Latest posts

First Page  |  «  |  1  ...  5  |  6  |  7  |  8  |  9  ...  24  |  »  |  Last Search found 237 matches:


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

guziri

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:47 AM

Tarbiyya1بسم الله الرحمن الرحيموالصلاة والسلام على عبدالله ورسوله نبينا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين(A). YADDA AKE YIN MURAJA’AR ALQUR’ANIAlqur’ani yana bukatar muraja’a kuma idan mutum ba ya yin muraja’a zai iyamanta duk abin da ya haddace, saboda shi al-qur’ani kamar rakumi ne idan ka rike akalarsa sai ya bika, idan kuma ka sake shi sai ya gudu, don haka idan mutum ya haddace alqur’ani yana da babban aiki akansa na yawan maimaita abin da ya haddace, kamata ya yi ka dinga hada hadda da muraja’a a lokaci daya don kar kana haddace wani wuri na baya yana rushewa, daga cikin hanyoyin muraja’a akwai:– Idan zai yiwu ka kasa al-qur-ani gida uku, kashin farko daga Suratu Annas zuwa Ankabut, kashi na biyu daga Suratul Kasas zuwa Yunus, kashi na uku daga Suratu Attaubah zuwa Baqara.– Idan ka haddace izu ashirin, kar ka cigaba sai ka yi kamar wata kana maimaitashi, wannan zai taimaka wajan karfafa haddarka.– Idan ka haddace izu arba’in, kar ka cigaba sai ka yi kamar wata biyukana maimaita shi, wannan zai sa haddarka, ta yi kwari.– Idan ka haddace al-qur’ani gaba daya ka yi kokari ka matsawa kanka, wajan yin bitar wani bangare na al-qur’ani kullum, kamar izu biyu kulum ko makamancin haka, duk kuma ranar da ba ka yi ba, ka yi kokari ka rama.(Duba : khuduwatun ilassa’adah 195-196)(B). KA’IDOJIN HADDACE AL-QUR’ANI– Ya wajaba Dalibi ya rinka yin hadda a wajan malami saboda ya dinga gyara masa.– Ka da Dalibi ya dinga haddace abu mai yawa, musamman farkon fara haddarsa, saboda wannan zai jawo ya yi hadda mara karfi, ya kamata ya dinga yi daidai yadda zai iya yin muraja’a sosai, don ya inganta haddarsa.– Idan dalibi zai fara hadda ya fara daga suratu Annas saboda ta fi sauki.– Ya rinka yin hadda da al-qur’ani iri daya, saboda zaisa shi ya dinga tuna gurin da kowacce aya ta ke, da kuma tuna inda kowanne shafi ya ke karewa.(Duba : khuduwatun ilassa’adah 200-201)(C). ADALCI YA KASU KASHI BIYU :1. Adalci wajan mu’amala da Allah 2. Adalci wajan mu’amala da bayinSa.– Adalci wajan mu’amala da Allah shi ne :1. ka bauta maSa yadda ya kamata.2. Ka da ka ce za ka yi jayayyada Shi a cikin siffofin da ya kebanta da su.3. Ka gode maSa shi kadai a cikin ni’imar da ya baka.4. Kada ka yi amfani da ni’imarSa wajan saba masa.5. Kada ka yiwa kowa cikakkiyar godiya sai Shi.6. Ka da ka bautawa kowa saiShi .– Adalci wajan mu’amala da bayinSa shi ne :1. Yin mu’amala da su da abin da kake so su yi maka mu’amala da shi.2. Ajjiye kowa a matsayinsa, ka sanya babba daga cikin musulmai ya zama babanka, matsakaicinsu kuma ya zamadan’uwanka, karaminsu kuma ya zama kamar ‘Da a wajanka, don haka sai ka girmama babanka, ka karrama dan’uwanka, ka ji tausayin danka.YI NAZARI DON KA GA GWARGWADON ADALCINKA.