tare da audu 2

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

tare da audu 2

from nuramuhd3 on 03/26/2015 09:31 PM

**TAREDA ABDUL-JABBAAR gameda Mas'alar: JARABTAR MAFI KARAMCIN HALITTU DA ZUNUBI** MUNAAQASHAR WANNAN BABI A MUQADDIMA!A Mujalladi na 2, shafi na 19, bayan kawo wannan Mas'alar a shafi na 17, Abdul-Jabbar yace: "Sabaninmu da Ibn Taymiyahr.a baida alaqa da falalar TUBA daga zunubi, don wannan lamarine da mukai ittifaqi akansa, sai dai ABINDA MUKE KAAMASHI da shi kuma muka WATSI DASHI sannan bazamu karbai ba bakuma zamu taba karbarsa ba shine fadinsa:"Haqiqa Allah ya Jarabci Mafi girman Halittu da Zunubi"! Ina alaqa anan tsakanin Falalar tuba da wannan mummunan magana kasashshe?".NACE: Alhamdulillah, ai muma filin daagar tsakaninmu dakai itace cewa:"ANNABI s.a.w" ne ake nufi awannan ASARdin!!!Sam ba Annabi s.a.w ake nufi ba, dukda Shine Mafi Karamci, Girma da Darajar Halittu a wajen Allah s.a.w, akwai Falala, sunaye da kebantattun Lamura dasuke tsakanin Allah Madaukaki da kuma Sauran Annabawa a.s!Don haka zanso muyi yawa a littafai mugani, shin idan Akace "AKRAMUL-KHALQIINDALLAAHI" wa ake nufi?????1: Hadisi Yazo cikin Musannif na IBN-ABIY-SHAYBAH cewa: Allah yayiwa Annabi Ibrahim Wahayi cewa: (Kaine mafiKaramcin Halittu a gareni...........), Hadisi mai Lamba 24875.2: Wani mutum ya Tambayi Annabi s.a.w: Wanene mafi karamcin Halitta a wajen Allah? Sai Annabi s.a.w yace: Ban sani ba, sai Jibril yazo masa, sai yace: (Yaa Jibril, wane Halittace mafi karamci wajen Allah?) Sai yace: Ban sani ba, sai Jibril ya tafi, sannan ya dawo, sai yace: (Mafi Karamcin Halittu wurin Allah sune: Jibril, Mika'il, Israafiyl da Malaa'ikan Mutuwa............). Al-Azamah na Abish-Shaikh Al-Asbihaani:hadisi na: 380. Kanzul Ummaal: Hadisi na 45553.3: Yazo cikin Dogon Hadisin Anas r.a daga Manzon Allah s.a.w na abinda Allah yayiwa Annabi Musa a.s wahayi, ciki yake cewa: ((..........YaaMusa, lallai duk wanda yayi Imaani, to shine Mafi KARAMCIN HALITTU A WAJENA........)). Hilyatul-Auwliya:2/343, sannan ya sake maimaita shi da qarin: ((Yaa Musa ka isarwa banu Israa'il cewa: duk wanda yayi Imani da Ahmad toshine MAFI KARAMCIN HALITTU a wajena.......)). HILYAH:6:32.4: Sarkin Rum ya rubuto Wasiqa ga Mu'awiyah bn Abiy-Sufyan r.a yana tambayarsa gameda: Mafi Falalar Magana, da Mafi Karamcin Halittu wajen Allah.........,sai aka cewa Sayyadina Mu'awiyah r.a ka tura wajen Abdullahi bn Abbas ka tambayeshi, cikin Amsar da Ibn Abbar r.a ya bayar akan Waye Mafi Karamcin Halittu wajen Allah itace:"Annabi ADAM shine mafi karamcin Halittuwajen Allah". Attamhiyd Limaa fil-Muwatta minal Ma'aaniy wal asaaniyd:6:49-50.Qari da Fadin Allah madaukaki: ((Lallai mafi karamcinku wajen Allah shine Mafi tsoron Allah cikinku))Da Hadisin da yazo cikin Riyaadus-saalihiyn, Babin Taqwa Hadisi na 69, Muslim:168, Bukhari:3353,3374,3490,4689,wanda ke qara qarfafa wannan Ayah, dakuma cewa: ANNABI YUSUF a.s shine mafi Karamcin mutane wajen Allah!.Idan Muka Hada wadannan Nusu din, A dunqule zamuga cewar: AKRAMUL KHALQI bawai kadai yana nufin Annabi s.a.w bane, *Laa wa Alfu laa*!Gamida cewar Shine Shugaban Halittu kuma shine Shugaban Talikai, Mafi Tsada,Girma daraja, Matsayi da Karamci wajen Allah wanda wannan baya buqatan dalili!Wannan baya kore kasantuwar wasunsa a wannan Matsayi, Kamar yanda shi da kansa yace: "Yusuf ne Mafi Karamcin Mutane wajen Allah"!!! Wannan bai koreshi a wannan matsayi ba s.a.w, hakanan Annabi Ibrahim Shine Khalilullahi, kamar yanda Qur'ani ya tabbatar, amma kuma Annabi Muhammad s.a.w shima Khalilullahi ne kuma Yafi Annabi Ibrahim a.s! d.s!Don Haka: A Jumlace Annabawa kakaf dinsu sune Akramul-Khalqi Alallaahi, dukkansu suna Qasan Annabi s.a.w! Wannan bai kore Falalarsa akansu, kuma bai kore falalarsu suma din a qasansa!Sannan Mataki na 2 shine: A dukkan Sauran Halittu: Masu Tsoron Allah sune mafi Karamci wurin Allah s.w.a, qarqashinAbubakar r.a, sai Umar r.a sai Usman r.a sai Aliyu r.a! Wannan bai kore kasantuwarsauran Taqiyyai na bayin Allah cikin Jerin nan ba, hakanan baya kore daukaka da Darajar wadannan Manyan Waliyai 4 r.a ba!A bisa wannan Fahimta, Dauriya bisa ta jiya nake cewa: Abin Nufi da AKRAMUL KHALQI anan shine dayan 2:1: Annabi Adam a.s, bisa zuwan Nassi kancewa shine AKRAMUL KHALQI kamar yanda na kawo, Wanda Qur'ani ya bada labarin laifinsa da Tubarsa gaba daya!2: Annabi Dawud a.s, bisa hujjar siyaaqin Maganar a Minhaaj, wanda shima Laifinsa sananne ne a Qur'ani da kuma Tubarsa.Idan kuma wani na da'awar cewa Lallai Annabi s.a.w Ibn Taymiyah r.l ko shi Yahyaa din suke nufi, to Ya kawo mana dalili abisa hakan, sabanin abinda muka kawo, amma kusani, duk wata Kalmah mai Dilaalah mai yawai, dole duk wata ma'ana da za'a bata a tsaida qariynar da zata sanya abata wannan ma'anah, mu ga Dalilanmu nan kan cewa Ba Annabi s.a.w ake nufi ba! wannan itace Gaskiya Kuma Zahirin Magana

Reply

« Back to forum