kawarda shubuha

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nura

36, male

Posts: 124

kawarda shubuha

from nura on 08/06/2014 02:05 PM

KAWAR DA SHUBHACi gaba daga bugun baya7- Raddi ga maqaryata a dunqule da kuma rarrabeNi zan ambata maka abubuwan da Allah ya ambata cikin littafinsa, jawabi ga maganganun da mushrikai suka yi hujja da shi akan mu a wannan zamanin namu, sai muce jawabin maqaryata ta hanya biyu ne: a dunqule da kuma a rarrabe.Amma wanda yake a dunqule, to al’amari ne mai girma, kuma fa’ida ce mai girma ga wanda ya hankalceta, wannan kuwa ita ce maganar Allah:“Shi ne wanda ya saukar maka da littafi, a cikinsa akwai Ayoyi mabayyanan ma’anoni, sune asalinlittafin, da kuma wasu masu kama da juna. Amma waxanda suke da karkata a cikin zuqatansu, sai suna bin masu kama da juna daga cikinsa, domin neman fitina da neman fassararsa. Kuma babu maisanin fassararsa sai Allah”. Kuma haqiqa Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa ya ce: “Idan kuma ga waxanda suke bin wanda ya yi kama da juna daga cikin (Alqur’ani), to waxannan su ne waxanda Allah ya ambata ku guje su”. Misali, idan wani mushriki ya ce maka: “Ku saurara! Lalle waliyyan Allah babu tsoro gare su kuma basa yin baqin ciki”. Kuma ceto gaskiya ne, kuma waliyyan su na da alfarma a wajen Allah; ko kuma ya ambaci wani hukunci dagamaganar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana kafa hujja dashi akan wani abu na qaryarsa, kai kuma baka san ma’anar zancen da ya ambata ba, to ka amsa masa da cewa: Allah ya ambata a cikin littafinsa cewa waxanda suke akwaikarkara a cikin zuciyarsu suna barin Ayoyin bayyananmu, bin masu kama da juna (waxanda ma’anoninsu suke rikitarwa); abin da na ambata maka kuwa na cewa Allah ya ambaci mushrikai cewa suna iqirari da rububiyyar Allah, kum kafircinsu sabosa ratayarsu da mala’iku da Annabwa da waliyyai ne tare da faxinsu “Waxannan su ne masu cetonmu a wajen Allah….” Suratu Yunus, Aya ta 18. wannan al’amari ne bayyanan ne, babu wanda yake da ikon musanya ma’anarsa.Abin da ka ambata mini kuwa ya kai mushriki daga Alqurani da maganar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ban san ma’anarsa ba, amma ni na tabbatar cewa lalle zancen Allah ba ya savawa juna, kuma wannan jawabi ne mai kyau kuma daidai ne. Amma babu wanda zai fahimce shi sai wanda Allah ya yi ma gamdakatar, dan haka kada ka raina shi, domin shi kamar yadda Allah ya ce ne: “Kumaba za a cusa wa kowa wannan hali ba sai waxanda suka yi haquri, kuma ba za’a cusa shi ba sai ga maibabban rabo”. Suratul Fussilat, aya ta 35.Amma jawabi a dunqule, sai mu ce: Lalle maqiyan Allah suna da soke soke akan Musulunci, AddininManzanni waxanda suke kawar da mutane dasu daga bin Addinin Allah. Daga ciki akwai faxinsu cewamu ba ma yin shirka da Allah; muna shaidawa babu mai halitta da azurtawa, kuma babu mai amfanarwa ko cutarwa sai Allah shikaxai, bashi da abokin tarayya, kuma lallle Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba ya mallaka wa kansa wani amfani ko cuta, ballantana ma Shehu Abdulqadir ko waninsa, sai dai ni mai zunubi ne kuma salihai suna da makami a gurin Allah kuma ni ina nema gurin Allah ne ta hanyarsu. To, jawabinsa shi ne abin da ya gabata, wato shi ne cewa lalle waxanda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yaqe