(D). ABUBUWA GUDA GOMA SUNA KARIYA DAGA SHAIDANIbnul kayyim yana cewa : bawa yana samun kariya daga Shaidan da abubuwa guda goma :1. Neman tsari da shi kamar yadda Allah ya yi umarni da hakan a al’qur’ani.2. Karanta kula’uzai guda biyu.3. Karanta ayatul kursiyyu4. Karanta suratul bakara.5. Karanta ayoyi biyun karshena suratul bakara.6. Karanta ayoyi uku na farkon suratul Gafir.7. Karanta Laa’ilaha illallahu wadahu laa shariikalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa alaa kulli sha’in kadeer, sau dari.8. Yawan ambaton Allah9. Yin alwala lokacin sallah.10. Barin kallo da zancen da ba shi da amfani, da abincin da ya wuce bukata, da barin cakuduwa da mutane, sai gwargwadon bukata.(E). HAKURI YA KASU KASHI UKU1. Hakuri akan biyayya ga Allah, sau da yawa mutum zai ji wahala da nauyi wajan aikata wasu daga cikin abubuwan da Allah ya umarce shi da su, kamar yin alwala da kuma sallar asuba a lokacin tsananin sanyi, da fitowa sallar azahar a lokacinda ake tsananin zafi, dole sai ya yi hakuri da juriya kafin yaiya aikatawa.2. Hakuri wajan barin abin daAllah ya hana, sau da yawa zuciyar mutum za ta ji tana sha’awar abin da Allah ya haramta, duk wanda ya yi hakuri ya bar abin da Allah ya hana, to zai ba shi mafi alkairinsa a Lahira, wanda yabar giyar duniya mai wari Allah zai shayar da shi giyar lahira mai kamshi, wanda ya bar matan banza masu kwailin aduniya Allah zai aura masa matan aljanna tsarkaka, kyawawa masu manyan ido, wadanda wani namiji kafin shi bai taba taba su ba, idan ‘yan aljanna su ka shiga aljanna mala’iku za su shiga wajansu, su ce musu ” Amincin Allah ya tabbata a gare ku, saboda hakurin da kuka yi (akan abin da Allah yaumarta da barin abin da Allah ya hana) ” Suratu Arra’ad aya ta 243. Hakuri akan musifu da bala’o’in da Allah ya jarabceka da su, duniya gida ne na jarrabawa, duk lokacin da farin ciki ya sameka sai kagodewa Allah ka samu lada, idan bakin ciki ya sameka ka yi hakuri saikasamu lada, dole ne mutum ya yi imani da kaddara komai dacinta, kuma imaninsa ba zai cika basai ya yarda da ita. Allah yana jarrabar mutum gwargwadon imaninsa, Annabi tsira da amincinAllahsu tabbata a gare shi yana cewa “wadanda aka fi jarrabasune Annabawa, sai kuma wadanda suke bin su wajan nagarta, haka dai zuwa wadanda suke bi” Tirmizi da Ibnu Hibban.Ka zama mai hakuri akan duka wadannan guda ukun, Allah yana cewa : “Ana cikawa masu hakuri ladansu ba tare da kidayawa ba” Suratu Azzumar aya ta 10(F). GINSHIKAN GODEWA NI’IMAR ALLAH GUDA BIYAR NEIbnul kayyim yana cewa : godiya ga Allah ta ginu ne akan ginshikai guda biyar :1. Kaskantar da kai ga wandaya yi maka abin,wato Allah.2. Nuna soyayya gare shi.3. Yin furuci da ni’imar da ya yi maka.4. Yabonsa da ni’imar da ya yi maka.5. Kar ka yi amfani da ni’imarta sa wajan abin da yake ki.Yin furuci da ni’imar Allah yana daga cikin abubuwan da su ke kara yawan ni’imomin da Allah ya yi maka, wani daga cikin magabata yana cewa : “Godewa ni’ima yana kare maka ni’imar da kake ciki, sannan kuma yana farauto ni’imar da ba ka cikinta”. Dukkan wani abu da kake amfana da shi a rayuwarka ta yau da kullum wani bangare ne na na’imomin Allah, Allah yana cewa : “Idanda za ku kirga ni’imomin Allah, da ba ku iya kidaye su ba” (Suratul Ibrahim aya ta 34).Shin ka kan yi amfani da gabobinka wajan abin da Allah yake so, ko kuma ka kan saba masa da su, an tambayi JUNAID (daya daga cikin magabata) cewa me akenufi da godewa ni’imar Allah sai ya ce shi ne : “RASHIN YIN AMFANI DA NI’IMARSA WAJAN ABIN DA YA HANA”Abin da yake taimakawa wajan gode ni’imar Allah shi ne kallon na kasa da kai a wajan abin duniya, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: “KU DIN GA KALLON NA KASA DA KU, DOMIN HAKANSHI ZAI SA KU KI WULAKANTA NI’IMAR DA ALLAH YA YI MUKU” Tirmizi ne ya rawaito.