Latest posts
First Page | « | 1 ... 3 | 4 | 5 | 6 | 7 ... 24 | » | Last
Search found 237 matches:
ina ALLAH yake2
from nuramuhd3 on 04/26/2015 09:54 PMAn kavo daga Nafi’u daga Abdullahi xan Umar (R.A) ya ce: Lokacin da Manzon Allah (S.A.W) ya rasu, sai Sayyadina Abubakar ya ce: “Ya ku mutane idan kun kasance Muhammadu shi ne Ubangijin da kuke bautawa, to, Muhammadu ya mutu. Idan kun kasance Allah (S.W.T) kuke bautawa, to Allah wand ayake sama ba zai mutu ba”. Sai Abubakar (R.A) ya karanta aya ta 144 cikin Ali-Imrana wadda take tabbatar da cewar Annabi (S.A.W) zai mutu. Abu Sa’id Addarimi ya fitar da hadisin a cikin littafinsa na Raddu alal-Jahmiyya shafi na (44 – 45).Wani hadisi da malamai sukafi kafa hujja da shi, shi ne hadisin wani Sahabi mai suna Mu’awiyya bin Hakam Assulamiy, wanda yake buqatar ’yanta baiwarsa. Sai Annabi ya ce ya zo da baiwar, lokacin da ya kawo tagaban Annabi (S.A.W) sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da baiwar: “A ina Allah yake?” Sai ta ce: “Yana sama”.Sai Annabi (S.A.W) ya ce mata: “Ni wane ne?” Sai ta ce: “Kai Manzon Allah ne”. Sai Annabi ya ce da Mu’awiyya ka ’yanta ta dominita mumina ce”. Allah Akbar! Wato wannan hadisi yana nuna mana cewar yarda da tabbatar da cewa Allah yana sama, yana daga tabbatar imanin mumini. Saboda haka, Imam Sa’id –Darami cikin Raddu al-Jahmiyya yake cewa: “Idan mutum bai yardacewar Allah yana sama ba, toshi ba mumini ba ne, ko da waye kuwa. Domin ’yantawa bai tabbatar ba ga wannan baiwa har sai da aka tabbatar da imaninta na cewar Allah yana sama”. Wannan hadisi na Jariya kamar yadda malamai suke kiran sa. Imam Bukhari ya fitar da shi cikin littafin Juz’ul Qira’a Khalfal Imam. Imam Muslim, Nisa’i da Ibn Khuzaima duk sun rawaito shi da jingine mai inganci.An karvo hadisi daga Usamatu ibn Zaid ya ce: “Na ce da Manzon Allah (S.A.W) ya Manzon Allah na ga kama azumin wani wata fiye da sauran watanni sai dai watanRamadan”. Sai Annabi ya ce: “Wane wata ne?” Sai na ce: “Watan Sha’aban”. Sai Annabiya ce: “Shi ne watan da ake xaukaka ayyukan bayi zuwa ga Ubangijina Talikai a cikinsa. Saboda haka ya sa nake son a xaukaka aikina, ina mai Azumi”. Imam Ahmad da Nasa’i suka rawaito da jingine mai kyau.Saboda haka wannan hadisi hujja ne domin ana xaukaka ayyukan bayi zuwa sama ake nufi wajen Allah. Haka nan hadisin Mi’iraji wanda na kawo a babin da ya wuce shi ma hujja ne.DALILAI DAGA MAGABATA NA GARIAqidar Ahlus Sunna wal Jama’a shi ne kafa hujja daga littafin Allah da sunnar Manzon Allah (S.A.W) a bisa fahimtar magabata na gari. Domin Annabi ya ce: “Fiyayyen mutane su ne waxanda na rayu da su, sai waxanda suka bi su, sai waxanda suka biyo waxanda suka bi su”. Ma’ana su ne sahabbai, tabi’ai da kuma tabi’ut tabi’ina. To waxannan su ne ajin farko na magabatana gari. Kuma ga hujja daga Alqur’ani da take nuna mana wajabcin koyi da abin da suka yi ijma’i a kansa. Allah yana cewa: “Kuma wanda ya sava wa Manzo daga bayan shiriya ta bayyana a gare shi,kuma ya bi wanin muminai, za mu jivintar masa abin da ya jivinta. Kuma mu qone shida jahannama, kuma ta munana ta zamo makoma”. (Nisa’i: 115).Xaya daga cikin malamai magabata Imamul Auza’i ya ce: “Mu da Tabi’ai mun kasance muna cewa Allah (S.W.T) yana sama, kuma mun amince da siffofi”.Imamul Shafi’i cewa ya yi: “Allah (S.W.T) yana bisa Al’arshinSa a cikin sama yan akusantar bayinSa yadda ya so, kuma yana saukowa zuwasaman duniya yadda ya so”.Imamu Abu Hanifa kuwa cewa ya yi: “Duk wanda ya ceban sani ba, shin Allah yana qasa ko yana sama? To, ya kafirta. Domin Allah ya ce: “Mai Rahama ya daidaita a kan Al’arshinSa”. (Ash-shura: 10) domin Al’arshi tana saman sammai duka…”.Wannan shi ne ra’ayin malamai magabata na gari. Kuma a farko mai karatu ya karanta bayanin Imamu Malik na tabbatar da cewar Allah yana bisa Al’arshinSa.Mai karatu waxannan abubuwa da muka bayyana duka, shi ne aqidar Manzon Allah (S.A.W) ya kawo a cikin shari’arsa zahiri ba baxini ba.Kuma ita ce aqidar da sahabbai suka tafi a kanta, kuma muna fatan Allah (S.W.T) ya karvi rayukanmu akanta.Haqiqa mun yi Imani da Allah (S.W.T) yana tare da halittarSa da jinSa da iliminSa da ganinSa, yana bisa Al’arshinSa, kuma yana ganin ayyukansu. Kuma yanatsara al’amarinsu yana azurta talaka, yana xora karyayye, yana ba da mulki ga wanda ya so. Yana qwacewa daga wanda ya so. Kuma yana xaukaka wanda ya so. A hannunsa alheri yake kuma shi a bisa dukkan komai mai iko ne.Wanda ya kasance haka sha’aninsa yake. To, lallai yana tare da halitarsa a haqiqa, yana ganin su yana jin su, kuma yana bisa da su a Al’arshinSa. “Babu wani abu da ya yi kama da shi, kuma shi mai iko ne mai gani”. (Ash-shura: 11).Kuma ba za mu faxi irin abin da qungiyar Haruriyya daga cikin ’yan Jahamiyya da ire-irensu suke cewa ba. Wai Allah yana tare da halittarSa a kan doron qasa. Kuma wai yana ko’ina. Duk wanda kuwaya siffanta Allah da waxannan abubuwa, to, ya siffanta Allah da siffofin da ba su dace da Allah ba na tawaya. Wanda wasu malamai suna ganin wannan zai iya kai mutum ga kafirci!DALILAN MASU CEWAR ALLAH YANA KO’INAAkwai wata aya da masu da’awar Allah yana ko’ina suke kafa hujja da ita cewar Allah (S.W.T) yana ko’ina. Inda Allah yake cewa: “Kuma shi ne Allah a cikin sammai kuma a cikin qasa yana saninasirinku da bayyananku, kuma yana sanin abin da kuke yi na tsirfa”. (An’am: 3).To, amma manyan malamai magabata sun fassara wannan ayar da cewar: Inda Allah ya ce: “Kuma shi ne Allah a cikin sammai”. Wato ma’ana shi ne wanda yake sama bisa Al’arshinSa sai kuma ci gaban ayar ya ce: “Kuma a cikin qasa yana sanin asirinku da bayyanenku”. Wato ma’ana a qasa yana sanin asirinku da abin da kuke bayyanawa duk da kasancewarSa yana sama.Saboda haka wannan aya ba hujja ba ce a wajensu, illa maraddi take yi musu.Haka nan suna kafa hujja da aya ta 84 a cikin Suratul Zukhruf inda Allah ya ce: “Kuma shi ne wanda ake bautawa a sama, kuma abin bautawa a qasa, kuma shi nemai Hikima Masani”. Wannan aya ba tana nufin Allah yana sama kuma yana qasa ba, a’a, tana nuna manahalittun sama da na qasa dukAllah suke bautawa.Suna kuma kafa hujja da indaAllah yake cewa: “Shi ne wanda yake tare da ku duk inda kuke, kuma Allah mai gani ne ga abin da kuke aikatawa”. (Hadid: 4) da kuma faxin Allah inda yake cewa: “Ashe ba ka ga cewa lallai Allah yana sane da abinda ke cikin qasa ba? Wata ganawa ta mutum uku ba za ta kasance ba face Allah shi ne na huxu xinta, kuma babuta mutum biyar facer shi ne na shida xinta, kuma babu abin da ya kasa. Wannan kuma babu abin da yake mafiyawa face shi yana tare da suduk inda suka kasance, sannan ya ba su labari game da abin da suka aikata a ranar qiyama. Lallai Allah Masani ne ga dukkan komai”.(Mujadala: 7) Suna kafa hujjaa waxannan ayoyi cewa ai Allah ya ce: “Yana tare da su duk inda suka kasance”. Sai su ce ai yana tare halittarSa. To, amma Imam ibn Kathir ya fassara wannan aya da cewar: “Ma’ana yan atare da halittarsa yana sanin ayyukansu duk inda suka kasance a tudu ko a kwari da dare ko rana a gidajensu da sauransu”. Saboda haka wannan duk yana sanin su da ilminSa da ganinSa da jinSa. Yana jin zancensu, yana kallon su, yana sanin sirrinsu da bayyanensu. Ba ka ji ma abin da ya ce da Annabi Musa da Haruna ba? Lokacin da ya aika su wajen Fir’auna? Sai ya ce musu: “Ya ce kada ku ji tsoro, lallai ni ina tare da ku, ina ji kuma ina ganin ku”. (X.H: 46). Wannan aya ta fassara manawaxancan ayoyi da muka ambata a baya. (Ma’ana aya takan fassara wata ayar a Alqur’ani).Har yanzu dai sukan kafa hujja da ayar da ke cewa: “Mai Rahama ya daidaita a kan Al’arshinSa”. (X.H: 5). Suna fassara ta da Tawili su ce wai ba Istawa (ya daidaita)ake nufi ba amma Istaula (ya mamaye) ake nufi. To, a nan muna da ma’auni wato Annabi da Sahabbai da Magabata, sun fi mu sanin Tafsirin Alqur’ani (saboda haka sun fi mu fahimtarsa), amma ba su fahimci ayar a haka ba. Waxannan mutane shin suna nufin sun fi Annabi(S.A.W) da sahabbansa saninAlqur’ani ke nan?A wannan matsala Babban Magabacin malamin nan Ibn Qayyim Al-Jauziy ya ce: Allah ya umarci Yahudawa da cewar ku ce hixxa sai suka cehinxa suka canja harafi xaya.Saboda haka Allah ya yi musu uquba ba. To, haka nan sai Allah ya ce Istawa saimasu Tawili suka ce Istaula. Mai karatu ka duba yadda waxannan mutane suka yi aiki daidai da na Yahudawa. Domin duk aikin nasu babu bambanci. Ka duba Suratul Baqara ka ga yadda Allah yake mayarwa da Yahudawa raddi.Lallai Ma’aiki (S.A.W) MA’ANARSA1. Al-Ibana An Usuluddiyana:Imam Abdul-Hasan Al’Ash’ariy.2. Raddi Alal Jahmiyya: ImamAbu Sa’ida Ad-Darini.3. Tarjamar Alqur’ani Mai girma: Sheikh Abubakar M. Gumi.4. Tafsiril Qur’anil Azeem: Imam ibn Kathir.5. Aqidatu Ahlus – Sunnah wal Jama’a: Sheikh Muhammad Saleh Al-Uthimeen.6. Sharhi Usulul Imam: Sheikh Muhammad Saleh Al-Uthaimeen.
