luwadi ashi anci

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nura

36, male

Posts: 124

luwadi ashi anci

from nura on 08/06/2014 02:45 PM

MUT’A KO DAI ZINA (Luwadi)Ci gaba daga fitowa ta 250LUWAXI DA MATALalle kowa ya san luwaxi mummunar xabi’a ce kuma yana daga cikin manyan laifuffuka a wurin Allah (Subhanahu Wata’ala). Kuma haqiqa yin luwaxi na daga cikin abubuwan dake kawo musibu a cikin qasa. Shi ya sa saboda muninsa ko dabbobi ma suna qyamarsa, amma abin ba haka yake ba a wurin Shi’a `yan sha biyu, domin suna ganin halaccin yin luwaxi da mace, kamar yadda ya zo a cikin manyan littafansu ingantattu a wurinsu. Suna cewa: daga Safwan xan Yahya yana cewa “Na ce wa Arrida (A.S.) “Lalle wani mutum daga cikin bararrun bayinka ya umurce ni in tambaye ka game da wata mas’ala, sai ya ga girman kwarjininka, kuma ya ji kunyarka. Ya ce: Mece ce tambayar? Sai na ce masa “Mutum ne ya zo wa matarsa ta duburarta?”sai ya ce “Ya halatta a gare shi”. Saina ce “To kai kana aikata haka? Sai ya ce “Lalle mu bamu aikata haka?” (Ka duba: Furu’ul Kafi 5/1431 Hadsi na 10253.RA’AYIN KHUMENIAyatullahi Khumeni shi ma yana ganin halacccin luwaxi da mace, bayan ya lissafo wasu al’amura da suke haramta miji ya kusanci matarsa lokacin haila:Daga cikinsu:Haramcin takinta ta farji akan mijinda ita. Sai dai yana halatta ya ji daxida waninsa kamar sumba da wasa da cinyoyinta da abin da ya yi kamada shi; har takinta ta dubura a bisa zance mafi qarfi. Ko da yake an karhanta shi karhanci mai tsanani, amma abin da ya fi kewayewa ya nisance shi”.Ka duba: Tahrirul Wasila na Khumeni shafi na 46-47. Allah ya tsare mu.

Reply

« Back to forum