shi a da kafieta musulmi
[ Go to bottom | Go to latest post | Subscribe to this topic | Latest posts first ]
shi a da kafieta musulmi
from nuramuhd3 on 04/02/2015 09:18 AMSHI’A DA KAFIRTA MUSULMI!!!Bismillahi, wa sallallahu a’la nabiyyina Muhammad, wa a’la Alihi wa Ashabihi.Duk mai bibiyar tattaunawar da ake yi tsakanin ‘yan shi’a yan sha biyu da yan uwa Ahlus-Sunnah a kafofin sada zumunci ( kamar ; facebook )zai ga yadda yan shi’a suke yawan tuhumar Ahlussunnahda cewa suna kafirta musulmi, wani lokacinma ba a kan wannan abu ake tattaunawar ba, amma sai sun san yadda suka lankwaso zance, suka karkatar da hankulan mutanezuwa ga waccan tuhuma ta karya, maras asali a cikin littattafan Sunnah.Amma abin da zai baka mamaki shi ne a duk cikin kungiyoyin addini babu kungiyar da ta kai shi’a kafirta musulmi, tare da zagi da cin mutuncin bayin Allah, wannan abu ne da yake kunshe a cikin manya-manyan littattafansu, ba wai tuhuma ba ce ta karya marasasali irin wadda suke wa Ahlus-Sunnah, don haka ma bari mu kawo kadan daga cikin irin dimbin riwayoyinsuda suke tabbatar da haka, watakila wasu daga cikinsu wadanda aka rude su da karya da takiyya su sake nazari, su fahimci gaskiya.1- Babban malaminsu al-Kulainiy ya kawo riwaya a cikin littafinsa mai suna (al-Kafi 8/246) daga limaminsu muhammad Al-bakir yana cewa, “Mutane sun yi ridda bayan Annabi s.a.w sai mutum uku, al-Mikdad ‘dan Aswad, da Salman al-Farisiy, da Abu Zarril Gifari”.2 – hakanan dai ya zo a cikin (al-Kafi 1/233) Imaminsu ar-Ridha yana cewa “Babu wanda yake kan addinin Musulunci wanda ba mu ba kuma ba ‘dan shi’armu ba”.3 – A wata riwayar a cikin (ar-Raudatu Minal Kafi 8/2109) daga limaminsu Abu Ja’afar yana cewa, “Ya kai Abu Hamza wallahi dukkan mutane gabadayansu yan zina ne banda yan shi’armu”.4- Babban Malaminsu Ni’imatullahi al-Jaza’iriy yana bayanin hukuncin Nawasib – wato a nufinsu Ahlussunnah – ya ce ” Kafirai ne su, najasace da IJMA’IN DUKKAN MALAMAN SHI’A IMAMIYYAH, sun fi yahudu da nasara sharri. Alamar Nasibi kuwa ita ce gabatar dawanin Aliyyu a wajen khalifanci”. Duba : (al-Anwarun Nu’umaniyya 2/206 – 207).Wannan kadan kenan daga cikin irin riwayoyi da dimbin maganganun malaman shi’a a kan kafirta duk wanda ba dan shi’a ba. kuma wannan ita ce akidar duk wani ‘dan shi’a na gaskiya, shi ne yana ganin kafircin wanda duk ba shi’a ba ne, kai yana ganinsa ‘dan zina ne, kamar yadda muke gani suna rubutawa a kafafe kamar facebook yayin tattaunawa da su.A bangare guda kuma baza ka samu irin wannan kafirtawar ba a litattafan Sunnah, kai hatta shehun Musulunci Ibnu Taimiyyah da Shehun musulunci Muhammad Bin Abdulwahhab, wadanda kullum ake tuhuma, hadi da yi musu karyar cewa su suka kawo kafirta musulmi, ba za ka taba samun irin wannan acikin litattafansu ba, sai dai alankwasa musu magana ko a yi mata mummunar fahimta.Allah Ka tsare mu daga bata, Ka dora mu akan madaidaiciyar hanya.

Reply