a ina ALLAH yake
from nuramuhd3 on 04/26/2015 09:48 PMGODIYA TA MUSAMMANNa yi godiya ga Allah (S.W.T) da ya qaddari na zamo cikin Musulmi, har na rayu cikin Musulunci tare da yin xan wani abu a cikinsa. Ba tare da alfahari ba, ina godiya ga Annabin Rahama (S.A.W) da ya bayyana komai filla-filla ba tare da voye wani abu ba a cikin Manzanci.Ina kuma qara godiya ga magabata na gari – sahabbaida waxanda suka biyo su da kyautatawa, waxanda a cikin bincikensu ne, na tsakuro abin da na gabatar a wannanxan qaramin littafi.Ina godiya ga dukkan malamai na addini da na boko waxanda da hasken karantarwarsu ne na dubo duk abin da na rubuta. Godiya ta musamman ga Malam Abdullahi Saleh Pakistan, shugaban Jama’atu Izalatil Bidi’a wa Iqamatis Sunnah na Jihar Kano, kuma Limamin Masallacin Tudun Murtala, wanda ya karanta littafin daga farko har qarsheya kuma yi gyare-gyare a cikinsa.Haka kuma ina godiya ga xan’uwa Imam Ja’afar Mahmud Adam, Darakta na Makarantar Usman bin AffanGadon Qaya, wanda shi ma ya karanta littafin kafin a buga, ya kuma bayar da shawarwari masu muhimmanci.Godiya ga Alhaji Ibrahim Xanyaro wanda da taimakonsa ne littafin ya zama yadda yake a yanzu. Wato shi ya xauki nauyin buga littafin. Allah ya saka masa da alheri, amin.A qarshe ina godiya ga dukkan abokaina da suka ba ni qwarin gwiwa da shawarwari har littafin ya zama haka.MA’ANAR IMANI DA ALLAHImani wani abu ne wanda zuciya take qudurta shi, harshe yake furta shi, aiki yake tabbatar da shi. Haka nan Imani da Allah yana nufin qudurcewa da tabbatarda kaxaita Allah (S.W.T) a cikin sanin Shi ne Ubangiji Mahaliccinmu, mai rainonmu (Tauhidin Rububiyya). Haka kuma yana cikin Imani da Allah kaxaita shi da bauta Shi kaxai ba tareda yi masa kishiya ba wato (Tauhidin Uluhiyya). Sannan yana daga cikin Tauhidi ko Imani da Allah yin Imani da siffofinSa da sunayenSa Maxaukaka waxanda suka tabbata a cikin littafinSa Alqur’ani da waxanda Annabi(S.A.W) ya tabbatar masa.Saboda haka Tauhidi ya kasu kashi uku kamar haka:1. Tauhidur Rububiyya: Shi ne kaxaita Allah a ayyukanSa Shi Allah. Shi ne mai azurtawa, mai rayawa, mai kashewa, mai rainon mu. Kuma wanda halitta da iko duk a hannunSa suke. Babu mai waxannan ayyuka sai Shi. Domin Allah yana cewa: “Allah ne mai halitta dukkan komai, kuma Shi ne wakili a kan komai”. (Zumar: 62).Hatta mushirikai sun tabbatar da wannan Tauhidi domin sun yi imanin Allah nemai halitta. Allah yana cewa: “Ka ce wane ne yake azurta ku daga sama da qasa? Shin ko kuma waye yake mallakar ji da gani, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga cikin mamaci, kuma ya fitar da mamaci daga mai rai, kuma wane ne yake shirya al’amari?” To, za su ce “Allah”. To ka ce: “Shin ta ba za ku yi taqawa ba?” (Yunus: 31).2. Tauhidul – Uluhiyya: Shi nekaxaita Allah da bauta, a ayyukan bawa. Ma’ana, Allah Shi ne wanda yake abin bautawa ba tare da haxa shi da kowa ba a cikin bauta. Ba a haxa Allah cikin bauta kamar addu’a, neman tsari, Salla, Azumi, Hajji da sauransu. Domin Allah Mai Tsarki yana cewa: “Ka ce, Ni, mutum ne kawai kamar ku, ana yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lallai ne abin bautawarku, abin bautawa guda ne, saboda haka wandaya kasance yana fatan haxuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na qwarai kuma kada ya haxa kowa ga bauta wa Ubangijinsa”. (Kahfi: 110).Haka nan Allah yana cewa: “Allah ya shaida cewar lallai ne babu abin bautawa face Shi, kuma mala’iku da ma’abota ilmi sun shaida. Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai hikima”. (Ali-Imran: 18). Saboda haka duk wanda ya yi shirka, to ya haxa Allah da wani cikin bauta. Kuma Tauhidin Uluhiyya ya rushe, saboda makomarsa hasara ne. domin Allah ya ce: “Kuma mun yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waxanda ke gabanka: Lallai idan ka yi shirka, haqiqa, aikinka zai vaci, kuma lallai za ka kasance daga masu hasara”. (Zumar: 65).Amma Tauhidin Uluhiyya ba a yi tarayya da kafirai da mushirikai ba, kamar yadda ake tare a cikin Rububiyya. Maxaukakin Sarki ya ce: “Lallai su (kafirai) sun kasance idan an ce musu Babu abin bautawa, face Allah”. Sai su xora girman kai. Kuma suna cewa: “Shin mu lallai masu barin gumakanmu ne, saboda maganar wani mawaqi, mahaukaci”. (Saffat: 35 – 36).3. Tauhidul Asma’i Wassifati: Shi ne Imani da sunayen Allah da siffofinSa waxanda Allah (S.W.T) ya ambata a cikin littafinsa Alqur’ani ko kuma waxanda AnnabinSa (S.A.W) ya ambata a cikin hadisansa ingantattu, kamar yadda suka zo ba tare da korewa, ko kamantawa ba. Haka nan ba tare da misaltawa ko gogewa ba. Domin Allah ya ce: “Wani abu bai kasance tamkar kamarsa ba”. (Shura: 11). Haka ya sake cewa: “Sannan kada ku bayar da waxansu misalai ga Allah. Lallai ne Allah yana sani, kuma ku ba ku sani ba”. (Nahli: 74).Saboda haka Allah yana da sunaye da dama kuma yana da siffofi waxanda suka dace da shi. Lallai mun yi imani daabin da ya zo daga Ayatul Kursiyyu da Suratul Ikhlas damafi yawan surorin Makka da suke maganar sunayen Allah da siffofinsa. Haka surorin Madina, kai mafi yawan Alqur’ani yana magana a bisa haka. Misali, farkon suratul Fatiha – “Bismillahir Rahmanir Rahim”. Ma’ana: “Da sunan Allah mai Rahama, mai Jinqai”. A nan mun fahimci Allah ya ambaci kansa yana da sunaye, mai Rahama, mai Jinqai.Haka nan cikin siffofi Allah yanuna mana cewa yana gani yana zance, yana ji da sauransu. Misali, Allah ya ce:“Ya kuma kasance mai ji ne mai gani”. (Nisa’i: 134). Kumaya ambaci kanSa cewar mai gafara ne: “To lallai ne Allah ya kasance mai gafara mai jinqai”. (Nisa’i: 129). A cikin surori da dama Allah ya ambaci cewar yana da haquri, yana afuwa da sauransu. To, yana daga cikin siffofinsa cewa YA DAIDAITA A KAN AL’ARSHINSA wato daidaito wanda ya dace da shi. Tsira ya tabbata a gare Shi.IMANI DA AL’ARSHIKafin mu kawo hujjojin da ke tabbatar da cewa Allah ya daidaita a kan Al’arshi. Tilas ne mu nusar da cewa, wajibi ne mutum ya yi imani da Al’arshi, amma shin menene ake nufi da Al’arshi? Kuma waxanne hujjoji ne suka tabbatar da wanzuwarsa?Al’arshi wani bigire ne a saman sammai duk inda Allah (S.W.T) ya ambata cewar ya daidaita a kansa. Kuma Shi Al’arshi, Allah ya halicce shi kafin halittar sama da qasa, Subhanahu wa Ta’ala. Kuma Allah ya tabbatar da Al’arshinSa a wurare da dama a cikin Alqur’ani kamar inda ya ce: “Kuma Shi ne wanda ya halicci sammai da qasa a cikin kwanaki shida, kuma Al’arshinSa ya kasance a kan ruwa”. (Hud: 6).Kuma hadisan Annabi (S.A.W) sun tabbatar da Al’arshi kamar hadisin Imranibn Hussain ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku karvi bushara banu tamin”. Sai suka ce: “Ka yi mana bushara, to ka ba mu”. Sai fuskar Manzon Allah (S.A.W) ta nuna vacin rai. Daga nan sai mutanen Yemen suka zo sai ya ce: “Ku karvi bushara mutanen Yemen”. Sai suka ce: “Mun karva”. Sai Annabi ya ba su labarin wannan halitta yadda aka fare ta. Ya ce: “Allah ya kasance kafin komai, kuma Al’arshinSa tana kan ruwa”. Imamul Bukhari da Muslimu suka rawaito da lafazi mai kyau.Saboda haka wannan hadisi yana nuna mana lallai akwai Al’arshi tun da Annabi (S.A.W) ya yi mana bayaninsa. Saboda haka wajibi ne mu yi imani da kasancewarsa. Allah kuma yace: “Mai rahama Ya daidaita a kan Al’arshi”. (DH: 5). Haka nan Allah ya sake ambatar Al’arshi a cikin Suratul – Furqan a ya ta (59). Inda ya ce: “Wanda ya halitta sammai da qasa da abin da yake a tsakaninsu, a cikin kwanuka shida, sannan ya daidaita a kan Al’arshi, mai Rahama, sai ka tambayi mai ba da labari game da shi”.Ubangiji mai Tsarki ya kuma cewa: “Kuma kana ganin mala’iku suna masu tsayuwa da haqqoqin da aka xora musu daga kewayen Al’arshi suna tasbihi game da gode wa Ubangijinsu”. (Zumar: 75).Tunda mun tabbatar cewa akwai Al’arshi, kuma kamar yadda muka bayyana a babinTauhidul Asma’i wassifati cewar Allah ya daidaita a kanshi wannan Al’arshi, wanda yake can sama. To, za mu bayar da dalilan mu daga Alqur’ani da hadisi da kuma haxuwar malamai na gari (magabatansu da waxanda suke raye), a bisa wannan matsala.DALILAI DAGA ALQUR’ANIDalilinmu na farko shi ne Alqur’ani domin Allah (S.W.T)yana cewa: “Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah, ku bi Manzo da ma’abota al’amura daga cikinku, (shugabanni). Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa, idan kunkasance kun yi imani da Allah da ranar lahira wannanshi ne mafi kyau ga fassara”. (Nisa’i: 59).Saboda haka lallai mun yi jayayya a bisa cewar: “Shin a ina Allah yake?” Domin samun amsa ingantacciya, sai ayar ta nuna mana sai mu mayar da abin jayayyarmu zuwa ga Allah daManzonSa. Bari mu ji abin daAllah ya ce: “Mai Rahama ya daidaita a kan Al’arshinSa”. (Suratul X.H: 5). Ma’anar wannan shi ne Allah (S.W.T) ya daidaita wato yana bisa Al’arshinsa a sama. Wannan aya tana nuna mana quru-quru cewar Allah yana sama. To, a nan Allah ya tabbatar mana cewar ya daidaita a kan Al’arshinSa. Daidaito wanda ya dace da shi. Amma yaya ya daidaita? Shi ne ba mu sani ba, kuma Musulmi ba ya halarta ya tambayi yaya Allah ya daidaita a kan Al’arshi? Wato daidaito ne ba irin wanda muka sani ga abin halitta ba. Kamar a ce: “Wane ya daidaita a kan kujera ko ‘’yana kan abin hawa” da sauransu. A’a ba amisalta Allah da kowa domin ya ce: “Wani abu bai zama kamar tamkarsa ba, kuma shi mai ji ne, mai gani”. (Shura: 11).Imam Malik ibn Anas (Allah ya ji qansa), an tambaye shi a kan cewar “Allah ya ce ya daidaita a kan Al’arshi to yaya daidaiton yake?”sai Imam Malik ya ce: “Daidaito dai sananne ne, yaya ya daidaita ba a sani ba. Kuma tamaya a kan yaya Allah ya daidaita bidi’a ce…”.Mai karatu, ka sani cewar babu abin da zai gyara al’ummar nan ta qarshe sai bin da ya gyara ta farkonta. Abin da ya gyara al’ummar farkonta kuwa shi ne littafin Allah da sunnar Manzon Allah (S.A.W). domin Annabi (S.A.W) ya ce: “Na bar muku abubuwa guda biyu. Ba za kuvata ba, matuqar kun yi riqo da su. Su ne: littafin Allah da Sunnata”.To, a kan waxannan abubuwa biyu za mu gina hujjojinmu na tabbatar da cewar Allah (S.W.T) yana sama a bisa Al’arshinSa.Da farko Allah yana cewa: “Shin ko kun amince wanda yake