun sama da na qasa dukAllah suke bautawa.Suna kuma kafa hujja da indaAllah yake cewa: “Shi ne wanda yake tare da ku duk inda kuke, kuma Allah mai gani ne ga abin da kuke aikatawa”. (Hadid: 4) da kuma faxin Allah inda yake cewa: “Ashe ba ka ga cewa lallai Allah yana sane da abinda ke cikin qasa ba? Wata ganawa ta mutum uku ba za ta kasance ba face Allah shi ne na huxu xinta, kuma babuta mutum biyar facer shi ne na shida xinta, kuma babu abin da ya kasa. Wannan kuma babu abin da yake mafiyawa face shi yana tare da suduk inda suka kasance, sannan ya ba su labari game da abin da suka aikata a ranar qiyama. Lallai Allah Masani ne ga dukkan komai”.(Mujadala: 7) Suna kafa hujjaa waxannan ayoyi cewa ai Allah ya ce: “Yana tare da su duk inda suka kasance”. Sai su ce ai yana tare halittarSa. To, amma Imam ibn Kathir ya fassara wannan aya da cewar: “Ma’ana yan atare da halittarsa yana sanin ayyukansu duk inda suka kasance a tudu ko a kwari da dare ko rana a gidajensu da sauransu”. Saboda haka wannan duk yana sanin su da ilminSa da ganinSa da jinSa. Yana jin zancensu, yana kallon su, yana sanin sirrinsu da bayyanensu. Ba ka ji ma abin da ya ce da Annabi Musa da Haruna ba? Lokacin da ya aika su wajen Fir’auna? Sai ya ce musu: “Ya ce kada ku ji tsoro, lallai ni ina tare da ku, ina ji kuma ina ganin ku”. (X.H: 46). Wannan aya ta fassara manawaxancan ayoyi da muka ambata a baya. (Ma’ana aya takan fassara wata ayar a Alqur’ani).Har yanzu dai sukan kafa hujja da ayar da ke cewa: “Mai Rahama ya daidaita a kan Al’arshinSa”. (X.H: 5). Suna fassara ta da Tawili su ce wai ba Istawa (ya daidaita)ake nufi ba amma Istaula (ya mamaye) ake nufi. To, a nan muna da ma’auni wato Annabi da Sahabbai da Magabata, sun fi mu sanin Tafsirin Alqur’ani (saboda haka sun fi mu fahimtarsa), amma ba su fahimci ayar a haka ba. Waxannan mutane shin suna nufin sun fi Annabi(S.A.W) da sahabbansa saninAlqur’ani ke nan?A wannan matsala Babban Magabacin malamin nan Ibn Qayyim Al-Jauziy ya ce: Allah ya umarci Yahudawa da cewar ku ce hixxa sai suka cehinxa suka canja harafi xaya.Saboda haka Allah ya yi musu uquba ba. To, haka nan sai Allah ya ce Istawa saimasu Tawili suka ce Istaula. Mai karatu ka duba yadda waxannan mutane suka yi aiki daidai da na Yahudawa. Domin duk aikin nasu babu bambanci. Ka duba Suratul Baqara ka ga yadda Allah yake mayarwa da Yahudawa raddi.Lallai Ma’aiki (S.A.W) MA’ANARSA1. Al-Ibana An Usuluddiyana:Imam Abdul-Hasan Al’Ash’ariy.2. Raddi Alal Jahmiyya: ImamAbu Sa’ida Ad-Darini.3. Tarjamar Alqur’ani Mai girma: Sheikh Abubakar M. Gumi.4. Tafsiril Qur’anil Azeem: Imam ibn Kathir.5. Aqidatu Ahlus – Sunnah wal Jama’a: Sheikh Muhammad Saleh Al-Uthimeen.6. Sharhi Usulul Imam: Sheikh Muhammad Saleh Al-Uthaimeen.

Reply

« Back to forum