(MADARIJUSSALIKIN 2244)(G). MUNANAN MUSIBUN DA ZUNUBAI SUKE JAWOWA (1)Allah madaukaki yana cewa : “Babu wata musiba da za ta same ku, face sai ta kasance daga abin da hannunku ya aikata ne” suratu Asshuraa aya ta 30. Zunubai suna jawobala’oi da yawa, wadanda suke cutar da zuciya da jiki, aDuniya da Lahira, ba wanda ya san adadinsu sai Allah, daga cikinsu akwai :1. Haramta samun arziki, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : “Bawa ana haramta masa arziki saboda zunubin da ya aikata”Ibnu majah ne ya rawaito kuma Albani ya inganta shi.2. Haramtawa mutum samunilimi Abdullahi dan Mas’ud yana cewa: (Ina saran mutum zai iya manta ilimin da ya sani saboda zunubin da yake aikatawa) kuma Imamu Shafi’i yana cewa:ﺷﻜﻮﺕ ﺇﻟﻰ ﻭﻛﻴﻊ ﺳﻮﺀ ﺣﻔﻈﻲ** ﻓﺄﺭﺷﺪﻧﻲ ﺇﻟﻰ ﺗﺮﻙ ﺍﻟﻤﻌﺎﺻﻲﻭﻗﺎﻝ ﺍﻋﻠـﻢ ﺑﺄﻥ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻧـﻮﺭ ** ﻭﻧﻮﺭﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﺆﺗﺎﻩ ﻋﺎﺻــﻲMa’ana:Na kai karar munin haddata wurin waki’u (malaminsa ne)# sai ya shiryar da ni zuwa barin zunubai.Kuma yace ka sani ilimin haske ne # hasken Allah (s.w.t.) ba’a bawa mai sabo1. Haramtawa mutum aikata alkairi, saboda zunubi kamarabinci ne mai cuta a ciki, wanda idan ka ci guda daya, to zai iya hanaka cin wani mai dadi, Al-fadlu bn iyadh yana cewa :”Duk sanda ka ga ba ka iya tsayuwar dare to katabbatar zunubai ne su ka dabaibaye ka”(H). MUNANAN MUSIBUN DA ZUNUBAI SUKE JAWOWA (2)1. Fuskantar wahalhalu iri iri a cikin rayuwa, da cijewar abubuwan da suke gabansa, daya daga cikin magabata yana cewa ” Na kan sabawa Allah, sai inga danshin sabona halayyar abin hawana da matata” kuma Ibnu seerin yana cewa lokacin da wani bakin ciki ya dame shi “Wannan bakin cikin ya sameni ne, saboda wani zunubi dana aikata shekaru arba’in da su ka wuce”Allah madaukaki yana cewa : “Babu wata musiba da za ta same ku, face sai ta kasance daga abin da hannunku ya aikata ne” (Suratul Zukruf ayata 30).Zunubai suna jawo bala’oi dayawa, wadanda suke cutar dazuciya da jiki, a Duniya da Lahira, ba wanda ya san adadinsu sai Allah. Saboda ba za’a dora maka wani ya dinga cutar da kai ba, sai idan akwai wani zunubi da kaaikata, ka san zunubin ko ba ka san shi ba, wani daga cikin magabata ya hadu da wani mutum sai ya aibanta shi, sai ya ce masa : jira ni nashiga gida na fito, sai ya shiga gida yayi sallah ya tubazuwa ga Allah, bayan ya fito sai mutumin ya ce masa: me ka yi, sai yace : na tuba zuwa ga Allahn da ya dora ka akaina.2. Samun duhu a cikin zuciya,Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa ” Idan mumini ya yi zunubi, ana yin bakin digo a zuciyarsa, in ya tuba ya nemi gafara sai a cire idan yacigaba sai wannan bakin ya karu” Ibnu majah ne ya rawaito kuma Albani ya kyautata shi.