cikin sama, ba zai iya shafe qasa tare da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza? Ko kun amince wanda ke cikin sama ba zai iya sako muku iskar guguwa ba? To za ku sani yadda (aqibar) gargaxina take”. (Mulk: 16 – 17). Waxannan ayoyi guda biyu na Suratul Mulk suna nuna mana, Allah shi ne wanda yake a saman kuma a bisa Al’arshinSa. Domin shi Al’arshi yana saman sammai duka. Kasancewar Al’arshi tana saman sammai, sai Allah ya ce: “Ko kun amince wanda yake sama…”. Yana nufin wanda yake saman sammai duka a bisa Al’arshinsa, ba wai yana cikinsama yana nufin yana cikin kowace sama ba. Domin sammai har bakwai ne, to allahyana saman sama ta bakwai da zatinSa, amma yana sane da mu da ganinSa da iliminSa (S.W.T).Haka nan lokacin da Yahudawa suke ganin sun kashe Annabi Isa (A.S) sai Allah ya ce musu ba su kasheshi ba ko gicciye shi ba. Domin Allah ya tabbatar musu da Isa (A.S) yana ina? Sai ya ce: “A’a, Allah ya xaukeshi zuwa gare Shi, kuma Allah ya kasance Mabuwayi. Mai hikima”. (Nisa’i: 158). Ma’ana, wannan aya tana nuna mana cewar Allah ya xauke Isa (A.S) zuwa gare shia sama, kuma dukkanin Musulmi sun yarda cewar yana sama, kuma zai dawo qasa. Har ma muna jiran saukowarsa, kamar yadda Hadisan Manzon Allah (S.A.W) suka nuna.Xaya daga cikin hadisan shi ne wanda Imamul Bukhari yarawaito a babin saukowar Annabi Isa: abu Huraira (R.A)ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Na rantse da wanda raina yake hannunSa, ya kusata xan Maryam ya saukomuku yana mai hukunci, kuma mai adalci…”. A nan Annabi (S.A.W) ya tabbatar mana cewar Annabi Isa (A.S) yana sama, kuma zai sauko qasa. Saboda haka lallai Annabi Isa yana wajen UbangijinSa a sama.A cikin (Suratul Faxir: 10) Allah ya ce: “Zuwa gare shi magana mai daxi ke hawa, kuma aiki ne qwarai yana xaukakarsa”. Ma’ana yana xaukarsa zuwa sama. Haka nan dai Allah ya ce: “Yana shirya al’amari daga sama zuwa qasa, sannan ya taka zuwa gare shi a cikin yini, wanda gwargwadon shekaru dubu ne daga abin da kuke lissafawa”. (Suratul Sajda: 5).A cikin (Suratul Ghafir: 36) Allah ya ce: “Kuma Fir’auna ya ce ya Hamana ka gina mini bene tsammanina za ni isa ga qofofi. Qofofin sama domin yi tsinkaya ga abin bautawar Musa. Kuma lallai ni haqiqa ina zatonsa maqaryaci”. A nan, Fir’auna kansa ya san Allah yana sama, kuma hujjar da take qara tabbatar mana da haka shi ne Allah (S.W.T) bai yi wa Fir’auna raddi game da iqirarinsa na cewar Allah yana sama ba. Fir’auna ba Musulmi ba ne, amma Allah ya tabbatar da maganarsa domin gaskiya ya faxa.Haka nan cikin (Suratul Ma’arij: 4) Allah ya ce: “Mala’iku da Ruhi (Jibril) sunatakawa zuwa gare shi”. Ma’ana suna takawa wajen Allah wanda yake bisa Al’arshi a sama.Wata hujja da ta qara fito da abin fili ita ce aya ta farko ta cikin Suratul Isra’i inda Allah ya ce: “Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da BawanSa, da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nisa, wanda Muka sanya albarka agefensa domin Mu nuna masa daga ayoyinmu. Lallai ne shi, shi ne mai ji, mai gani”. (Isra’i: 1).Isra’i shi ne tafiyar dare da Allah ya yi da Annabi daga Makka zuwa Baitul Muqadis. Sannan Mi’iraji zuwa sama inda aka ba shi salloli. Ma’ana, Isra’i kullum tare yake da Mi’iraji. Saboda hakamasu da’awar Allah ba a sama yake ba, suna iya cewar Isra’i da Mi’iraji da Buraqa duk ba su da ma’ana.An karvo daga Yunus daga Hishab daga Anas bin Malik ya ce: “Abu Zair (R.A) yana bada hadisi daga Annabi (S.A.W) cewar: “An buxe rufin xakina ina Makka, sai Jibrilu ya sauka ya xauke ni zuwa saman duniya. Lokacin da muka isa saman duniya sai Jibrilu ya ce da mai tsaron qofar saman ‘ka buxe mana qofa’. Sai ya ce: ‘Kai da wane ne?’ Sai ya ce: ‘Ni da Muhammadu’. Sai ya ce: ‘An aiko masa ya zo ne?’ Sai ya ce: ‘Na’am! Sai aka buxe musu qofa…’. A qarshen hadisin Annabi ya iske Annabawa kamar su Adam, Idrisu, Musa, Isa da Ibrahim (A.S) Bukhari ya rawaito wannan hadisi ba ya buqatarwani qarin bayani, hujja ce qarara.Gaskiya dalilai daga Alqur’animai girma suna da yawa, ba zan iya kawo su duka a cikin wannan qaramin littafi ba, domin suna da dama.DALILAI DAGA SUNNAHSunnar Manzon Allah (S.A.W)ita ce matakina biyu na kafa hujja a cikin Shari’ar Musulunci. Domin Allah ya ce: “Duk abin da Manzo ya zomuku da shi, ku riqe shi. Dukabin da ya hane ku, to ku hanu”. (Hasari: 7). Saboda haka Annabi (S.A.W) ya zo mana da sunna. Kuma Allah ya sake cewa: “Lallai waxanda suke sava wa tunaninsa (shi Annabi) su yi jiran wata azaba mai raxaxi ta same su”. (Nur: 63).Saboda haka lallai za mu kafahujjoji daga sunna na tabbatar da cewar Allah yanabisa Al’arshi. Amma ba kowa zai yarda ba, sai mai imani. Domin a cikin Suratun Nisa’i: 65 Allah ya nuna mana cewaryarda da hadisi/sunna yana cikin imani inda ya ce: “To a’aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi imani ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin daya sava a tsakaninsu, sannan kuma ba su sami wani qunci a cikin zukatansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama, sallamawa”.To, a cikin sunnar ne muka iske hujjoji da dama da ke tabbatar mana cewa Allah (S.W.T) yana sama ya daidaita a kan Al’arshi. Daidaito wanda ya dace da shi. Aqidar da ta sava wa masu cewar Allah yana ko’ina, ana nufin yana cikin qazanta ke nan. Ko kuma idan yana jikin halitta to komai ma yana iya zama Allah ke nan, a bisa ruwayarsu. Tsarki ya tabbata ga Allah a bisa abin da suke siffanta shi da su.To, bari mu ji abin da fiyayyen halitta Mustafa (S.A.W) ya ce: Abu Huraira (R.A) y a rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewar: “Idan xaya bisa ukun dare ya yi saura, Allah yana sauka a kowane dare zuwa sama ta qasa, ya ce: wane ne zai roqeNi in amsa masa. Wane ne zai tambaye Ni, in amsa masa, wane ne zai nemi gafara in gafarta masa? Imam Ahmad ya rawaito wannan hadisi da jingine maikyau da kuma lafazi mai yawa.A wani hadisi Annabi (S.A.W) yana cewa: “Shin ba za ku amince mini ba. Alhali ni ne amintaccen wanda yake sama”. Bukhari da Muslim suka rawaito shi. Kuma wata rana Annabi (S.A.W) ya raba wani abu ga sahabbansa sai wani sahabi ya ce: “Wannan rabo ba a yi adalci ba”. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Wane ne zai yi adalci don ni ban yi adalci ba. Alhalin ni neamintaccen wanda yake sama?”A lokacin da Manzon Allah (S.A.W) ya yi Hajjin Bankwana, ranar Arfa ya yi huxuba, yana cewa: “Shin na isar muku da saqo?” sai sahabbai suka ce: “Na’am ka isar”. Sai Annabi ya xaga hannayensa guda biyu zuwa sama ya ce: “Allah ka shaida”. Kamar yadda bayaniya gabata wannan hujja ta hankali domin duk muna daga hannayenmu zuwa sama ne. wani lokaci har da fuskokinmu yayin yin addu’a. Domin a aikace a nan mun tabbatar Allah yaana sama a kan Al’arshinSa.A wani hadisi ingantacce Annabi (S.A.W) ya ce: “Ku jiqan waxanda suke qasa domin wanda yake sama ya jiqanku”. Wato idan kun tausaya wa bayin Allah da kuke tare da su. Allah wanda yake sama zai tsauaya muku.Wannan hadisi Tirmizi ya rawaito shi da isnadi mai kyau.
BAYANI A KAN BIKIN MAULIDI KASHI NA DAYA: (1)
from nuramuhd3 on 04/26/2015 09:38 PMtsakaninmu da ranar goma sha biyu ga watan Rabii’ul Awwal kwana 10 ne kacal, sannan kamar yadda aka sani ne cewa wannan rana ta 12/3/ ita ce ranar da wasu daga cikin masu ikirarin Musulunci ke bukin ranar haifuwar Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah cikinta saboda neman lada da falala a wurinAllah, duk kuwa da cewa rikon wannan rana a matsayin Idi bidi’a ce wurin dukkan Maluman Musulunci!Allah Sarki! Haka dai Shaidanyake badda mutane cikin mamaki wani lokaci! Allah Madaukakin Sarki yana cewa cikin Suratu Faatir aya ta 8:-(( ﺃﻓﻤﻦ ﺯﻳﻦ ﻟﻪ ﺳﻮﺀ ﻋﻤﻠﻪ ﻓﺮﺍﻩ ﺣﺴﻨﺎ ﻓﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻀﻞ ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻭﻳﻬﺪﻱ ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻓﻼ ﺗﺬﻫﺐ ﻧﻔﺴﻚ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺣﺴﺮﺍﺕ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻢ ﺑﻤﺎ ﻳﺼﻨﻌﻮﻥ )).Ma’ana: ((yanzu wanda aka kawata masa mummunan aikinsa har ya gan shi wani abu Mai kyau “yana daidai dawaninsa?” saboda haka lalle Allah yana batar da wanda yake so, kuma ya shiryar da wanda yake so, kada ranka ya halaka a kansu saboda bakin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sana’antawa)).Ni a nan, a bisa dogara da ayah ta 104 a cikin Suratu Ali Imrana inda Allah Madaukakin Sarki Ya ce:-(( ﻭﻟﺘﻜﻦ ﻣﻨﻜﻢ ﺃﻣﺔ ﻳﺪﻋﻮﻥ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻭﻳﺄﻣﺮﻭﻥ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ﻭﻳﻨﻬﻮﻥ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ ﺍﻟﻤﻔﻠﺤﻮﻥ )).Ma’ana: ((A samu wata al’umma daga cikinku da za ta yi kira zuwa ga alheri, sannan ta umurni da abin daShari’ah ta sani, kuma ta yi hani ga abin da Shari’ah batasani ba. To su wadannan Al’umma sune masu rabauta)). Da kuma dogara kan aya ta 78, da 79 cikin Suratul Maa’idah inda Allah Madaukaki ya yi maga a kan Banuu Isaraa’iil ya ce:-(( ﻟﻌﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﺍﺳﺮﺍﺋﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﻟﺴﺎﻥ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﻋﻴﺴﻰ ﺍﺑﻦ ﻣﺮﻳﻢ ﺫﻟﻚ ﺑﻤﺎ ﻋﺼﻮﺍ ﻭﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﺘﺪﻭﻥ . ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻻ ﻳﺘﻨﺎﻫﻮﻥﻋﻦ ﻣﻨﻜﺮ ﻓﻌﻠﻮﻩ ﻟﺒﺌﺲ ﻣﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻔﻌﻠﻮﻥ )).Ma’ana: ((An la’anci wadandasuka kafirta daga Banu Isaa’iil a bisa harshen Daawuuda da Isa Dan Maryam, saboda irin yadda suka yi sabo, suka kasance suna ketare iyaka. Suka kasance ba sa hana juna yin mummunan aikin da suke aikatawa. Wallahi abin da suka kasance suna aikatawa ya yi muni)). Intaha. Da kumadogara kan hadithin da Imam Muslim ya ruwaito hadithi na 49 inda Annabi mai tsira da amincin Allah yake cewa:-(( ﻣﻦ ﺭﺃﻯ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﻨﻜﺮﺍ ﻓﻠﻴﻐﻴﺮﻩ ﺑﻴﺪﻩ ﻓﺎﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻠﺴﺎﻧﻪ ﻓﺎﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻘﻠﺒﻪ ﻭﺫﻟﻚ ﺍﺿﻌﻒ ﺍﻻﻳﻤﺎﻥ )).Ma’ana: ((Wanda duk ya ga munkari daga cikinku sai ya jirkita shi da hannunsa, in kuma ba zai iya ba, sai ya jirkita shi da harshensa, in kuma ba zai iya ba sai ya jirkita shi da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin Imani)). Intaha. Da kuma dogara kan maganar SahabinAnnabi Abdullahi ‘Dan Mas’ud Allah ya kara masa yarda, wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh,dhah shafina 11 da littafin Ali’itisaam naImamush Shaatibii 1/107 inda ya ce:-(( ﺍﺗﺒﻌﻮﺍ ﻭﻻ ﺗﺒﺘﺪﻋﻮﺍ ﻓﻘﺪ ﻛﻔﻴﺘﻢ)).Ma’ana: ((Ku bi -abin da Annabi ya zo da shi- kada ku kirkiri bidi’ah, domin an gama muku kome -na addini-)). Dankuma dogara har yanzu a kan maganar shi Sahabi Abdullahi Dan Mas’uud wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh’dhah shafi na 11 da kuma Sunanud Daarami 1/68-69 a inda ya celokacin da ya wuce wani mai wa’azi a cikin masallaci yana ce wa mutane: ku yi Subhanallah kafa goma, ku yila’laha illalah kafa goma, sai ya ce da su:-(( ﻭﻳﺤﻜﻢ ﻳﺎ ﺃﻣﺔ ﻣﺤﻤﺪ ﻣﺎ ﺍﺳﺮﻉ ﻫﻠﻜﺘﻜﻢ ! ﻫﺆﻻﺀ ﺻﺤﺎﺑﺔ ﻧﺒﻴﻜﻢ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﺘﻮﺍﻓﺮﻭﻥ ﻭﻫﺬﻩ ﺛﻴﺎﺑﻪ ﻟﻢ ﺗﺒﻞ ﻭﺃﺗﻴﺘﻪ ﻟﻢ ﺗﻜﺴﺮ ﻭﺍﻟﺬﻱ ﻧﻔﺴﻲ ﺑﻴﺪﻩ ﺍﻧﻜﻢ ﻟﻌﻠﻰ ﻣﻠﺔ ﻫﻲ ﺃﻫﺪﻯ ﻣﻦ ﻣﻠﺔ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻭ ﻣﻔﺘﺘﺤﻮﺍ ﺑﺎﺏ ﺿﻼﻟﺔ . ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻳﺎ ﺃﺑﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﻣﺎ ﺍﺭﺩﻧﺎ ﺍﻻﺍﻟﺨﻴﺮ ﻗﺎﻝ ﻭﻛﻢ ﻣﺮﻳﺪ ﻟﻠﺨﻴﺮ ﻟﻦ ﻳﺼﻴﺒﻪ ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺍﻥ ﻗﻮﻣﺎ ﻳﻘﺮﺀﻭﻥ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻻ ﻳﺠﺎﻭﺯ ﺗﺮﺍﻗﻴﻬﻢ ﻭﺍﻳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﺍﺩﺭﻱ ﻟﻌﻞ ﺍﻛﺜﺮﻫﻢ ﻣﻨﻜﻢ ﺛﻢ ﻭﻟﻰ ﻋﻨﻬﻢ )).Ma’ana: ((kaitonku ya ku al’ummar Muhammad mamakin saurin halakarku! Wadannan Sahabban annabinku ne mai tsira da amincin Allah ga su nan da yawa, wadannan tufafinsa neba su gama yagewa ba, wadannan butocinsa ne ba su gama fashewa ba. Ina rantsuwa da Wanda raina yake hannunsa lalle ne ku ko dai kuna kan wani addini ne da ya fi addinin Muhammad shiriya ko kuwa ku masu bude kofar bata ne. Sai suka ce wallahi baban Abdurrahman babu abin da muke nufi sai alheri. Sai ya ce ai da yawa mai son alheri ba zai taba samun sa ba. Lalle Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya gaya mana cewa akwai wasu mutane da za su rika karantaAlkur’ani amma kuma ba zai wuce makogoronsu ba, ina rantsuwa da Allah watakila mafi yawansu daga cikinku suke. Daga nan sai ya juya yabar su)). Intaha. Da kuma dogara kan maganar babbanTaabi’ii Hasanul Basarii wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh’dhah, da littafin Alitisam na Shaatibii 1/111 inda ya ce: ((Mai yin bidi’ah ba zai ‘kara kokari cikin azuminsa na bidi’ah ba, ko sallarsa ta bidi’ah ba, face hakan ya nisantar da shi daga Allah)). Intaha.Dogara kan wadannan ayoyi da hadithai da maganganun Sahabbai da Taabi’ai da kuka ji su yanzu ne ya sa muke gargadin Al’ummar Musulmi,muke hana su rikon ranar haihuwar Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah a matsayin ranar Idi, muke musu gargadin rikon bukin maulidi a matsayin wani abu na addini da ake neman lada da shi a wurin Allah Madaukakin Sarki!Saboda abu ne tabbatacce wurin Maluman Musulunci cewa Annabi Mai tsira da amincin Allah bai yi bukin maulidi ba, Sahabbai ba su yibukin maulidi ba, Taabi’ai ba su yi bukin maulidi ba, Taabi’ut Taabi’in ba su yi bukin maulidi ba. Duk kuwa abin da ba zama addini ba a zamanin Sahabbai, da Taabi’ai, da Taabi’ut Taabi’in tare da kasancewar sababin yin sa a lokacin nasu’ da kuma ikon yin sa daga gare su yana nan, amma kuma babu Wanda ya yi shi daga cikinsu, to lalle wannan abin babu ta yadda za a yi ya zamanto addini karbabbe a wurin na bayansu har zuwa tashin Kiyama.Yan’uwa Musulmi! Lalle shi rikon ranar maulidi a matsayin Idi, da maida shi ranar buki, ba a fara yin shi ba cikin wannan Al’umma saicikin ‘karni na hudu na hijirarAnnabi Mai tsira da amincin Allah’ watau sai a cikin shekara ta dari uku da settin da biyu (362). Sannan mutumin da ya fara yin wannan buki na maulidi shi ne wani sarki dan Shi’ah Fadimiyyah Mai suna Almu’izzu li Dininl Lah a garinAlkahira’ kamar yadda yake rubuce cikin littattafan Musulunci da tarihi, da wasunsu, kuna iya duba wadannan littattafan:-ﺍﻟﻤﻮﺍﻋﻆ ﻭﺍﻻﻋﺘﺒﺎﺭ ﺑﺬﻛﺮ ﺍﻟﺨﻄﻂ ﻭﺍﻻﺛﺎﺭ ﻟﻠﻤﻘﺮﻳﺰﻱ ١/ ٤٩٠، ﻭﺻﺒﺢ ﺍﻷﻋﺸﻰ ﻓﻲ ﺻﻨﺎﻋﺔ ﺍﻹﻧﺸﺎﺀ ﻟﻠﻘﻠﻘﺸﻨﺪﻱ ٣/ ٤٩٨، ﻭﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻻﺣﺘﻔﺎﻝ ﺑﺎﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻟﻠﺴﻨﺪﻭﺑﻲ ﺹ٦٩، ﻭﺃﺣﺴﻦ ﺍﻟﻜﻼﻡ ﻓﻴﻤﺎ ﻳﺘﻌﻠﻖ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺒﺪﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﻟﻤﺤﻤﺪ ﺑﺨﻴﺖ ﺹ٤٤، ٤٥، ﻭﺍﻟﻤﺤﺎﺿﺮﺍﺕ ﺍﻟﻔﻜﺮﻳﺔ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻋﻠﻲ ﻓﻜﺮﻱ ﺹ٨٤، ﻭﺍﻹﺑﺪﺍﻉ ﻓﻲ ﻣﻀﺎﺭ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﻉ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻋﻠﻲ ﻣﺤﻔﻮﻅ ﺹ١٢٦، ﻭﺍﻟﺘﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻌﺒﺎﺳﻲ ﻭﺍﻟﻔﺎﻃﻤﻲ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﺍﺣﻤﺪ ﻣﺨﺘﺎﺭ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﻱ ﺹ٢٦١، ٢٦٢ .Almawaa’izu wa Litibaar na Maqriizii 1/490, da Subhul A’ashaa na Qalqashandii 3/498, da Taariikhu Lihtifaali Bil Maulidin Nabawii na Sanduubii shafi na 69, da Ahsanul Kalam fi ma yataallaqu bis Sunnati wal Bidi’ati minal Ahkam na Muhammad Bakhiit shafi na 44,45, da Almuhadharaatul Fikriyyah na Ali Fikrii shafi na84, da Al’ibdaa fi Madharri Libtidaa na Ali Mahfuuz shafina 126, da Taarikhul Abbaasiiwal Faatimii na Ahmad Mukhtaar Al’abbadii shafi na 261,262.MALUMAN MUSULUNCI DABAN DABAN SUN HANA YIN BIKIN MAULIDI:Yan’uwa Musulmi! Lalle da yawa daga cikin maluman Musulunci sun gargadi Al’umma sun hana su yin bukin maulidi da rikon shi a matsayin wata ibadah da za anemi lada wurin Allah da ita, kuma sun bayyanar da cewa yin bukin maulidi bidi’a ce kuma bata.Daga cikin wadannan malamai akwai manya manyan malumanmu na mazhabar Malikiyyah, kamar Ibnul Hajj wanda ya rasu a shekarar hijira ta 732 watau yau da rasuwarsa shekaru 702 ke nan da suka wuce, da kuma Umarul Faakihaanii wanda ya rasu a shekarar hijira ta 734 watau yau da mutuwarsa shekara 700 ke nan da suka wuce, da kuma Ibraahimush Shaatibii wandaya rasu a shekarar hijira ta 690 watau yau da rasuwarsa shekara 744 ke nan da suka wuce, da kuma uwa-uba Sheik Uthmanu Dan Fodiyo wanda ya rasu a shekarar hijira ta 1234 watau yau shekara 201 ke nan da rasuwarsa.Amma Sheik Ibnul Hajj ga abin da yake cewa cikin littafin Almudkhal 2/2, da 2/10-11
( ﻭﻣﻦ ﺟﻤﻠﺔ ﻣﺎ ﺍﺣﺪﺛﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉﻣﻊ ﺍﻋﺘﻘﺎﺩﻫﻢ ﺍﻥ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻛﺒﺮ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ ﻭﺍﻇﻬﺮ ﺍﻟﺸﻌﺎﺋﺮ ﻣﺎ ﻳﻔﻌﻠﻮﻧﻪ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻣﻦﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﻗﺪ ﺍﺣﺘﻮﻯ ﻋﻠﻰ ﺑﺪﻉ ﻭﻣﺤﺮﻣﺎﺕ ﺟﻤﻠﺔ ﻓﻤﻦ ﺫﻟﻚ ﺍﺳﺘﻌﻤﺎﻟﻬﻢ ﺍﻟﻤﻐﺎﻧﻲ ﻭﻣﻌﻬﻢ ﺁﻻﺕ ﺍﻟﻄﺮﺏ (( ﺍﻟﻰ ﺍﻥ ﻗﺎﻝ )) : ﻭﺍﻥ ﺧﻼ ﻣﻨﻪ ﻭﻋﻤﻞ ﻃﻌﺎﻣﺎ ﻓﻘﻂ ﻭﻧﻮﻯ ﺑﻪ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﺩﻋﺎ ﺍﻟﻴﻪ ﺍﻻﺧﻮﺍﻥ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﻛﻞ ﻣﺎ ﺗﻘﺪﻡ ﺫﻛﺮﻩ ﻓﻬﻮ ﺑﺪﻋﺔ ﺑﻨﻔﺲ ﻧﻴﺘﻪ ﻓﻘﻂﺇﺫ ﺍﻥ ﺫﻟﻚ ﺯﻳﺎﺩﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﻟﻴﺲﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﻤﺎﺿﻴﻦ ﻭﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﻞ ﺃﻭﺟﺐ ﻣﻦ ﺍﻥ ﻳﺰﻳﺪ ﻧﻴﺔ ﻣﺨﺎﻟﻔﺔ ﻟﻤﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻷﻧﻬﻢ ﺍﺷﺪ ﺍﺗﺒﺎﻋﺎ ﻟﺴﻨﺔ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻟﻪ ﻭﺳﻨﺘﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻟﻬﻢ ﻗﺪﻡ ﺍﻟﺴﺒﻖ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺒﺎﺩﺭﺓ ﺍﻟﻰ ﺫﻟﻚ ﻭﻟﻢ ﻳﻨﻘﻞ ﻋﻦ ﺍﺣﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﺍﻧﻪ ﻧﻮﻯ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﻧﺤﻦ ﻟﻬﻢ ﺗﺒﻊ ﻓﻴﺴﻌﻨﺎ ﻣﺎ ﻭﺳﻌﻬﻢ )).Ma’ana: ((Yana daga cikin jumlar abin da suka kirkira na bidi’o’i tare da akidar cewa hakan yana daga cikin manyan ibadodi, kuma yana daga cikin alamomin Musulunci mafi fita fili: abin nan da suke aikatawa cikin watan Rabii’ul Awwal na bukin maulidi. Shi dai maulidi ya tattari abubuwan haramun da yawa a dunkule,daga cikinsu akwai wake-wake da suke yi tare daKayan kade-kade …. To amma idan yin maulidi ya wofanta daga yin wake-wake tare da kayan kade-kade mai yin maulidin ya yi abinci kawai ya yi nufin maulidi da shi ya kira yan’uwa zuwa cin abincin, to, yin hakan ya zama bidi’ah saboda niyyar maulidin da ya yi, domin niyyar maulidin kari ne a cikin Addini ba ya kuma dagacikin ayyukan Salaf Magabataba, bin Magabata kuwa shi ne ya fi dacewa, kai shi ne ma wajibi da a ce mutum zai kara wani abu sabanin abin da suka kasance a kansa, domin su Magabata su ne suka fi kowa yin koyi da Manzon Allah, kuma su ne suka fi kowa girmama shi da girmama sunnarsa, kuma su suke da kafar rigaya wajen takawa zuwa ga abin da yake alheri ne, babu kuma mutumdaya da ya ciro yin niyyar maulidi daga dayansu, mu kuwa sauran Musulmi mabiya ne gare su, dukkan abin da ya wadatar da su na addini shi ne zai wadatar da mu)). Intaha.Sannan Imamul Faakihaanii ya ce cikin Risalarsa ta maulidi mai suna Almurid fil Kalaami alaa Hukmil Maulid:-(( ﻻ ﺍﻋﻠﻢ ﻟﻬﺬﺍ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﺻﻼ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﻭﻻ ﺳﻨﺔ ﻭﻻ ﻳﻨﻘﻞ ﻋﻤﻠﻪ ﻋﻦ ﺍﺣﺪ ﻣﻦ ﻋﻠﻤﺎﺀ ﺍﻻﻣﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻫﻢ ﺍﻟﻘﺪﻭﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻟﻤﺘﻤﺴﻜﻮﻥ ﺑﺂﺛﺎﺭ ﺍﻟﻤﺘﻘﺪﻣﻴﻦ ﺑﻞ ﻫﻮ ﺑﺪﻋﺔ ﺍﺣﺪﺛﻬﺎ ﺍﻟﺒﻄﺎﻟﻮﻥ ﻭﺷﻬﻮﺓ ﻧﻔﺲ ﺍﻋﺘﻨﻰ ﺑﻬﺎ ﺍﻻﻛﺎﻟﻮﻥ ﺑﺪﻟﻴﻞ ﺍﻧﺎ ﺍﺫﺍ ﺃﺩﺭﻧﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﺨﻤﺴﺔ ﻗﻠﻨﺎ ﺍﻣﺎ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻭﺍﺟﺒﺎ ﺍﻭ ﻣﻨﺪﻭﺑﺎ ﺍﻭ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﺍﻭ ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ ﺍﻭ ﻣﺤﺮﻣﺎ ﻭﻫﻮ ﻟﻴﺲ ﺑﻮﺍﺟﺐ ﺇﺟﻤﺎﻋﺎ ﻭﻻ ﺑﻤﻨﺪﻭﺏ ﻻﻥ ﺣﻘﻴﻘﺔ ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺏ ﻣﺎ ﻃﻠﺒﻪ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺫﻡ ﻋﻠﻰ ﺗﺮﻛﻪ ﻭﻫﺬﺍ ﻟﻢ ﻳﺄﺫﻥ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻭﻻ ﻓﻌﻠﻪ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻻ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻮﻥ ﻭﻻ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﺍﻟﻤﺘﺪﻳﻨﻮﻥ ﻓﻴﻤﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﻭﻫﺬﺍ ﺟﻮﺍﺑﻲ ﻋﻨﻪ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻋﻨﻪ ﺳﺌﻠﺖ ﻭﻻ ﺟﺎﺋﺰ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﻻﻥ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﻉ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻟﻴﺲ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﺑﺈﺟﻤﺎﻉ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻓﻠﻢ ﻳﺒﻖ ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ ﺍﻭ ﺣﺮﺍﻣﺎ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .Ma’ana: ((Ban san wata hujja da za ta halatta yin maulidi ba a cikin Alkur’ani da Sunnah, kuma ba a nakalto yin bukin maulidi koda daga mutum daya ba cikin maluman Al’umma wadanda su ne abin koyi a cikin Addini, kuma su ne ke riko da maganganun magabata, kai, abin da dai yake ciki shi ne: shi dai maulidi wata biri’ah ce da marasa aikin yi suka kirkira kuma sha’awar son rai ce da masu cin dukiyar mutane cikin ‘karya suka runguma, saboda shi dai bukin maulidi idan muka shimfida shi a kan hukunce-hukuncin nan guda biyar sai mu ce: ko dai ya zama wajibi,ko kuwa ya zama mustahabbi, ko kuwa ya zama mubaahi, ko kuwa ya zama makruuhi, ko kuwa ya zama haraamun, to in mun yihakan za mu ga cewa shi dai ba wajibi ba ne bisa Ijmaa’in Malamai, shi kuwa ba mustahabbi ba ne domin abin da ake nufi da mustahabbi shi ne abin da Shari’ah ta ce a yi ba tare da an zargi Wanda ya ki yi ba, shi kuwa maulidi Shari’ah ba ta ce a yi shi ba, kuma ni a sanina Sahabbai, da Taabi’ai, da malamai masu riko da Addini ba su yi shi ba, wannan shi ne jawabina a gaban Allah a kan bukin maulidi in har aka tambaye ni. Kuma ba zai halatta ba a ce Maulidi ya zama mubaahi saboda kirkiran wani abu cikin addini ba zai zama mubaahi ba a bisa Ijmaa’in Musulmi, saboda haka babu abin da ya rage face maulidi ya zama makruuhi ko kuwa haramun)). Intaha.Sannan Imamush Shaatibii ya ce -a lokacin da yake yin bayanin ma’anar bidi’ah- cikin littafinsa mai suna Alitisam 1/50,53
( ﻋﺒﺎﺭﺓ ﻋﻦ ﻃﺮﻳﻘﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻣﺨﺘﺮﻋﺔ ﺗﻀﺎﻫﻲ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻳﻘﺼﺪ ﺑﺎﻟﺴﻠﻮﻙ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺍﻟﻤﺒﺎﻟﻐﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻌﺒﺪ ﻟﻠﻪ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ …. ﻳﻌﻨﻲ ﺍﻧﻬﺎ ﺗﺸﺎﺑﻪ ﺍﻟﻄﺮﻳﻘﺔ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺍﻥ ﺗﻜﻮﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﺔ ﻛﺬﻟﻚ ﺑﻞ ﻫﻲ ﻣﻀﺎﺩﺓ ﻟﻬﺎ ﻣﻦ ﺃﻭﺟﻪ ﻣﺘﻌﺪﺩﺓ …. ﻣﻨﻬﺎ ﺍﻟﺘﺰﺍﻡ ﺍﻟﻜﻴﻔﻴﺎﺕﻭﺍﻟﻬﻴﺌﺎﺕ ﺍﻟﻤﻌﻴﻨﺔ ﻛﺎﻟﺬﻛﺮ ﺑﻬﻴﺌﺔ ﺍﻻﺟﺘﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺻﻮﺕ ﻭﺍﺣﺪ ﻭﺍﺗﺨﺎﺫ ﻳﻮﻡ ﻭﻻﺩﺓ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﺍ ﻭﻣﺎ ﺃﺷﺒﻪ ﺫﻟﻚ )). ﺍﻧﺘﻬﻰ .Ma’ana: ((Bidi’ah wata kirkirarriyar hanya ce cikin addini mai kama da addinin gaskiya ana nufin kaiwa matuka matuka cikin bautar Allah da yin ta .., ina nufin itabidi’ah tana kama da hanyar Shari’ah ba tare da ta kasance hanyar Shari’ah ta hakika ba, kai a gaskiya ma tana karo ne da hanyar Shari’ah ta fiskoki da yawa … Daga cikinsu akwai lazimtar wasu irin siffofi ayyanannu, kamar zikirin da ake yi a bisa tsarin haduwa a kan sauti daya’ da kuma rikon ranar haihuwar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a matsayin idi, da abin da yakeKama da haka)). Intaha.Sannan Shehu Uthmanu Dan Fodiyo ya ce cikin littafinsa mai suna Ihyaa’us Sunnah wa Iqmaadul Bid’ah shafi na 104
( ﻓﺎﻥ ﻗﻠﺖ ﻣﺎ ﺣﻜﻢ ﻣﺎ ﻳﻔﻌﻞ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻭ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺴﺎﺑﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻣﻦ ﺍﺟﺘﻤﺎﻉ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻟﻠﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﻄﻌﺎﻡ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﻌﻤﻠﻮﻧﻪ ﻟﺬﻟﻚ؟ ﻗﻠﺖ: ﺍﻧﻪ ﺑﺪﻋﺔ ﻣﻜﺮﻭﻫﺔ ﺍﻥ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻛﻞ ﻣﻌﺼﻴﺔ . ﻭﻗﻴﻞ : ﺍﻥ ﺍﻟﺼﻮﺍﺏ ﺍﻥ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻟﺸﺮﻳﻒ ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺍﻟﺤﺴﻨﺔ ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺑﺔ ﺍﺫﺍ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻣﻌﺼﻴﺔ .ﻭﺃﻣﺎﻣﺎ ﻳﻌﺘﺎﺩﻩ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺰﻣﺎﻥﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﺧﺘﻼﻁ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻤﻌﺎﺫ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﺍﺣﺪ ﺑﺠﻮﺍﺯﻩ )). ﺍﻧﺘﻬﻰ .Ma’ana: ((Idan ka ce: Mene ne hukuncin abin da mutane suke yi a cikin watan Rabii’ul Awwal a ranar maulidi ko kuwa a ranar bakwai ga maulidi na taruwar jama’a saboda yin zikiri da cin abincin da aka yi tanadinsa saboda hakan? Sai in ce: Wannan bidi’ah ce makruuhiyah in yin maulidin ya wofinta daga dukkan sabon Allah. Amma kuma wasu sun ce: Abin da yake daidai shi ne shi bukin maulidin Annabi yana daga cikin bidi’o’i masu kyau matukar dai ya wofinta daga ko wane sabon Allah. To amma abin da mutane suka Saba yin shi a maulidi a wannan zamani na cakuda tsakanin maza da mata a’uuzu billahi da wani mutumzai ce halal ne)). Intaha.Wannan shi ne abin da malumanmu na mazhabar Malikiyyah suka fada game da bikin maulidi.Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah wanda ya rasu a shekarar hijira ta 728 watau shekaru 706 ke nan da suka wuce shi ya yi maganar maulidi ya kuma tabbatar da cewa maulidi bidi’ah ce, ya rubuta cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqiim 2/123-124
( ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻣﺎ ﻳﺤﺪﺛﻪ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻣﺎ ﻣﻀﺎﻫﺎﺓ ﻟﻠﻨﺼﺎﺭﻯ ﻓﻲ ﻣﻴﻼﺩ ﻋﻴﺴﻰ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺍﻣﺎ ﻣﺤﺒﺔ ﻟﻠﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻗﺪ ﻳﺜﻴﺒﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻤﺤﺒﺔ ﻭﺍﻻﺟﺘﻬﺎﺩ ﻻ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻣﻦ ﺍﺗﺨﺎﺫ ﻣﻮﻟﺪ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﺍ ﻣﻊ ﺍﺧﺘﻼﻑ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻣﻮﻟﺪﻩ ﻓﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﻟﻢ ﻳﻔﻌﻠﻪ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻣﻊ ﻗﻴﺎﻡ ﺍﻟﻤﻘﺘﻀﻲﻟﻪ ﻭﻋﺪﻡ ﺍﻟﻤﺎﻧﻊ ﻣﻨﻪ ﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﺧﻴﺮﺍ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﺧﻴﺮﺍ ﻣﺤﻀﺎ ﺍﻭ ﺭﺍﺟﺤﺎ ﻟﻜﺎﻥ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ ﺍﺣﻖ ﺑﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺎﻧﻬﻢ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﺍﺷﺪ ﻣﺤﺒﺔ ﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻟﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﺍﺣﺮﺹ ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻛﻤﺎﻝ ﻣﺤﺒﺘﻪ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﻪ ﻓﻲ ﻣﺘﺎﺑﻌﺘﻪ ﻭﻃﺎﻋﺘﻪ ﻭﺍﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺇﺣﻴﺎﺀ ﺳﻨﺘﻪ ﺑﺎﻃﻨﺎ ﻭﻇﺎﻫﺮﺍ ﻭﻧﺸﺮ ﻣﺎ ﺑﻌﺚ . ﺑﻪ ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ﺑﺎﻟﻘﻠﺐ ﻭﺍﻟﻴﺪ ﻭﺍﻟﻠﺴﺎﻥ ﻓﺎﻥ ﻫﺬﻩ ﻃﺮﻳﻘﺔ ﺍﻟﺴﺎﺑﻘﻴﻦ ﺍﻷﻭﻟﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻳﻦ ﻭﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﺗﺒﻌﻮﻫﻢ ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ )). ﺍﻧﺘﻬﻰ .Ma’ana: ((Haka nan abin da sashin mutane ke kirkira ko dai saboda koyi da Kiristoci cikin bukin Kirsimeti’ ko kuwasaboda son Annabi mai tsira da amincin Allah da girmama shi, zai yiwu Allah ya ba su lada a kan nuna kokari da soyayya’ amma ba zai ba su lada a kan bidi’o’in rikon maulidin Annabi mai tsira da amincin Allah a matsayin idi ba duk da yake ma masu tarihi sun yi sabania kan wace rana ce da wani wata ne aka haife shi! Shi dai bukin maulidi babu wani daga cikin magabata da ya yi shi duk kuwa da cewa dukkan dalilan da ake bayarwa na yin bikin a yanzu akwai su a wancan lokacin ma, kuma babu wani abu da zai hana su yin bukin inda yinshi alheri ne. Lallai ne da yin bikin maulidi tsantsar alheri ne to da Salaf Magabata su suka fi cancantar yin sa a kanmu, saboda sun fi mu son Manzon Allah mai tsira da amincin Allah da girmama shi, kuma sun fi kowa son aikata alheri. Lalle cikar soyayya da girmamawaga Annabi tana cikin bin shi ne da yi masa da’ah da bin umurnin shi, da raya sunnar shi ciki da waje, da yada abinda aka aiko da shi, da yin jihadi da zuciya, da hannu, da harshe a kan hakan wannan ita ce hanyar Magabata na farko daga cikinMuhajirai da Ansarawa da wadanda suka bi su da kyautayi)). Intaha.Yan’uwa Musulmi! Wannan shi ne matsayin bukin maulidi daga bakunan wadannan gagga-gaggan maluman Musulunci, tare ma kuma da cewa Maluman tarihi da siiirah sun yi sabanigame da ranar haihuwar shi Annabi mai tsira da amincin Allah, a inda wasu suka ce:1- An haife shi ne a ran biyu ga watan Rabii’ul Awwal.2- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran takwas ga watan Rabii’ul Awwal.3- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma ga watan Rabii’ul Awwal.4- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha biyumga watan Rabii’ul Awwal.5- wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha bakwai ga watan Rabii’ul Awwal.6- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran ashrin ga watan Rabii’ul Awwal.7- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha biyu ga watan Ramadhan.Domin ganin wannan sabanin sai ku dubi littafin Taariikhul Islam na Imamuz Zahbiy a Juz’in Siyrah shafi na25-27, da kuma littafin Albidaayatu wan Nihaayatu na Alhaafiz Ibnu Katheer 2/662.Yan’uwa Musulmi! ‘Kauli daidai har bakwai a kan ranar haihuwar Annabi mai tsira da amincin Allah babu kuma wani wanda ya isa ya ce: wannan ‘kauli shi ne hakikanin gaskiya wancan kaulin kuma ba gaskiya ba ne, saboda abu ne da ya farukafin zuwan Musulunci kumabayan shi Musulunci ya zo bai tabbatar da ranar haihuwar ba ta hanyar wahayi saboda rashin muhimmancin yin hakan a cikin Addini.Wannan shi ne kashi na farko game da bayananmu a kan bukin maulidi, kashi biyuna tafe in sha Allahu Ta’ala, kuma zai yi bayani ne game da shubuhohin da yan bidi’ah ke ambatawa domin tabbatar da bidi’ar maulidi.Allah Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya ba mu ikon bin ta, Ya kuma nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon‘kin ta.
