m kln hdarinkaji5

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nura

36, male

Posts: 124

m kln hdarinkaji5

from nura on 09/10/2014 07:51 AM

DALILIN DA YASA MUKE WA MAULUDI KALLON HADARIN KAZAKashi Na Hudu (4).Babu ko shakka akan cewa, duk wanda ke biye da mu akan ainihin abin da a ke muhawara a kansa ya san cewa wajibi ne ya gasgata Allah da Manzonsa (S.A.W), kuma wajibi ne ya nisanci abin da aka yi hani ga barinsa.Mine ne aka yi hani ga barinsa, a wannan muhawara? Amsa ita ce: "Bidi'ah" wato Kirkirarrun Al'amura, kamar Mauludi da sauransu. Saboda wannan dalilina musamman daga taskar Manzon Allah (S.A.W):An karbo daga Abu Najih, Irbad Ibn Sariya (R.A) ya ce:"Manzon Allah (S.A.W), ya yi mana wa'azi, mai isa matuqa cikin bayani; zukata sun tsorata da shi, kuma idanu sun kwararada hawaye saboda Shi, sai muka ce: Ya Manzon Allah! Kamar dai wannan wa'azin mai bankwana ne, don haka ka yi mana wasiyya. Sai ya ce: Ina yi muku wasiyya da tsoron Allah, Mabuwayi, Mai daukaka, da kuma ji da biyayya (ga wanda aka sa shi shugabanci a kanku), ko da kuwa bawa ne yake shugabanci a kanku. Domin lallai wanda ya yi tsawon rai daga cikinku, zai ga sabani da yawa. Sai ku lizimci Sunnata da Sunnar halifofi shiryayyu masu shiryarwa (da za su zo) a bayana. Ku yi riqo da ita, kuma ku cije a kanta da haqoranku. Kuma ku kiyayi kirkirarrun al'amura, domin kowane kirkirarren al'amari bidi'a ne, kuma kowace bidi'a bata ce".Duba wannan hadisi a cikin Arba'una Hadis na Imam Muhyiddeen Yahya Ibn Sharaf Al-Nawawi, hadisi na 28.To, daga dai qin gaskiya sai bata, yakamata masu makauniyyar biyayya su sake nazari, ko da zasu gane abin da Malamansu na yanzu ke musu na cuwa-cuwa da cuku-cuku.Saboda Mauludi dai bidi'a ne dadaular Fadimiyyah, wato 'yan Shi'ah a kasar Masar suka kirkiro, kuma sun fi kowa kwakwazo da zuguiguita wannan bidi'ar ta Mauludi.Mu hadu a Kashi na Karshe.

Reply

« Back to forum