karkasuwan shi a
[ Go to bottom | Go to latest post | Subscribe to this topic | Latest posts first ]
karkasuwan shi a
from nura on 09/10/2014 08:27 AM**** KARKASUWAN SHI'A ****Duk a cikin kungiyoyin da akayi a musulunci shi'ace, kungiyar da tafi kowace kungiya karkasuwa domin ko a acikin littafin Algunya na Sidi Abdulkadir jilani yakawo kungiyoyin shi'a kusan talati (30) a zamanin sa, ga kadan daga cikinsu:1)SHI'A IMAMIYYAH: wannan shi'ar ita ce tafi karfi don haka ita zamu yi magana a kanta, saboda haka basai mun tsawaita magana akanta ba a nan.2)SHI'A ZAIDIYYA: wannan shi'ar itace ake ganin tana da sassauci domin basu la'antar sahabbai kuma fiqihun su yana kama da na Ahlus-sunnah, sai dai su suna fifita imamu Aliyu r.a akan halifofin manzon Allah s.a.w, ayanzu ana samunsu a kasar yeman.3)SHI'A ISMA'ILIYYA: ita kuma wannan shi'ar ta balle ne daga isna ashariyya(imamiyya) ana samun sune a Afirka da Asiya.

Reply