HAKIKANIN ‘KAUNAR ANNABI (SAW)
from nuramuhd3 on 04/26/2015 09:34 PMHAKIKANIN ‘KAUNAR ANNABI (SAW)Bismillahi, dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ta’alah, tsira da aminci su qara tabbata ga Annabinmu Muhammadu s.a.w da IyalengidanSa da SahabbanSa.Son Manzon Allah (S.A.W) wajibi ne, duk wanda ba ya son Manzon Allah (S.A.W) to kafiri ne ba musulmi ba ne, saboda haka ya wajaba a kandukkan musulmi ya rika jin son Annabi ( S.AW ) a cikin zuciyarsa a ko yaushe, ba waisai a wani lokaci ba.Kasancewar yanzu muna cikin watan maulidi, watan da aka haifi fiyayyen halitta manzon Allah (S.A.W) ya zama wajibi a kan malamai na hakika, su bayyanawa mutane hakikanin ma’anar son Manzon Allah (S.A.W), domin a yau an wayi gari a na ganin yin maulidi shi ne kauna da so ga Annabi (S.A.W), har ma a na ganin wanda duk baya yin Maulidi to ba ya kaunar Manzon Allah (S.A.W), wanda wannanmaganar kuskure ce mai girma, saboda son Manzon Allah (S.A.W) ba a baki yake ba, a’a abu ne da tushensa a zuciya ne, idan babu shi a zuciya to fadin baki ba zai amfanar ba, don haka da mutum zai kwana yana maimaitawa da bakinsa cewa: yana son Annabi (S.A.W) amma babu wannan kauna da son a zuciyarsa da babu ruwan Allah da wannan abin da yake fada.Sannan kuma babu wani musulmi na gaskiya wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira da za a ce baya son Annabi (S.A.W) sai dai in ba musulmin ba ne, saboda haka jifan wani bangare dagacikin musulmi da cewa ba sa son Annabi (S.A.W) saboda kawai ba sa yin Maulidi babban kuskure ne, domin kafirta su ne, kafirta musulmikuwa – wanda bai aikata abinkafircin ba – laifi ne babba a wurin Allah.Saboda haka malamai magabata sun riga sun yi mana bayanin hakikanin ma’anar son ga Annabi (S.A.W), sun bayyana mana alamomi da suke nuna cewa mutum yana kaunar Manzon Allah (S.A.W), wadanda su yakamata mu maida hankali wajen lazimtar karantarwar su da kokarin aikata su, don kaunarmu da sonmu ga fiyayyen halitta ta qara yawa da danko, kuma ta qara gasgata. Don haka, ga abubuwan da malamai uka fada a kan sune alamomin son Annabi s.a.w :1. Alamata ta farko : Imani da Shi (S.A.W) da yarda cewaAllah ne ya aiko Shi, kuma Shi mai gaskiya ne abin gasgatawa. Duk wanda bai yi imani da Manzon Allah (S.A.W) to wannan ba shi da rabo a duniya da lahira, kuma ya tabe, ko da yana son Annabi (S.A.W), don wani dalili na daban, kamar ma su son Annabi (S.A.W) don kasantuwarSa Yana ‘dan uwansu, ko don Yana ‘dan su, irin son da Abu Dalib ya yi masa, ya so Shi ne saboda ‘dan ‘dan uwansa ne, wannanyasa ya ba Shi kariya, ya kula da Shi, ya hana kowa ya tava Shi, amma da yake bai yi imani da Shi ba, sai ga shi wannan son bai amfane shi ba, kamar yadda yake a cikin hadisin da Imamul Ahmad da Bukhari da Muslim da Tirmizi da Nasa’i da Hakim da sauransu suka rawaito cewa : “Lokacin da Abu Dalib ya zo barin duniya, Manzon Allah (S.A.W) Ya zo ya same shi a kwance, Ya ce masa, ya baffana, ka ce “La’ilaha illal Lahu” kalma ce da Zan kare ka da ita a gaban Allah” sai Abu Jahli da Abdullahi bin Umayya suka ce masa : “Yanzu za ka bar addinin kakanka Abdulmuddalib”. Manzon Allah (S.A.W) bai gushe ba Yana maimaita masa wannan maganar, su kuma su na maimaita masa cewa kada ya bar addinin kakansa, karshe ya ce shi yana kan addinin Abdulmuddalib, ya qi ya ce la’ilaha illal lahu. Daga nan sai Manzon Allah (S.A.W) Ya tashi Yana cewa “Wallahi zan nema maka gafara matuqar ba a hana ba” sai Allah ya saukar da Ayah ya ce, “Baya hallata ga Annabi da waxanda suka yi imani su nema wa mushirikai gafara ko da makusantansu ne, bayan ya bayyana gare su cewa (waxannan mushirakan) ma’abota wuta ne” (Tauba : 113).Wannan hadisi ya tabbatar mana da cewa babban matakin farko ga mutum shi ne ya yi imani da Manzon Allah (S.A.W).2. Alama ta biyu : Biyayya gare Shi (S.A.W) cikin dukkanabin da Ya yi umarni da shi, da koyi da Sunnarsa, da aikata ta a ko yaushe a ko ina, ba tare da ja baya ba. Allah Madaukakin Sarki a cikin Al-Qur’ani a wurare da dama Ya yi da maganar yi waManzon Allah (S.A.W) ‘da’a da biyayya, saboda wannan ita ce babbar Alamar da ke nuna qauna da so ga fiyayyen halitta (S.A.W). daga cikin Ayoyin da suka yi maganar yi wa Manzon Allah(S.A.W) biyayya Ayah ta 132 aAli-Imran, da Ayah ta 59 a Suratun Nisa’i, da Ayaha ta 92 a Suratul Ma’ida, da Ayah ta 1 a Suratul Anfal, da dai sauransu.Imam Alkali Iyad babban malamin nan mai littafin as-Shifa’ ya yi Fasali guda a cikin wannan littafin na shi mai albarka, ya ce (Fasali cikin Alamomin Son Annabi S.A.W) sai ya fara da fasalin da cewa : ((Ka sani duk wanda yake son wani abu to zai fifita shi, ya kuma fifita dace wa da shi, in ko bai yi haka ba, to ba son gaskiya yake masa ba, kurum yana da’awa ne (cewa yana son shi) domin mai gaskiya wajen son Annabi (S.A.W) shine wanda alamun son suke bayyana a wurinsa Alama ta farko kuwa ita ce Koyi da Shi,da aiki da Sunnarsa, da kwatanta maganganunSa da ayyukanSa, da kwatanta yin abubuwan da Ya umarta, da nisantar abin da Ya hana da ladabtuwa da ladubbanSa, a lokacin tsanani da sauki, da nishadi da kunci)) (ash-Shifa :J 2, sh 24).3. Alamata uku : Gasgata shi (S.A.W) a cikin duk abin da Yaba da labari. Yana cikin alamun kafirci mutum ya qaryata Manzon Allah (S.A.W) cikin wani abin da Ya ba da labari cewa ya faru, ko zai faru, saboda Manzon Allah (S.A.W) ba Ya magana akan son zuciyarsa, duk abin da Ya fada wahayi daga wajen Allah Madaukakin Sarki. Babu qauna ga Annabi (S.A.W) ga mutumin da za a ce Manzon Allah (S.A.W) Ya ce, shi kuma ya ce, “Kai ban yarda da wannan ba” ko ya kore maganar Annabin (S.A.W) da hankalinsa.4. Alama ta hudu : Fifita Manzon Allah (S.A.W) a kan kowa, saboda Allah Madaukakin sarki ya fifita Annabi (S.A.W) akan dukkan halittu, shi ne shugaban Annabawa, cikamakinsu. Manzon Allah (S.A.W) yana cewa : ((Xayanku ba zai zama mumina ba, har sai na zama ya fi sona, a kan mahaifinsa, da ‘ya ‘yansa, da dukkan mutane gaba xaya)) (Bukhari ne ya rawaito shi).Don haka babu qaunar Annabi (S.A.W) ga mutumin da zai fifita son zuciyarsa, ko dukiyarsa, ko qabilarsa, a kan abin da Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi, ya qin bin umarnin Manzon Allah (S.A.W) don ya kare waxancan abubuwa. Ina qaunar Annabi (S.A.W) ga mutumin da ya kasa daina shaye-shayen kayan maye, alhali ya san Manzon Allah (S.A.W) ya ce : ((Dukkan Abu mai sa maye giya ne, dukkan giya kuwa haramun ce)).Ina qauna ga Manzon Allah ga mutum da ya kasa barin son zuciyarsa wajen neman abincinsa, wajen barin qarya a kasuwanci, da algus alhali ya san Manzon Allah ya hana. Ina qaunar Manzon Allah ga mutumin da yake sukan wani saboda ya yi abinda manzon Allah (S.A.W) ya ce a yi, wajen sallarsa, da sa tufafinsa, da sauran al’amuran ibadunsa. Allah yakare mu (Ameen)5. Alama ta biyar : Yi wa Manzon Allah (S.A.W) salati, shi da iyalan gidansa, kamar yadda Manzon Allah ya koyar. Manzon Allah (S.A.W) yana cewa : “Ku yawaita yi min salati ranar Juma’a da darenta” (Baihaqi ne ya rawaito shi).Imam Ibnul qayyim yana cewa, “Manzon Allah (S.A.W) shi ne shugaban halitta. Ranar Juma’a kuwa ita ce shugabannin ranaku, don haka yin salati ga Manzon Allah (S.A.W) a wannan ranaryana da fifiko akan sauran ranaku….”. Duba (Zadul Ma’ad) (J1/Sh 364).6. Alama ta Shida : Yaxa sunnar Annabi (S.A.W) da ba ta kariya daga dukkan wani abu da zai gurvata ta, ko ya canza ta. Kamar yadda sahabban Annabi (S.A.W) suka zama ba sa ganin an yi wani abu da ya sava wa abin da Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi face sai sun hana.Imam Abdur-Razzaq Assan’ani ya rawaito cewa : Sa’id bin Musayyib (xaya daga cikin Tabi’ai) ya ga wani mutum yana ta yin sallah bayan asuba,sai ya hana shi, ya ce “ya daina” sai wannan mutumin ya ce : “Yanzu Allahzai yi min azaba ne don ina yin sallah” sai Sa’id ya ce masa, “a’a (ba zai maka azaba don kana yin sallah ba)sai dai zai azabta ka akan yin abu savanin Sunnah”. Hakan nan Abu Musal Al-ash’ariy yafaxa wa Abdullahi xan Mas’ud cewa, ya ga wasu mutane sun kewaye juna, babbansu yanaba su umarnin cewa “a yi tasbihi adadi kaza” sai su kama yi, suna qirgawa da tsakuwowin da suke hannunsu, sai ya sake ba su wani umarnin, sai su yi. Nan da nan Abdullahi xan Mas’udya zabura ya ce musu “Ya al’ummar Muhammad (S.A.W) wa ya fi ku saurin halaka, ga akushinsa nan bai fashe ba, ga tufafinsa nan ba su lalace ba, amma har ga shi kun zo da wani abu wanda shi da shabbansa ba su aikata shi ba. To ku sani nine Abdullahi xan Mas’ud sahabin Annabi (S.A.W)” sai waxannan mutane suka ce masa ” Ya kai baban Abdur-Rahman wallahi alheri muke nufi (da wannan aiki), sai Abdullahi xan Mas’ud ya ce : “Mutune nawa ne suka yi nufin alheri amma ba su same shi”.Wannan yana nuna mana irin yadda magabata suke kare sunnar Annabi (S.A.W), haka kuma ya wajaba ga duk wani mai qaunar Manzon Allah (S.A.W) da ya yi :1. Alama ta Bakwai : Kare Manzon Allah (S.A.W) da mutuncinsa da martabarsa.A ga mutum duk lokacin da aka tava mutuncin Annabi (S.A.W) ya fito ya kare da dukabin da zai iya, ko dai hannunsa, ko bakinsa, ko kuma ya qi abin a zuciyarsa idan ba zai iya da baki ko da hannu ba, amma duk wanda aka tava mutuncin Annabi (S.A.W) aka vata shi ya yi shiru, bai