hujjojin yashi a

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nura

34, male

Posts: 124

hujjojin yashi a

from nura on 09/19/2014 08:31 PM

4- HUJJOJIN ÝAN SHI'A. Fadin Allah Madaukakin Sarki. ﺎﻤﻧﺇ ﻢﻜﻴﻟﻭ ﻪﻟﻮﺳﺭﻭ ﻦﻳﺬﻟﺍﻭ ﺍﻮﻨﻣﺍﺀ . MARTANI: FUSKA TA BIYAR: Da wannan aya na magana ne a kan cewa Aliyu ya bayar da zakka a daidai lokacin da yake ruku'i, kamar yadda suke ikirara, da hakan ta zama wani sharadi na wajabci a cikin cancantar shugabanci. Ta yadda musulmi ba za su jibanci kowa ba sai Ali shi kadai. Ba zancen Hassan ko Husaini ko sauran Banu Hashim ake yi ba. Wannan kuwa ya sabawa abinda ku kanku ýan Shi'a kuke cewa. FUSKA TA SHIDA: Ayar dai ta zo ne da lafazin jam'i ba na mutum daya ba. Don haka, ba ta danfaruwa a kan Ali shi kadai. FUSKA TA BAKWAI: Ta kuma tabbata cewa, Allah Ta'ala ba ya farin ciki, balle ya gode wa mutum a kan aikata komai, sai idan abin nan yardadde ne a wurinsa; ta hanyar kasancewarsa wajibi ko mustahabbi. Ita kuwa sadaka da kyauta da ýanta bayi da ba da haya da aure da saki, da ire-iren su, Malaman Musulunci sun yi ittafaki a kan cewa aikata su a cikin sallah ba da'a ba ne, balle su zama wajibi ko mustahabbi. Hasali ma da yawa daga cikin malaman na ganin aikata dayansu cikin sallah na bata ta, ko da ba a yi magana ba. Kai tana ma iya baci dalilin wata ishara da aka fahimci makasudinta, a wurin wasu daga cikin malamai. A yayin da wasu malaman suka kara da cewa, babu wani abu da ake iya mallaka ta wannan hanya, sakamakon rashin wani sanadari na shari'a a cikin harkar. Kuma da irin wannan aiki abin so ne to, da Annabi ya kasance farkon wanda ya aikata shi, ya kuma kwadaitar da Sahabbansa a kan haka. Da kuma an sami cewa Aliyun ya ta aikata hakan a wasu lokuta. Rasa daya daga cikin wadannan abubuwa, na tabbatar da kasancewar sadaka a cikin sallah ba wani aiki na madalla ne ba. Musamman ma da yake aikin tallafa wa makubakacin ba ya wucewa. Ta yadda mai sadakar zai iya hakura har ya kare sallah, sannan ya yi kyautar. Domin idan har sallah ta karba sunanta, to, ba za ta bayar da damar yin haka ba. FUSKA TA TAKWAS: MU kaddara cewa yin sadaka a cikin sallah shari'a ne. Da ba a kebance lokacin ruku'i don aikata ta ba; aikata a lokacin da ake zaune ko tsaye ya fi dacewa. Amma sai a ce babu wanda zai zama shugaba gare ku sai daya daga cikin wadanda ke bayar da sadaka a lokacin da suke ruku'u?? To, za a sami wani yayi sadakar a lokacin da yake tsaye ko zaune, bai cancanci wannan shugabancin ba ko??. FUSKA TA TARA: Cewar da ýan Shi'ah suka yi: fadar Allah Ta'ala a cikin ayar: "Kuma suna bayar da zakkah alhali su masu ruku'i ne (5:55)". Wai hakan na nufin wanda zai bayar da zakkar ya kasance yana cikin ruku'i. Magana ce ba ta sauraro ba. Domin Aliyu (R.A) ba ya cikin wadanda zakka ta wajaba kansu a wannan zamanin na Annabi (S.A.W) saboda kasancewarsa talaka. Kuma ita zakkar azurfa na wajaba ne a kan wanda ya mallaki nisabi tsawon shekara. Aliyu kuwa ba ya cikin wadanda suka mallake shi. FUSKA TA GOMA: Wani abin kuma shi ne, da yawa daga cikin malaman fikihu sun tafi a kan cewa fitar da zobe da bayar da shi a matsayin zakka ba ya isa, sai a lokacin da aka aminta da wajabcin zakka a cikin kayan ado. Aka kuma yarda da fitar da wani daga cikinsu a matsayinta. Sane muke da cdwa, akwai malaman da suka yarda da a fitar da kimar abinda ya wajaba din. To, amma ai yin wannan awo da gwaji don fitar da kimar, abu ne mawuyaci a cikin sallah. Kuma hasali ma ita kimantawar kanta ta sassaba gwargwadon sassabawar yanayi. FUSKA TA SHA DAYA: .................... Yana tafe, Insha Allah.

Reply

« Back to forum