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

jagoran wa azi 12 to end

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:33 AM

JAGORAN MAI WA’AZI١٢Wannan ya sa za mu ga Annabi yana da }as}antar da kai a cikin al’amuransa gaba]aya kamar yaddaAnas ]an Malik yake cewa Baiwa za ta iya kama hannunsa ta tafi da shi duk inda ta ke so ( saboda}as}antarda kansa) (51)Saidai wannan ba yana nufin ya zama sololo kowa ya taka shi, yadda yake so ba dole neya dinga karemutuncinsa.10 – AMFANI DA LAFAZI MAI KYAUKa yi }o}ari wajan yin amfani da lafazi mai kyau a cikin da’awarka kamar yadda wanimawa}i yake cewa :يا بني إن البر شيء هين وجه طليق و لسان لينMa’ana:Ya kai [ana kyautatawa abu ne mai sau}i saboda sakin fuska ne da tattausar magana.Kuma kamar yadda ka sani Allah ya yi umarni da yin magana mai kyau kamar yaddaAllah yake cewa:(وُقوُلوا للناسِ  حسناً )Ma’ana :Ku gayawa mutane magana mai kyau. (52)Idan kana yiwa mutane magana da sanyi za su yi amfani da wa’azinka kuma susaurare ka, shi ya sa za mu galokacin da Balaraban }auye ya yi fitsari a masallaci sahabbai su ka yi masa tsawa Annabi ya ce ku }yaleshi, lokacin da ya gama sai ya ce da shi wa]annan masallatai ba’a gina su saboda }azantar mutane ba, an ginasu ne kawai don sallah da ambaton Allah da karatun alqur’ani . (53)Kuma Annabi yana cewa (Allah yana son tausasawa a cikin komai kuma yana bayarwa ta hanyar tausayiabin da ba ya bayarwa ta hanyar tsanani)Sannan Annabi yana cewa ( Idan ka yi kyakykyawar kalma(ga musulmi ) akwai ladan sada}a) , (54)To inakuma ga wanda yayi wa’azi da kyakyawar kalma ?11- YA DOGARA DA KANSA, KAR YA DOGARA DA WANIKada ka zamar da wa’azi hanyar cin abincinka, Annabi yana cewa:عن أبي هريرة قال سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول لأن يغدو أحدكم فيحطب على ظهره فيتصدق به ويستغني به من الناسخير له من أن يسأل رجلا أعطاه أو منعه ذلك فإن اليد العليا أفضل من اليد السفلى وابدأ بمن تعولMa’ana:Annabi  ya ke cewa [ayanku ya yi sammako ya yo ice a bayansa, ya yi sada}a da shi ya kuma wadatudaga mutane , shi ya fi masa da ya tambayi wani mutum ya bashi ko ya hana shi, hannun da yake bayarwa yafi hannun da yake amsa, ka fara da wanda ka ke ]aukar nauyi.(55)Kuma ya tabbata cewa Annabi Dawud yana }ira yanacin abinci ta hanyarta, hakananAnnabi ya kasance kafin ya zama Annabi yana kiwo ana ba shi ku]i (56) AnnabiAdam ya kasance manomi ne, Annabi I dris kuma ma]inki ne , Annabi Nuhu kuma ya yi kafitanci .Hakanan Umar ]an Kha]ab yakasance yanayin kasuwanci, sannan Zubair ]an Awwam]aya daga cikinwa]anda aka yi musu bisharada aljanna ya kasance yana yin ]inki , sannan Amru BN Ass ya kasancemahauci ne, sannan Abubakar Assidi} ya kasance yana saida kaya, hakanan Usman ]an Affan da kuma٥١ Bukhari ne ya rawaito(٥٢) suratul Ba}ara aya ta 83٥٣ an yi bayanin wanda ya rawito shi a baya(٥٤ ) Bukhari da muslim(٥٥ ) Muslim ne ya rawaito٥٦ Bukhari ne ya rawaito, hakanan Mubarakfurii ya yi bayani akan haks, a cikin Rahi}il maktum .JAGORAN MAI WA’AZI١٣[alha, sannan Abu-sufyan ya kasance yana saida mai ne, sannan Utbah ]an Abi wa}}asya kasance yanayin kafinta ne don ya sami ku]in kashewa, wa]annan gaba ]aya dana gaya maka sahaban Annabi  donhaka sai kayi }o}ari wajan yinkoyi da su. (57)sannan manyan malaman wannan Al’umar suna da sana’o’in da suke yi suna cinabinci, misali Babban malaminnan