su suna tabbatar da abin da ka amtaba, kuma suna iqirarin cewa lalle gumakansu basa gudanar da komai, kawai suna neman alfarma dasu ne da ceto.Sannan kuma ka karanta masa abinda Allah ya faxa cikin littafinsa kuma ka qara masa bayaninsa. Idan ya ce ai waxannan Ayoyin sun sauka ne akan masu bautar gunki, ta yaya kuke sanya salihai kamar gumaka? Ko yaya kuke sanya Annabawa kamar gumaka? To, ka ba shi jawabi da abin da ya gabata, idan ya tabbatar da cewa lalle kafirai suna shaidar da Rububiyya dukanta ga Allah, kuma nufinsu daga waxanda suka fuskanta bai kasance ba face neman ceto, amma duk da haka yana so ya bambanta aikinsa da nasu da irin gurguwar hujjar da aka ambata, to sai ka ce masa: lalle kafirai cikinsu akwai mai kiran (roqon) gumaka, daga ciki kuma akwai masu kiran waliyyai, waxanda Allah ya ce a kansu: “Waxancan waxanda suke kiran suna neman tsani zuwa ga Ubangijinsu, waxannan ne mafifita a kusanci?” Suratul Isra’i, Aya ta 57.kuma suna roqon Isah xan Maryama da uwarsa, kuma Allah Ta’ala ya ce “Masihu xan Maryama bai kasance ba face Manzon Allah da mazanni suka wuce gabaninsa; kuma uwarsa Siddiqa (mai yawan ba da gaskiya) ce; sun kasance (Isah da Maryama) suna cin abin ci, ka duba yadda ake bayyana musu ayoyi sanann kuma ka duba yadda bijirewa gaskiya”. Ka ce: Shinkuna bautawa wanin Allah abin da ba zai mallaki cuta ko amfani a gare ku ba. Allah shi ne mai ji masani”. (Suratul Ma’ida, aya ta 75-76). Kuma ka ambata masa faxin Allah Ta’ala: Kuma ranar da Allah yake tara su gaba xaya, sannan ya cewa mala’iku: Shin waxannan ku suka kasance suna bautawa? Suka ce tsarki ya tabbata gare ka kai ne majivincinmu basu ba. A’a sun kasance suna bautawa aljanu ne; mafi yawansu dasu (aljanun) suka yi imani.” (Suratul Saba’i, aya ta 40-41).Da faxin Allah Ta’ala “Ka ambata lokacin da Allah ya ce; ya Isah xan Maryama! Shin kaine kace da mutane ku xauke ni da uwata abin buta biyu ba Allah ba? Ya ce tsarki ya tabbata gare ka, ba ya kasancewa a gare in faxi abin da bani da haqqinsa. Idan na faxe shi, to haqiqa ka sani; ka san abin da yake cikin raina amma ban san abin da yake cikin ranka ba. Lalle kaine mai yawan sanin abin da yake voye”. (Suratul Ma’idah, aya ta116).Ka ce masa shin ka san Allah ya kafirta wanda ya nufi gumaka? Kuma ya kafirta wanda ya nufi salihai (da sanin sa), kuma ManzonAllah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yaqe su. Idan ya ce: Ai kafirai suna nufin bauta musu ne, ni kumaina shaida wa lalle Allah shi ne maiamfanarwa kuma shi ne mai cutarwa kuma shi ne mai shirya al’amura, bana neman komai face gare shi. Su kuma salihai basu iya yin komai sai dai ina nufinsu don fatan cetonsu da Allah? To amsa itace: Lalle wannan irin maganar kafirai ce daidai da daidai. Sai ka karanta masa maganar Allah “Waxanda suka riqi wasu majivinta ba shi ba, (suna cewa) ai bama bauta musu sai domin kawai su kusanta mu zuwa ga Allah kusantawa….” (Zumar, Aya 3). Da kuma faxarsa: “Kuma suna cewa waxannan su ne masu ceton mu gurin Allah.” (Yunus Aya 18).Ka sani cewa waxannan shubhohi guda uku sne mafi girman abin da yake gare su. To idan ka san cewa Allah ya bayyana mana su cikin littafinsa kuma ka fahimta mai kyauto abin da yake bayansu ya fi sauqi.Ci gaba zai zo a bugu na gaba inshaAllah.

Reply

« Back to forum