mutu a da matan aure

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nura

36, male

Posts: 124

mutu a da matan aure

from nura on 08/06/2014 02:08 PM

MUT’A DA MATAR AURE MAI MIJILalle kowa ya san mace mai miji tana daga cikin matan da Allah (Subhanahu Wata’ala) ya haramta aaura, har sai in mijinta ya sake ta kuma ta yi Idda, to babu laifi a aureta bayan Idda. Allah (Subhanahu Wata’ala) yana cewa “Da tsararrun wasu maza (wato an haramta muku matan aure masu maza matuqar mazansu basu sake su ba)Nisa’i 24.To amma abin ba haka yake ba a Shi’a `yan sha biyu, domin sun halatta mut’a da matar aure mai miji kamar yadda suka ruwaito daga Fadlu bararren bawan Muhammad Xan Rashid daga Abu Abdullahi (A.S.) ya ce nace: Lalle ni na auri mace auren mut’a, sai tunanin tana da miji ya auku a raina, sai na bincika haka, sai kuwana samu tana da miji? Sai ya ce: “Saboda me ka bincika?” Ka duba: Furu’ul kafi na Kulaini 5/1394 Hadisi na 9933. Da kuma Tahzhibul Ahkam 7/1003 Hadisi na 9300.NASIHATA GA MATAR MUT’AYa ke `yar’uwa! Kiji tsoron Allah ki kama kanki, wallahi auren mut’a baauren Sunnah ba ne, zina ce, ba irin auren da kakanninki suka yi ba ne, kuma ba da shi iyayenki suka samar dake ba. Saboda haka kada ki samar da `ya’yanki ta irin wannan aure, domin kawai buqatarwani, domin wallahi zaki tsaya a gaban Allah (Subhanahu Wata’ala) ke da wanda ya xauki hayarki, domin ki yi masa bayani, saboda haka kada ki bari a mayar dake karuwa da sunan Addini, ki yi mazaki tuba tun kafin mutuwa ta riske ki a lokacin da tuba ba ta da amfani. Wallahi baki da wata hanya ta tsira face ki rungumi Aqidar Sunnah, Aqidar da Manzon Allah (SallallahuAlaihi Wasallam) ya bar Sahabbansa da Ahlul baiti akanta, Aqidar tausayi, mutumci, kunya da kare `yancin mata.Xan’uwanki a Musulunci, mai tsananin tausayinki, da qaunarki dafatan alkhairi a gare ki:“Mawallafi”.

Reply

« Back to forum