san annabi

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nura

36, male

Posts: 124

san annabi

from nura on 08/06/2014 02:36 PM

Hakikanin kaunar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama..( Sheikh Abdulwahhab Abdullah).January 24, 2014 12:20 am.Alhamdu lillahi rabbil A’lamin,Wa sallallahu wa sallama alaNabiyyina Muhammad wa ala alihi wasahbihi ajma’in.Amma ba’ad;.Lallai wanda yake son Manzon Allasallallahu alaihi wa sallama zai fifita shi akan duk abin da yake da girmako daraja ko tsada a gunsa. Dominson Allah da manzonsa sune imani,kuma imanin bawa bazai cika ba saida su. Allah subhanahu wa ta’alayace:.“ kace idan har iyayenku da‘ya’yanku da ‘yan uwanku damatanku da danginku da dukiyar da kuka tsuwurwurta dakasuwancin dakuke jin tsoron tasgaronsa da gidajeda kuke yarda dasu sune suka fisoyuwa a gareku daga Allah daManzonsa da jihadi saboda Allah ;toku zauna har Allah ya zo daal’amarinsa, allah baya shiryar dafasikai” {Tauba :24}..Wannan ayar nassi ce karara a bisawajibcin kaunar Manzon Allahsallallahu alaihi wa sallama,dawajibcin gabatar da wannan kaunarakan duk wani abin kauna.Alkali Iyadh yace: “wannan ayar taisa wajen zaburarwa da fadakarwa dashiryarwa da zama hujja ta gaske abisa wajibcin kaunar Manzon Allahsallallahu alaihi wa sallama dacancantarsa da wannan soyayyar,domin Allah ya kwankwashi wadandadukiyarsu da iyalansu da ‘ya ‘yansusuka fi soyuwa a garesu fiye da Allahda manzonsa,kuma yayi musu narkocewa su jira har Allah ya zo daal’amarinsa,sannan ya fasikantar dasu, ya kuma sanar da su cewa sunbacewa hanya madaidaiciya, Allah bazai shiryar da su ba.Hakanan kuma wanda ya yi la’akarida wannan ayar zai ga cewa umarninbai tsaya ga samuwar soyayya gaAllah da Manzonsa kadai ba, barimadai dole ne sai wannan son ya zamasama da son duk wani abu wanda basu ba..Wa sallallahu wa sallama alaNabiyyina Muhammad wa ala alihi wasahbihi ajma’in.

Reply

« Back to forum