nuna bacin ransa ba, to wannan ba mai qaunarManzon Allah ba ne (S.A.W). Yana cikin kare martabar Annabi (S.A.W) kare addininsa, da bada jini da tsoka don ganin ya tabbata, kuma ana yin sa kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi.2. Alama ta takwas : Kare Iyalan gidan Annabi (S.A.W) da Sahabbansa.Duk wanda zai ci mutuncin wani daga iyalan gidan Annabi (S.A.W) waxanda suka yi imani da shi, suka gasgata shi, ko ya tava mutuncin wata daga cikin matansa, ko ‘ya ‘yayansa, ko ya zagi wani daga cikin sahabbansa, ya ce musu munafukai, ko kuma ya raba tsakanin sahabban Annabi (S.A.W) da iyalan gidansa, ya ce, suna gaba da juna, sun ci amanarsa a kan iyalan gidansa, to haqiqanin gaskiya wannan ba mai qaunar Annabi ba ne, qauna ta gaskiya, domin kuwa ya rushe dukkan wani abu da Manzon Allah (S.A.W) ya ginashi a cikin wannan al’umma, ya nuna tarbiyar da ya yi wa mabiyansa a tsawon shekaruashirin da uku bai ci nasara ba! Allah ya kare mu daga vata.3. Alama ta tara : Bibiyar Sunnarsa (S.A.W) da kokarin saninta, don aikatawa da yaxa ta a cikin al’umma, duk wanda yake son Manzon Allah so na haqiqa za a ga kullum damuwarsa ita ce, Ya ya Manzon Allah (S.A.W) ya yikaza, don ni ma in yi irinsa.4. Alama ta goma : Jin daxi da nutsuwa da duk hukuncin da Manzon Allah (S.A.W) ya yanke, mutum zai bi ba tare da jin qunci ba, ko wata damuwa. Babu qauna da so ga Annabi (S.A.W) ga mutumin da za a faxa masa hukuncin Manzon Allah (S.A.W) a kan wani aiki da yake yi, ya ji haushi ko qunci,ko ya juya baya, ya ce, shi ba zai bi wannan hukunci ba, yinhakan alamun Munafinci ne da kafirci. Allah Maxaukakin Sarki ya kare mu.‘Dan uwa waxannan su ne Manya – Manyan alamun son Manzon Allah (S.A.W), bawai faxa da baki ba kawai, batare da aiki ba. duk wanda yasiffatu da waxannan alamomi to shi ne haqiqanin mai son Annabi (S.A.W) saboda shi ne ya yi qauna daso irin wanda sahabbai suka yi Annabi (S.A.W). Amma wanda babu waxannan alamu a tare da shi, ko kumasun qaranta a tare da shi, to acikin soyayyarsa ga Annabi (S.A.W) akwai tasgaro, sai ya yi qoqari ya gyara, mu sani sahabban Annabi (S.A.W) da waxanda suka zo bayansu, da sauran malaman shiriya aiki suka yi tuquru, wajen bayyana qaunarsu ga Manzon Allah (S.A.W) ba wai bukukuwa suka tsaya suna yi ba, amma ba su damu da gyara ayyukansu ba. Allah Maxaukakin Sarki Ina roqonka da Sunayenka kyawawa da siffofinka Maxaukaka ka qara mana son Annabi (S.A.W) a maganganunmu da ayyukanmu.
BAYANI A KAN BIKIN MAULIDI KASHI NA BIYU (ii)SHUBUHOHIN DA MASU BIKIN MAULIDI KE KAFA HUJJA DA SU A KAN BUKIN MAULIDI DA SUKE YI:
from nuramuhd3 on 04/26/2015 09:29 PMBAYANI A KAN BIKIN MAULIDI KASHI NA BIYU (ii)SHUBUHOHIN DA MASU BIKIN MAULIDI KE KAFA HUJJA DA SU A KAN BUKIN MAULIDI DA SUKE YI: Yan’uwa Musulmi! Akwai shubuhohin da masu bikin maulidi ke ambatawa a gaban wadanda suka raina wa hankali da karatu a matsayin hujjojin da suke wajabta yin bukin maulidi ko suke halatta shi, saboda hakaIna sha Allah Ta’ala za mu ambaci uku daga cikinsu a wannan rubutu namu (kashi na biyu ii) sannan mu ba da amsarsu mu yi musu raddi, saboda burin da muke da shina tsarkake addinin Musulunci daga wannan bidi’ah mai kama da bidi’ar Kirsimeti wacce Kiristoci ke yi cikin ko wace shekara.****************************SHUBUHA TA FARKO:Shubuha ta farko: Suka ce: Allah ne da kansa Ya yi umurni da yin bikin maulidi cikin Suratu Yunus aya ta 58 a inda ya ce:-{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ }.Ma’ana: {Ka ce: Ku yi farin ciki da falalar Allah da rahamarSa shi ne mafi alheridaga abin da suke tarawa}.Sai masu bidi’ar maulidi sukace: Annabi shi ne falalar Allah da rahamarSa, Allah kuwa Ya ce a yi farin ciki da falalarSa da kuma rahamarSa, farin cikin kuwa yana nufin shirya bikin maulidinsa ne ahi Annabi mai tsira da amincin Allah, ke nan shirya bikin maulidi ko wace shekara bin wani umurni ne na musamman Wanda ya fito daga Allah Madaukakin Sarki, rashin binwannan umurni kuwa lalle saba wa Shi Allah Madaukakin Sarki ne!!!Amsa a kan wannan shubuhata yan bidi’ar maulidi tana darassa da yawa:-Na farko: sai a ce da su: Fassara wannan ayar da cewa tana umurni ne da yin bukin maulidi fassara ce da take Kama da fassarar Baatiniyyah da gulaatus suufiyyah da suke yi wa wasunassoshin Alkur’ani mai girma, kamar yadda suka fassara ayah ta 25 cikin Suratu Nuuhin inda Allah Yake magana game da mutanen Annabi Nuhu Ya ce:-{ ﻣﻤﺎ ﺧﻄﻴﺌﺎﺗﻬﻢ ﺃﻏﺮﻗﻮﺍ ﻓﺄﺩﺧﻠﻮﺍ ﻧﺎﺭﺍ ﻓﻠﻢ ﻳﺠﺪﻭﺍ ﻟﻬﻢ ﻣﻦ ﺩﻭﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻧﺼﺎﺭﺍ }.Ma’ana: {Saboda laifukansu na ganganci aka nitsar da su (cikin ruwa) sannan aka sanya su a Wuta. Saboda haka ba su sama wa kansu wanin Allah a matsayin Mai taimako ba}.Sai suka ce: ma’anar ayar ita ce: Allah Yana nufin cewa abin nan da suka yi wa Annabi Nuhu na saba wa umurnin da Allah ya aiko shi da shi shi ne ya Kai su ga yin nitso cikin tekunan sanin Allah! Watau dai abin nan da suka yi na saba wa Annabi Nuhu babu wani zunubi a cikinsa kamar yadda wasu ketsammani!!Suka kuma fassara inda AllahYa ce cikin Suratul Israa’i aya ta 23:-{ ﻭﻗﻀﻰ ﺭﺑﻚ ﺍﻻ ﺗﻌﺒﺪﻭﺍ ﺍﻻ ﺇﻳﺎﻩ }.Ma’ana: {UbangijinKa Ya hukunta cewa kada ku bauta wa kowa sai Shi}.Sai suka ce: Ma’anar ayar ita ce: “Ubangijinka Ya riga ya kaddara muku cewa ba za ku yi wata bauta ba face Allahn ne dai kuka bautawa!saboda haka babu wani abu a duniyan da za ku bautawa face a hakikanin lamari Allah ne Shi kadanSa kuka bautawa!!Suka kuma fassara inda Allahya ce cikin Suratul Hijri aya ta99 :-{ ﻭﺍﻋﺒﺪ ﺭﺑﻚ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﺗﻴﻚ ﺍﻟﻴﻘﻴﻦ }.Ma’ana: {Kuma ka bauta wa Ubangijinka har mutuwa ta zo maka}. Sai suka ce: ma’anarsa shi ne: shi Dan Adam ana umurtansa da yin ibada ne har zuwa lokacin daya kai matsayin Yakini da sanin Allah, da zarar ya kai wannan matsayi ayyukan ibada sun fadi ke nan a Kansa!!Reshe na biyu: Sai a ce da su:Wani malami ne cikin maluman tafsiiri daga magabata Salafus Salih ya fassara wannan ayar da irin wannan fassara taku ta cewa:Ana nufin yin bukin maulidi ne da wannan ayah? Lalle muna tabbatar wa masu karatun wannan rubutu namu cewa: har abada yan bidi’ar maulidi ba za su iya kawo koda malamin tafsiiri daya ba daga cikin Salafus Salih da ya fassara wannan ayar da cewa tana nufin umurni ne da yin bukin maulidi.Rashe na uku: Sai a ce wa masu bidi’ar maulidi: In dai har wannan ayar tana nufin yin bukin maulidi ne to kuwa lazimin hakan shi ne: Sahabbai da sauran shugabannin Al’ummah kamar su Abu Hanifah, da Mali, da Shafi’ii da Ahmad, da sauransu dukkansu ke nan sun nuna kiyayya da rashin kauna ga Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah, sannan dukkansu ke nan sun saba wa umurnin Allah da ya zo cikin wannan aya ta 58 da ta zo cikin Suratu Yunus, domin har suka gama rayuwarsu babu wani daga cikinsu da ya taba yin bukin maulidi! Duk kuwa wanda ya ce:Sahabbai, da Taabi’ai da sauran shugabannin Al’ummah ba sa kaunar Manzon Allah ko ba sa girmama shi, ba sa bin umurnin Allah da ya zo cikin Alkur’ani na girmama shi to lalle wannan ya bace bata bayyananniya! Lazimin wannan kuwa shi ne: Yan bikin maulidi su ne batattu saboda lazimin maganarsu ta tabbatar da cewa Sahabban Manzon Allah da Taabi’ai, da Taabi’utttaabi’ina da sauran Sugabannin Al’ummah batattu ne, sabodaba su yi aiki da wannan Aya ba:-{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ }.Reshe na hudu: Sai a ce da Yan maulidi: Dukkan abin da bai zama nuna soyayya ba nega Manzon Allah a zamanin Shabbai da Taabi’ai da sauran Shugabanni kamar Imam Malik, da Abu Hanifah,da Shaa’i’ii, da Ahmad, to ba zai zama nuna soyayya ga Manzon Allah ba a wannan zamani namu.Idan kuma wani daga cikin yan bukin maulidi ya fidda jahilcinsa a fili ya ce: Ai Suyuutii ya halatta yin bikin maulidi! Sai a ce da shi: Ai shi Suyuutii ba ya daga cikin wadanda ake kira Magabata cikin Musulunci, a’a yana cikin jerin yan baya ne, domin ya mutu ne a shekara ta 911 na hijira watau yau shekara 523 ke nan da suka wuce. Kuma shi Suyuutii a wurin Malamai mutum ne dayake kama da mai tara kirarecikin dare, ya kan dauki kirare sannan ya kan dauki macizai da kunamu, saboda wannan idan har ya halatta bidi’ar bukin maulidi ba waniabin mamaki ba ne a gurin Malamai, domin ya yi ma abin da ya fi hakan muni da ban mamaki, saboda Mai littafin Rimaahu Hizbir Rahiim ya ce a cikin wannan littafi nasa wanda aka buga tare da littafin Jawaahirul Ma’aa’nii 1/199 ya ce shi Suyuutii ya ce cikin littafinsa mai suna :-ﺗﻨﻮﻳﺮ ﺍﻟﺤﻠﻚ ﻓﻲ ﺇﻣﻜﺎﻥ ﺭﺅﻳﺔ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻭﺍﻟﻤﻠﻚ“Ya ga Annabi kuma ya yi taro da shi a farke har sau saba’in da wani abu”! Mai irin wannan magana mara tushe don ya ce bikin maulidihalal ne mene abin mamaki a cikin maganarsa? Allah Ya tsare daga fadawa cikin ko wace irin halaka. Ameen.SHUBUHA TA BIYU:Shubuha ta biyu suka ce: Dukwata ni’ima da Allah Ya yi wa mutum, to dole ne ya gode aw Allah a kanta, saboda lokacin da Annabi ya dawo Madinah ya ga Yahudawa suna azumi a ranar goma ga watan Muharram sai shi Annabi mai tsira da amincin Allah ya tambaye su ya ce: Me ya sa kuke azumin wannan rana? Sai suka ce masa: Wannan rana ce da Allah Ya tsirar da Annabi Musa tare da jama’arsa, kuma