m kallan hadarin kaji
[ Go to bottom | Go to latest post | Subscribe to this topic | Latest posts first ]
m kallan hadarin kaji
from nura on 09/10/2014 07:49 AMDALILIN DA YASA MUKE WA MAULUDI KALLON HADARIN KAZAKashi Na Biyu (2).Abu ne sananne daga dalilan Alkur'ani da Sunnah, cewa duk wasu ayyuka suna ingantuwa neidan sun samo asali daga littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (S.A.W). Kuma wajibi ne a yi da'a ga duk abin da Allah da Manzonsa suka umurta ko suka yi hani. Ayoyi sun fi shurin masaqi da suka tabbatar da wannan, kamar yadda Allah Subhanahu Wa Ta'ala ya ce:"Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzonsa, da ma'abuta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa, idan kun kasancekuna imani da Allah da Ranar Lahira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara".[Suratun Nisa, aya ta 59]Ayoyin da suka zo da irin wannan ma'ana suna da yawa kwarai da gaske, alal misali duba Suratu Al'Imrana aya ta 32; Suratu Muhammad aya ta 33; Suratul Anfal aya ta 20; Suratul Mujadala aya ta 13; Suratul Tagabun aya ta 12; Suratul Anfal aya ta 1 da kuma aya ta 46.Mu hadu a Kashi Na Uku...

Reply