m kln hdarinkaji5
[ Go to bottom | Go to latest post | Subscribe to this topic | Latest posts first ]
m kln hdarinkaji5
from nura on 09/10/2014 07:52 AMDALILIN DA YASA MUKE WA MAULUDI KALLON HADARIN KAZAKashi Na Karshe (5).Tun lokacin da na fara rubuta akan Mauludi na hadu da mashiririta iri-iri masu yunkurinkare Mauludi ta kowace hanya, amma ina abin ya ci tura. Saboda ba wani dalili na takanas daga Alkur'ani ko Hadisi da ya tabbatar da cewa, Mauludi addini ne, kai bil-hasil ma sabawa hanin Manzon Allah(S.A.W) ne.Dan uwa mai karatu, haqiqa Allah Ta'ala ya girmama dan Adam ya martaba shi, kuma ya bashi hankali da basira, hikima da azanci, da sanin ya kamata tayadda zai iya bambance gaskiyada karya. Babu ko shakka duk wanda ya samu wadannan ni'imomin Allah, kuma ya karanta wannan bayani tun daga kashi na farko har zuwa wannan na karshen, idan ya hada natijar, to zai fahimci muhimman abubuwa kamar haka:(1). Addinin Musulunci ya kammala, baya buqatar qari ko ragi, kamar yadda aya ta 3 a cikin Suratul Ma'idah ta bayyana.(2). An fara Mauludi a karshen qarni na 6 ko farkon qarni na 7, wato shekara 600-700 BH, saboda haka Mauludi bidi'ah ne.(3). Ba wani Tabi'ina ko Tabi'it Tabi'ina da ya yi Mauludi balle wani Sahabi. Kuma sune mafifitan wannan al'ummah.(4). Duk wanda ya kirkiro wani abu a cikin addinin Musulunci ko ya aikata wani aiki da babu umarnin Manzon Allah (S.A.W), to wannan aiki ba karbabbe ba ne a wurin Allah.(5). Tsawatarwa a kan bidi'ah, wato duk wani abu da za a qara cikin addinin Musulunci, misali Mauludi.(6). Duk wani abu da ya zama sabo cikin addinin Musulunci, ba shi da lada ko ta sisin kwabo,kuma ba shi da amfani a wurin Allah.(7). Wajibi ne Musulmi su nisanci abin da aka yi hani ga barinsa, kuma wajibi ne su bi umarnin Allah da Manzonsa.(8). Kowane kirkirarren abu bidi'ah ne, kuma kowace bidi'ahbata ce, kamar yadda Hadisi ya nuna daga Abu Najih, Irbad Ibn Sariya.(9). Horo da riqo da Sunnah, da tabbatar da cewa, bin Sunnar Manzon Allah (S.A.W) shi ne hakikanin son Annabi, amma bayin Mauludi ba.(10). Mauludi baya nuna son Manzon Allah (S.A.W), hasali ma saba masa ne, domin ya tsawatar da mu kan bidi'ah.Allah ya tabbatar da duga-duganmu a kan Sahihiyar hanya, kuma ya haska zukatanmu a kan fahimtar gaskiya, Ameen.

Reply