wato JALALUDDIN ASSUYU[I ya kasance yanayin gadin labirare, sannan Abu Hanifita ya kasance yanasiyar da kaya, hakananmuhamad BN Sirin, (58)sannan Imamu Annawawi ]aya daga cikin malaman hadisi ya kasance yanazama a shagon Babansa, hakanan sheak Nasirudden Albani ya kasance yana gyaran agogoyana samun na kashewa ta hanyarsa.Misalan wa]annan suna da yawa, saidai wa]annan da mu ka kawo sun isa mu gane,cewa malamai ba a zaune su ke ba suna cin abinci da karatunsu.Daga lokacin da ka dogara gamutane wa’azinka zai yi raunisaboda ba za ka iya gayamusu gaskiya yadda ya kamata ba, kamar yadda Hausawa suke cewa idan baki ya cisai ido ya ji kunya, kuma Annabi yana cewa hannun da yake bayarwa ya fi hannunda yake amsa, (59) Shaikulislam Ibn Taimiya yana cewa:استغن عمن شئت تكن نظيره واحتج إلى من شئتتكن أسيره وأعط من شئتتكن أميرهMa’ana:Ka wadatu daga wanda ka so za ka zama daidai da shi, ka yi bu}ata ga wanda ka so zaka zama ribataccensa, ka kuma bawa wanda ka keso zaka zama shugabansa.sharhiAbin da malam yake nufi shi ne duk lokacin da mutum yake baka za ka zama sai yaddaya ce da kai, idan kuma ba kabu}ata a wajansa to za ka zama daidai da shi, idan kumakana yiwa mutum kyauta to za ka zama shugabansa sai abin da ka ce shi zai yi.Kuma ka yi }o}ari wajan yiwa mutane kyauta indai kana da hali kamar yadda ake cewaan halicci zukata akan son wanda ya kyautata mata kuma Annabi yana cewa ku rin}ayiwa juna kyauta za ku so juna (60).Wannan ~angangaren yana da mahimmanci sosai sai a kula da shi domin yana da tasiriwajan cigaban da’awa da kuma samun nasararta.12- YA ZAMA YANA DA KYAKYKYAWAR ALAKA TSAKANINSADA ALLAHYa zama dole ka zama kana da kyakykyawar dangantaka tsakaninnka da Allah maigirma, wannan yana kasancewa ta hanyar aikata aiyuka na gari kamar nafiloli da azumida sada}a da yawaita zikiri kamar yadda Allah ya cewa Haruna da Musa (kada ku rin}ayanke ambatona) (61)Saboda dagewa wajan aikata aiyuka masu kyau yana taimakawa wajan samun nasara a cikin wa’azi , sabodahaskensu zai rin}a bayyana a fuskarsa kuma za’a rin}a jin haka a cikin zancensa, za kuma su }ara masakwarjini , wannan sai ya sa mutane su rin}a girmama shisu kuma yi amfani da abin dayake fa]a . (62)Idan mu ka duba za muga Annabi shi ne ya fi cacanta mu yi koyi da shi a wannan~angaran Al}ali Iyadhyana cewa :(٥٧ ) idan kana son cikakken bayani akan haka sai ka dubaAL-MAARIF NA IBN { UTAIBAH daga shafi na 575 zuwa 577(٥٨ ) yana daga cikin Tabiai ya mutu 110٥٩ Bukhari da muslim da Baiha}i٦٠ Baiha}i ne ya rawaito(61) duba [ahah aya ta 42٦٢ ) Duba USUSU ADDA’WAHNA MUHAMMAD SAYYID WAKILJAGORAN MAI WA’AZI١٤( Biyayyarsa ga Ubangiji da kuma tsoransa gare shi ya kasance gwargwadon saninsa da ubangijinsa, yakasance yana yin sallah har}afafuwansa su ka kumbura kuma ya kasance yana neman gafara a wajan Allahsau ]ari a rana)saboda haka yana da kyau mai kira ya fi kowa kusa da Allah Ubangiji ya kuma zama mai yawan ambatonsa.A }arshe ya [an’uwa mai wa’azi ina fatan za ka yi }o}ariwajan kulawa da wa]annan abubuwa da akabayyana, ina mai tabbatar maka za ka samu cin nasara a cikin da’awarka da taimakon Allah.ALLAH YA BAMU DACEWA DA KUMA CIN NASARA A CIKIN RAYUWARMU .IDAN K A KARANTA SAI KA BAWA WANI YA KARANTA.سبحانك اللهم و بحمدك أ شهد أن لا اله إلا أنت أستغفر و أتوب إليكبقلم جميل يوسف زريواالجامعة الإسلامية كليةا لشريعة

