maulidi b m kashewando2

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nura

36, male

Posts: 124

maulidi b m kashewando2

from nura on 09/10/2014 07:44 AM

MAULUDI BIDI'AR MASU ZAMAN KASHE WANDOKashi Na Biyu (2).ASALIN MAULUDIAn fara Mauludi a garin Irbil a karshen qarni na shida, ko kuma farkon qarni na bakwai, wato shekara 600-700 bayan hijira. Wanda ya fara kirkira Mauludi shi ne sarkin Irbil Muzaffar ad-Din Abu Sa'eed Al-Kawkaburi, kamar yadda Malaman tarihi irin su Ibn Kasirda Ibn Khalikan suka bayyana.Wasu Malaman tarihi na cewa, farkon wadanda suka kirkira Mauludi su ne Banu Ubaid al-Kaddah, wandanda aka fi sanida "Fadimiyyuna" a kasar Masar. Asalin kakansu shi ne Ibnu Disan, wanda aka fi sani da Al-Kaddah, dan asalin garin Ahwaz.Idan ya tabbata cewa wadannan'yan Shi'ah sune farkon kirkira Mauludi, to wannan ba zai lizimci Ahlus Sunnah ba, domin Yahudawa suka assasa Shi'ah. Kuma da Yahudanci da Shi'anci duka daya ne, wai makafi sun yi dare, buqatarsu kurum su rushe addinin Allah.A biyomu akwai ci gaba, Insha Allahu.

Reply

« Back to forum