Ya halakar da Fir’auna tare da mutanensa cikin teku, shi ya sa Annabi Musa yake azumin wannan rana saboda gode wa Allah mu ma shi ya sa muke yin azuminsa, sai Annabi mai tsira da amincin Allah Ya ce: Mun fi ku cancantar yin abin da Annabi Musa ya yi, saboda haka ya yi azumin wannan ranar kuma ya umurci Musulmi da su yi azuminsa. A nan muna ganinbabu wata ni’ima da ta kai haihuwar Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah, kuma ko shakka babu wannan ni’ima za ta wajabta mana gode aw Allah, wannan kuwa shi ya samuke yin bukin maulidi saboda nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki.Amsa a kan wannan shubuhatasu sai a ce da su: Lalle gaskiya ne ni’imomin Allah suna wajabta godiyar Allah a kan bayinSa, to amma hakikani’ima mafi girma a cikin Musulunci ita ce:Ni’imar ba wa Annabi mai tsira da amincin Allah Manzanci, ba. Wai ni’imar haihuwar sa ba, domin Alkur’ani mai girma bai yi nuni da ishara zuwa haihuwarsa koda sau daya ba, to amma ya yi nuni da ishara zuwa ga manzancinsa ba sau daya ba ba sau biyu ba! Allahl Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratu Aa’li Imraan Aya ta 164:-{ ﻟﻘﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺇﺫ ﺑﻌﺚ ﻓﻴﻬﻢ ﺭﺳﻮﻻ ﻣﻦ ﺍﻧﻔﺴﻬﻢ ﻳﺘﻠﻮ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺁﻳﺎﺗﻪ ﻭﻳﺰﻛﻴﻬﻢ ﻭﻳﻌﻠﻤﻬﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺤﻜﻤﺔ }.Ma’ana: {Hakika Allah Ya yi babbar falala ga muminai domin Ya aika da Manzo daga ainihinsu yana karanta musu ayoyinSa Yana tsarkake su yana karantar da su Littafi da Hikima}. A nan Allah bai ce: domin an haifi wani Manzo daga cikinsu ba, a’a sai Ya ce: Domin an aiko wani Manzo. Wannan shi ne halin da za ku tarar game da ko wane Manzo daga cikin manzannin Allah Madaukakin Sarki, watau abin himmantuwa game da shi shi ne aiko shi ba wai ranar haihuwarsa ba, kamar dai yadda Allah Madaukakin Sarki ya ce cikin Suratul Bakara Aya ta 213:-{ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻣﺔ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻓﺒﻌﺚ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻣﺒﺸﺮﻳﻦ ﻭﻣﻨﺬﺭﻳﻦ ﻭﺍﻧﺰﻝ ﻣﻌﻬﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻟﻴﺤﻜﻢ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﻓﻴﻪ }.Ma’ana: {A da mutane sun kasance al’umm ce guda daya, sai Allah Ya aiko Annabawa suna masu bishara suna masu gargadi, kuma Ya saukar da
TAMBAYA:Akaramukallahu Allah ya kara basira, kuma ina nemanshawara cewa ni ina son na yi karatun addini, amma da na fara sai na ji kamar raina ba ya s
from nuramuhd3 on 04/12/2015 01:05 PMAMSA:To dan’uwa, akwai abubuwanda suke taimakawa wajan samun ilimin addini, ga muhimmai daga cikinsu :1. Tsarkake niyya- duk lokacin da ka tsarkake niyyarka wajan neman ilimi, to Allah zai taimakeka.2. Yin aiki da abinda mutum ya karanta- domin yin aiki da ilmi yana daga cikin abubuwan da suke taimakawa wurin rike ilmi dakuma kiyaye shi.3. Neman taimakon Allah – saboda a na so mai neman ilmi ya dinga tunawa cewa Allah Shi ne MASANI mai sanar da kowa, don haka ya dinga neman taimako a wurinsa yana rokonsa ya buda masa basira.4. Nisantar zunubai, saboda ilmin addini haske ne, kuma hasken Allah ba ya bawa maisabo.5. Yawan maimaitawa, dominmaimaita ilmi na daga cikin abubuwan da suke taimakawa wajan samun ilimi da tabbatarsa a zukata .6. Jure wahala da kuma hakuri , saboda neman ilimi ba ya yiwuwa sai da wahala kuma duk wanda ba zai iya jure wahala ba, zai yi wuya ya iya neman ilmi yadda ya kamata.7. . Farawa da abin da ya dace da dalibi, domin a na sodalibi ya fara da littafin da yadace da shi wurin neman ilmi, saboda idan ya fara da littafin da ya wuce matakin karatunsa, ba zai fahimce ba.Ina tabbatar maka mutukar ka rike wadannan to Allah zaitaimakeka, ka samu ilimi cikin kwanciyar hankali.ALLAH NE MAFI SANI
TAMBAYA:Akaramukallahu Allah ya kara basira, kuma ina nemanshawara cewa ni ina son na yi karatun addini, amma da na fara sai na ji kamar raina ba ya s
from nuramuhd3 on 04/12/2015 12:57 PMAMSA:To dan’uwa, akwai abubuwanda suke taimakawa wajan samun ilimin addini, ga muhimmai daga cikinsu :1. Tsarkake niyya- duk lokacin da ka tsarkake niyyarka wajan neman ilimi, to Allah zai taimakeka.2. Yin aiki da abinda mutum ya karanta- domin yin aiki da ilmi yana daga cikin abubuwan da suke taimakawa wurin rike ilmi dakuma kiyaye shi.3. Neman taimakon Allah – saboda a na so mai neman ilmi ya dinga tunawa cewa Allah Shi ne MASANI mai sanar da kowa, don haka ya dinga neman taimako a wurinsa yana rokonsa ya buda masa basira.4. Nisantar zunubai, saboda ilmin addini haske ne, kuma hasken Allah ba ya bawa maisabo.5. Yawan maimaitawa, dominmaimaita ilmi na daga cikin abubuwan da suke taimakawa wajan samun ilimi da tabbatarsa a zukata .6. Jure wahala da kuma hakuri , saboda neman ilimi ba ya yiwuwa sai da wahala kuma duk wanda ba zai iya jure wahala ba, zai yi wuya ya iya neman ilmi yadda ya kamata.7. . Farawa da abin da ya dace da dalibi, domin a na sodalibi ya fara da littafin da yadace da shi wurin neman ilmi, saboda idan ya fara da littafin da ya wuce matakin karatunsa, ba zai fahimce ba.Ina tabbatar maka mutukar ka rike wadannan to Allah zaitaimakeka, ka samu ilimi cikin kwanciyar hankali.ALLAH NE MAFI SANI
Tambaya : Assalamu alaikummalam, shin don Allah ina gaskiyar lamarin da ake cewa: Umar yana kuka wataran kuma sai a ga yana dariya, har aka tambaye sh
from nuramuhd3 on 04/12/2015 12:55 PMAmsa : To dan’uwa tabbas wannan maganar ta yadu a wajan masu wa’azi da masu huduba akan minbarai, saidai ba ta da tushe, kuma karya ce, saboda abubuwa kamar haka : 1. Masana tarihi sun tabbatar da cewa : matar Umar R.A ta farko a rayuwarsa, ita ce Zainab ‘yar Maz’un wacce ta Haifa masa Hafsan da Annabi s.a.w. ya aura, don haka Hafsa ita ce babbar ‘yarsa, kuma da ita ake masa alkunya, don haka idan bai rufe babba ba daga cikin ‘ya’yansa, ta yaya zai bunne wacce ta zo daga baya?, tare da cewa : ita kan ta Hafsan an haife ta ne kafin a aiko Annabi s.aw. da shekarabiyar, ka ga kenan abin da ta riska na jahiiliyya ba shi da yawa . 2. Wacce ake cewa Umar ya bunneta da ranta, gaba daya littatafan tarihi ba su fadi labarinta ba, ko su kirga ta a cikin ‘ya’yansa ba. 3. Sannan kabilar Adiy wacceUmar ya fito daga cikinta ba su shahara da binne ‘ya’ya mata ba, a zamanin jahiliyya.4. Dogon bincike ya nuna cewa : babu wannan kissa kwata-kwata a cikin littattafanAhlussunah, asalinta daga littatafan ‘yan shi’a aka cirota,don haka su ne suka kirkire ta, dama kuma sun saba yin kage ga sahabban Annabi s.aw.Allah ne mafi sani .Don neman Karin bayani duba : Dirasa nakdiyya fi shaksiyati Umar 1/111. دراسة نقدية في شخصيية عمر بن الخطاب وسياسته الإدارية 1/111-112
TAMBAYA:Assalamu alaikum, Dan Allahmalam a fitar da ni cikin duhu game da abin da yake damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin malami ai mata naganin ciwon
from nuramuhd3 on 04/12/2015 12:52 PMTo ‘dan uwa, tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, sai dai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur’ani, wasu malaman sun yi bayani cewa: a na iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-Kursiyyu da Kuliya da Ikhlas da Falaki da Nasi da kuma Ayah ta : 117 zuwa ta 122, na Suratul A’araf, sai kuma Ayahta : 79-81 a Suratu Yunus, sannan sai a hada da Ayah ta: 65-70 a Suratu Dhaha, za’a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai, sannan ayi wanka da shi.Amma bai halatta ka taimakama ta ba, wajan bada wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba’a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah. Ya wajaba ka yi ma ta nasiha cikin hikima, ka sanar da ita cewa : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana cewa, “Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba’in” kamar yaddaMuslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2230.Ka ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari’a tayarda da ita, a wani hadisin kuma yana cewa, “Duk wanda ya je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to tabbas ya kafurce da abinda Annabi Muhammad ya zo da shi”, kamar yadda ya zo a Sunanu-Abi-Dawud hadisi mai lamba ta :3904, kuma Albani ya ingantashi .INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA.Allah Ne mafi sani.
WASU TAMBAYOYI NAKE ROKON Malam daya taimakamin da amsoshinsu in Allah yasa malam yasansu.
from nuramuhd3 on 04/12/2015 12:51 PMWASU TAMBAYOYI NAKE ROKON Malam daya taimakamin da amsoshinsu in Allah yasa malam yasansu.1.SHIN MALAM Wai a kwai wasu abubuwa uku da ake somata tafi mijin da zata aura dasu,sannan shima akwai abu guda uku da’akeso yafita dasu?,sannan akwai wadanda sukayi musharaka akansu,DAFATAN MALAM YASANSU KUMA ZA’A TAIMAKAMIN DA Su.NAGODEAmsa : To dan’unwa masana ilimin zamantakewar aure suna cewa, ana so mace ta fi mijinta da abubuwa uku : ta fi shi a kyau, ta fi shi kanananshekaru, ta fi son shi, sama da yadda yake sonta . Ana somiji ya fi matarsa da abubuwa uku : ya fi ta kudi, ya fi ta ilimi, ya fi ta jarunta Ana so su hadu a abubuwa uku : ya zama akwai yaran dayake hada su, ya zama addininsu daya, ya zama dukkansu suna son tarbiyya. Idan aka samu wadannan uku-ukun, to za’a samu jin dadin aure.

Reply