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

jagoran wa azi 9-11

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:29 AM

JAGORAN MAI WA’AZI٩musu a farko kar ku sha giya,da sun ce ba za mu daina sha ba, hakanan da an ce musuda farko kar ku yi zina da sunce ba za mu daina zina ba . (34)Wannan abin da Nana A,ishata fa]a shi ne manhajin qur’ani, don haka za mu gaalqur’ani ya sauka a cikin shekara ashirin da uku, kuma za muga cewa abubuwa dayawa Allah ya haramta su ne daga baya amma bai haramta su a farkon musulunci ba.Ya [an’uwa musulmi ka yi}o}ari ka fara koyawa Mutane abubuwan da su ka wajabaakansu, idan ka gama da su sai ka zo sunnoni da mustahabbai.Amma abin mamaki sai ka gawasu Masu wa’azin sun tsayaana ta rigima da su akanabin da yake sunna ne ko mustahabi alhalin kuma Mutane ba su gama iya abin da yawajaba akansu ba.Sannan kar ka ri}a tsawaita musu wajan wa’azi, kar kumaka ce za ka tura musu ilimitashi ]aya, ka ri}a binsu a hankali domin hakan shi ne aikin Annabi a cikinwa’azinsa, Abdullahi ]an Mas’ud ya kasance yana yiwamutane wa’azi duk ranaralhamis sai wani mutum ya ce masa (zan so ace kana yi mana wa’azi kullum) sai ya ceabin da yake hana ni in yi haka shi ne ba na so ku }osa,kuma ina so in rin}a ]aga muku}afa a wajan wa’azi kamar yadda Annabi yake yi mana don kar mu }osa. (35)Ina fatan za mu gyara wannan domin mu samu cin nasara a cikin Da’awarmu.7- TAUSASAWA MUTANEBa bu shakka in dai Malam yana so ya sami nasara a cikin wa’azinsa dole ne ya zamamai tausayi, saboda haka karya rin}a }osawa a cikin da’awarsa kar kuma ya damudabijirewar da ake yi masa, domin idan ya bar su ya daina kiransu makomarsu baza ta yikyau ba, shi ya sa za mu ga Annabawa sun fi kowa tausayi, kuma za mu iya fahimtarwannan tausayi a cikin }issar Annabi NUHU inda Allah ya ke cewa:( (لَقَد أَرسلْنا نوحاً إِلَى قَومه فَقَالَ يا قَومِ اعب  دوا اللَّه ما لَ ُ كم من إِلَه غَيرهإِني أَخا  ف علَي ُ كمعذَاب يومٍ عظيمٍ) (الأعراف: ٥٩Ma’anaHa}i}a mun aiki Nuhu i zuwa mutanansa, sai ya ce da su ya ku mutanena ku ji tsoranAllah ba ku da wani Ubangiji sai shi, ha}i}a ni ina ji muku tsoran azaba mai ra]a]i.A cikin wannan magana ta Annabi Nuhu za muga akwai tausayi a ciki da kuma rahama,bayan ya fa]a musu wannan maganar sai su ka jefe shi da~ata to amma duk da haka bairama ba sai ya korewa kansakawai, irin wa]annan misalansuna da yawa a cikinAlqur’ani da kuma hadisai kamar yadda aka rawaito daga Annabi cewa :(إنّ الله رفيق يحب الرفق، ويعطي على الرفق ما لا يعطي على العنف)Ma’anaAllah mai tausayi ne yana son tausayi, kuma yana bayarwa ta hanyar tausayi abin daba ya bayarwa ta hanyar tsanani. (36)Idan mu ka duba za mu ga cewa tausayi yana daga cikin dalilan da su ka saAnnabi ya ci nasara a cikin Da’awarsa, saboda Annabi ya siffantu da tausayibabban misali akan haka shi ne hadisin Balaraban {auye:Anas ]an Malik ya rawaito hadisi cewa wani balaraben {auye ya zo ya yi fitsari amasallaci sai Mutane su ka yimasa tsawa, sai Annabi ya ce ku }yale shi bayan yagama sai Annabi ya sa aka kawo guga na ruwa aka zuba.37)A wata riwayar Manzon Allah yake cewa an aiko ku masu sauki ne, ba’a aiko kumasu tsanantawa ba.(38)(٣٤ ) Bukhari ne ya rawaito٣٥ Bukhari da muslim(٣٦) muslim ne ya raw aito(٣٧) Bukhari da Muslim ne suka rawaito(٣٨) Bukhari ne ya rawaitoJAGORAN MAI WA’AZI١٠SharhiA cikin wannan hadisin za mu fahimci irin tausasawar Annabi ga mutanansa,domin ga shi Balaraban {auye yana fitsari a cikin masallaci amma Annabi saiya ce da sahabbai su kyale shi saboda tausasawa da kuma rahama.Saboda HAKA Allah ya yi umarni da taiusasawa har gaKafirai, misali idan mu kaduba }isar Annabi Musa shi da [an’uwansa Annabi Haruna lokacin da Allah yaaike su i zuwa Fir’auna ya ce da su ku gaya masa zance mai taushi babu mamaki yawa’aztu ko kuma ya ji tsoron Allah Kuma Annabi ya cewa A’isha ( ya A’isha ki ri}a yin tausayi domin Allah idanya so mutanan gida da alkhairi sai ya nuna musu tausayi) (39)A wani hadisin Annabi yanacewa :(من يحرم الرفق يحرم الخير)Ma’ana:Duk wanda aka haramta masa tausayi to an haramta masa alkhairi. (40)Ya [an’uwa mai wa’azi ka rin}a tausasawa a wa’azinka ta wajan magana da kumamu’amala wannan zai sa ka sami nasara da taimakon Allah, domin hatta Allahubangijinmu ya siffantu da rahama kamar yadda yake cewa ( كتب على نفسه الرحمة ) ma’anaAllah ya wajabtawa kansa rahama (ga bayinsa).Idan Allah da manzonsa sun kasance masu rahama, ina ga