tarihi 3
[ Go to bottom | Go to latest post | Subscribe to this topic | Latest posts first ]
tarihi 3
from nuramuhd3 on 03/06/2015 10:09 PMBISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMMU KARANTA TARIHITARIHIN RIKICIN TATTAR(MAJLISI NA 3)Shigowar Tattar a BiranenMusulunci:Wuri na farko da Tattar suka farakai hari shi ne Bukhara,inda sukayi angaya a bayan wannan babbanbirni. Suka kwana uku sunagwabzawa da mayakan musulmi.Daga karshe dai da yawan sojojinmusulmi suka gudu saboda bala’inda suka gani wanda basu iyawa dashi, suka tasar ma Khurasana.Mutanen gari basu samu watamafita ba sai dai su yi saranda sunemi a basu lamuni a kanrayukansu. Alkali Badruddini ne yajagoranci masu neman wannansulhun. A ranar 4 ga watan ZhulHajji 616H aka buda ma Tattarkofofin gari, suka shiga da makircisuna masu nuna tausayawa dakyautatawa ga mutane. Jinkizkhanya nemi mutanen Bukhara sukama masu don su yakisojoji4000 da suka shiga Qal’ahwadanda basu samu tserewa ba,ya ce kuma duk wanda bai je ba zaa kashe shi. Ya kuma bada umurnia cike babban ramin dasojojinsuka yi garkuwa da shi har ya saaka rinka dauko Alkur’anai dagamasallaci ana zubawa cikin ramindon a cike shi. Aka kuma daukomimbarin masallaci aka kakkaryakatakonsa don a zuba cikin ramin acike shi. Da haka suka isa wannanwuri suka gama da duk sauransojojin da suka rage ma musulmi.Bayan haka ne sarkin Tattar ya cea rubuta masa sunayenmuhimmanmutanen gari, ya sa aka rinka kiransu guda guda, aka kwace duk wanimakami ko wata dukiyada kehannunsu, sannan aka yi masuyankan rago baki daya. Sannanaka kewaye sauran musulmi akarinka kisan su, aka farauci matansuda ‘ya’yansu aka rinka aikataalfasha da su gaban mazajensu.Wadanda suka samu iya tserewasuka gudu, wasu kuma suka aukacikin makiya da makamai sukasamu shahada, cikin suhar dababban malamin fikihun nanRuknuddin Zadah da alkaliSadruddin Khan. Wasu kuma akakama su ga hannu. Kai,a takaicedai Tattar ba su bar birnin Bukharaba sai da suka kunna masa wuta,suka kone masallatai damakarantu da gidaje babu iyaka,suka azabta fursunoninda sukakama matsananciyar azaba. Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.Daga nan suka tasar maSamarkanda, suka gargadofursunonin musulmi kamar awaki agabansu, wanda duk yakasa tafiyasai su kashe shi su wuce. Sukamika ma ko wane musulmi tuta yadaga don a tsorata jama’armusulmin Samarkanda. Da isowarsu basu bata lokaci ba sukagwabza da rundunar musulmi sukakashe soja 50,000 sannan suka farma farar hula. Daga baya sai sukarinka ja da baya suka zame jikimusulmi na bin su, ashe watamakida ce suka shirya sai da akafita garin gaba daya sai suka yankewata gada da suka haka suka yiwa musulmi kimanin 70,000 zobesuka kuma yi musu kisan kiyashi.Su ma dai sauran mutanen da akabaro a cikin birni sai dawancanbala’in da ya cimma mutanenBukhara ya cimma su. Suka nemisulhu, Tattar suka ba su, kumasuka yaudare su. Aka nemi subude kofofin gari, sannan su fito dadukiyoyin da duk suka mallaka,sannan su yo waje da dabbobinsuda matansu da ‘ya’yansu. Aka cemasu zamu kai ku waniwuri indazaku rayu.. daga karsheakagargada su zuwa titin alkiyamabaki daya. Sannan aka konababban masallacin gari, aka cimutuncin budare musulmi da ranatsaka, aka aikata fasadi wanda bashi faduwa. Duka wannan ya faru acikin watan Muharram na shekarar617H.Zamu ci gaba in Allah ya so.

Reply