kai mai wa’azi wandayake so Mutane su gane hanyar gaskiya?8- KYAKYKYAWAR MU’AMALADA [ABI’U MASU KYAUMu’amala mai kyau da kuma [abi’u kyawawa suna taimakawa wajan tabbatar daDa’awa.A matsayinka na mai wa’azi ya zama dole ka rin}a yin mu’amala mai kyau damutananka, wannan ya ha]a da kai musu ziyara kyautata musu.Idan mu ka duba za mu ga Annabi ya kula da wannan~angaren sosai misali akanhaka shi ne hadisin da Bukhari ya rawaito cewa:Wani Yaro Bayahude da ya ke yiwa Annabi hidima ya yirashin lafiya, saiAnnabi ya je gaishe shi sai ya zauna kusa da kansa sai yace da shi ka musulunta,sai(Yaron) ya kalli Babansa sai (Babansa) ya ce da shi ka bi Baban Al}asim(Annabi) sai ya musulunta sai manzon Allah ya fito yana cewa godiya ta tabbataga Allah wanda ya tseratar da shi daga wuta. (41)SharhiA cikin wannan hadisin za mu fahimci amfanin kyautatamu’amala da Mutane,domin ga shi Annabi ya je gaida wannan yaron a sakamakon haka sai yamusulunta.Sannan za mu fahimci cewa Da’awa ba’a na yinta ta hanyar wa’azi ba ne kawai, zamu fahimci ana iya kiran Mutum zuwa musulunci ta hanyar ]abi’u kyawawa.Idan mu ka duba musamman a farkon musulunci za mu ga akwai mutanen da su ka yiimani da Annabi saboda gaskiyarsa, don haka yana dakyau ka zama mai ]abi’u masukyau kamar yadda Annabi yake cewa (fiyayyunku su ne wa]anda su ka fi kyawawan]abi’u), (42) idan kana zaune a cikin mutane ka yi }o}ari wajan girmama su da kuma kaimusu ziyara da gaida marasalafiyansu, saboda ta haka za su gane cewa ha}i}a suna damahimmanci a wajanka, sannan zai sa su su amshi wa’azinka hannu bi-biyu.٣٩ ) Ahmad ne ya rawaito٤٠ muslim ne ya rawaito(٤١) Bukhari ne ya rawaito٤٢ Bukhari ne ya rawaitoJAGORAN MAI WA’AZI١١9- {AS{ANTAR DA KAI GA MUTANEKa yi }o}ari ka zama mai kas}antar da kai, ka kuma guji girman kai domin girmankai shi ne farkon zunubin da aka aikata bayan an halicci Annabi Adamu, kumasaboda shi ne Allah ya kori SHAI[AN daga Aljanna ya kuma nisanta shi dagarahamarsa, ka kuma san cewa jahilci ne yake kawo girman kai, domin idan damutum ya sani to da ba zai yigirman kai ba saboda girma siffa ce da ga cikinsiffofin Ubangiji kamar yaddaAllah yake cewa a cikin hadisin da muslim ya rawaitocewa ([aukaka mayafina ne girma kuma kwarjallena ne, don haka duk wanda ya yijayayya da ni a ]aya daga cikinsu zan yi masa azaba).(43)Kuma ka daina alfahari da abin da Allah ya baka na ilmi domin abin da ka jahilta ya fiabin da ka sani yawa kamar yadda Allah yake cewa:( وما ُأوتيتم من الْعلْمِ إِلَّا قَليلاً) (الاسراء: ٨٥Allah yake cewa: Ba’a ba ku komai daga ilmi ba sai ]an ka]an.Saboda haka ya kamata ka yi}o}ari wajan siffantuwa da}as}antar da kai, kar kuma karin}a yaban kanka a gaban mutane sai su }osa da kai, kakuma san cewa gaba ]ayailiminka wata baiwa ce daga Allah, ka kuma yi }o}ari wajan bin sarakuna da kumashuwagabanni mutu}ar ba susa~awa Allah ba, Annabi yana cewa (wanda ya bishigaba ha}I}a ya bini, wandakuma ya sa~awa shugaba ya sa~a min) (44) .Sannan kuma yana cewa ( ku ji kuma kuma ku yi biyayya, koda an shugabantar mukubawa daga habasha) (45) (46)Don haka Annabi ya ke cewa (duk wanda yake da girman kai kwatankwacin kwayarzarra ba zai shiga aljanna ba (47)Idan mu ka duba alqur’ani zamu ga Allah ya yabi Annabi saboda sau}in kansakamar yadda ya ke cewa:ولَو ُ كنت فَظّاً غَليظَالْقَلْبِ لَانفَضوا من حولكMa’ana:Idan da ka kasance mai munanan ]abi’u mai kaushin zuciya, da (mutane) sun tafisun ba ka waje (48)Duk lokacin da ka zama mai kasan}antar da kai za ka samu nasarar a cikin wa’azinkadomin mutane za su kusantozuwa gareka wannan shi ya sa Allah ya umarci Annabida ya kas}antar da kai ga Muminai kamar yadda ya ke cewa( واخفض جناحك لمنِ اتبعك من الْ مؤمنِين) (الشعراء: ٢١٥Ma’anaKa shimfi]a fika-fikanka (ka}as}antar da kai) ga wa]anda su ka yi maka biyayyadaga muminai(49)Sai ka yi }o}ari ka zama mai}as}antar da kai ga mutane, ka rin}a nuna cewa kai ba kowa ba ne, kar kayi alfahari a cikin wa’azinka kamar yadda Annabi yake cewa ( Allah ya yi min wahayida cewa ku}as}antar da kai ta yadda wani ba zai yi alfahari ga wani ba) (50)(٤٣ ) muslim da Bukhari da Ibn Majah ne su ka rawaito(٤٤ ) muslim da Bukhari ne su ka rawaito(٤٥ ) Bukhari ne ya rawaito(٤٦ ) ma’ anar hadisin shi ne koda makaskanci daga cikinku ne ya zama shugabanku, To dole ne ku yimasa biyayya .(٤٧) muslim ne ya rawaito(٤٨) Ali-Imraana 159(49) shu’ara’i aya ta 215٥٠ muslim da Ibn Majah ne su ka rawaito

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

jagoran wa azi 7-8

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:26 AM

JAGORAN MAI WA’AZI٧3-ka rin}a saran cewa Allah zai ya ye maka wahalar da kake ciki kamar yadda ya kecewa Dukkan tsanani yana tare da sau}i Sharhi Aya ta 64-ka tuna cewa rayuwa ba ta rabuwa da wahalhalu, kuma Da’awa hanya ce mai wahala.Daga cikin abubuwan da suke nuna ha}uri mai wa’azi akwai:1- Rashin yin ramuwa idan akai masa wani abu.2- Rashin damuwa idan ba kasamu nasara da wuri ba.3- Cigaba da yin da’awa ba yankewa.4- Kada ya jefa kansa a cikin bala’i ( kamar idan ya zama in ya yiwa wani wa’azizai iya shiga halaka, to ya halatta ya }yale shi)5- SANYA HIKIMA A CIKIN WA’AZIIdan kana so ka samu nasaraa cikin Da’awarka dole ne ka sanya hikima a ciki kamaryadda Allah yake cewa:(اد  ع إِلَى سبِيلِ ربك بِالْحكْمة والْموعظَة الْحسنة)Ka yi kira i zuwa hanyar Ubangijinka da hikima da kuma wa’azi mai kyau (26)Sheik Ibn Uthaimin Allah ya yi masa rahama ya ce (Abin da ake nufi da hikima shi nekyautata abu da kuma inganta shi ta hanyar ajjiye shi a gurin da ya dace da shi,yacigaba da cewa ba zai yiwu ka ce mutane sai sun koma kamar SAHABAI ba tashi ]ayaba don haka wa’azi ba zai tafidaidai ba sai ana bin Mutanea hankali.) (27)Idan mai wa’azi yana yin amfani da hikima zai samu cin nasara da wuri a cikin wa’azinsa, saboda Annabiya yi amfani da hikima don haka za mu ga ya yi tasiri a cikin mutane wanda ba’a ta~a samun wanda ya yiirin wannan tasirin ba a tarihin duniya.Ga wasu daga cikin hanyoyin da za ka bi wajan kiran mutane ta hanyar hikima:1- Rashin yi musu wa’azi kodayaushe don kar su }osa, Abdullahi ]an Mas’ud ya kasance yanayiwa mutane wa’azi duk ranar alhamis sai wani mutum ya ce masa (zan so ace kana yimana wa’azi kullum) sai ya ceabin da yake hana ni in yi haka shi ne ba na so ku }osa,kuma ina so in rin}a ]aga muku }afa a wajan wa’azi kamar yadda Annabi yake yimana don kar mu }osa. (28)2- Duba maslaha lokacin da kake yin wa’azi, wannan ya ha]a da barin abin da yakebabu alhaki a cikin barinsa, idan ya zama aikata shi zai kawo fitina, misali za ka samumutane suna wani abu a cikin al’adunsu idan wannan abin da suke yi bai sa~awa shariaba, to ka }yale su su ci gaba koda kuwa barin wannan abin shi ya fi musamman idan kasan cewa hana su zai kawo fitina, misali akan haka Annabi ya bar rushe ka’aba dasake gina ta kamar yadda Annabi Ibrahim ya gina ta saboda mutane ba su da]e da shigamusulunci ba kamar yadda yake cewa da A’ISHA( ban da mutanenki ba su da]e dabarin jahiliyya ba da na yi umarni da a rushe ]akin ka’aba don in shigar da abin da basushigar da shi ba (29)Babban abin da za mu fahimta a wannan hadisin shine Annabi ya bar rushe ka’aba saboda maslaha domin{uraishawa ne su ka sake gina ta a lokacin jahiliyya, saboda haka yana tsoran kar ya rushe wata fitina ta auku.3- idan kana da hali ka rin}a yi musu kyauta shi yasa Allahya shara’anta bawa mutanan da ake tunanin za sumusulunta zakka kamar yadda Annabu yace ku rin}ayiwa juna kyauta za ku so juna (30)4- idan kaga wani ya yi laifi kana so ka fa]akar da shi lokacin da kake wa’azi kar ka fa]i sunansa domin hakanshi ne aikin Annabi misali za ka iya cewa me yasa mutane su ke yin kaza ko makamancin haka.(٢٦) NAHLI Aya ta 125(27) shafi na 18 a cikin Littafin زاد الداعية إلىالله٢٨ Bukhari da muslim٢٩ Bukhari ne ya rawaito٣٠ Baiha}i ne ya rawaitoJAGORAN MAI WA’AZI٨5- yawan buga misalai lokacin da kake yin wa’azi kamar yadda Larabawa su kecewa ta hanyar misalai akefahimtar magana, shi yasa zamuga Allah da manzonsa suna yawan buga misalai kamar yadda Allah yakecewa:(ولَقَد ضربنا للناسِ في هذَا الُْقرآن من ُ كلِّ مثَلٍ لَعلَّ هم يتذَكَّرونَ)Ma’anaHa}i}a mun bugawa mutane kowanne irin misali a cikin Alqur’ani don su wa’aztu. (31)6 – sanya hikima wajan koyawa mutane abin da basuiya ba , babban misali akan haka shine labarin ImamuAhmad lokacin da yake tafiyashi da abokinsa YAHAYA [AN MA’IN sai su ka ga wani tsoho bai iyaalwala ba, sai su ka yi tunani n hanyar da za su bi su koya masa, sai su ka ce da shi , muna gardama ne atsakaninmu akan waye ya fi iya alwala shi ne mu ke so mu yi ka gani don kayi mana shari’a sai su kayialwala a gabansa, sai ya ce duk kun fi ni iyawa.A cikin wannan kissar za mu ga yadda su ka koya masa alwala da dabara. (32)Yana daga cikin hikima a cikin wa’azi yiwa kowa wa’azi daidai da hankalinsa, da kuma duba maslahalokacin da m utum yake yin wa’azi, saboda Abdullahi [an Mas’ud yana cewa ba zaka ta~a gayawa Mutaneabin da bai kai }wa}walwarsuba, face sai ya zama fitina ga wasu daga cikinsu.6 – FARAWA DA ABIN DA YA FI MAHIMMANCI SANNANWANDA YA KE BIN SADaga cikin hanyoyin Annabiwajan da’awa shi ne yana farawa da abu maimahimmanci, sannan wandayake binsa, don haka za mu ga lokacin da yake makka yafi bada }arfi wajan kiran Mutane i zuwa Tauhidi saboda shi ne ya fi komai mahimmancia cikin addinin MUSULUNCI, sauran farillai kuwa yawanci an shara’anta su ne aMadina.Babban misali akan wannan ginshi}i shi ne Hadisin Mu’az bn Jabal wanda Ibn Abbasya rawaito yake cewa:لمّا بعث معاذا إلى اليمن قال :(إنك تأتي قوما من أهل الكتاب فليكن أول ما تدعوهم إليه  وعن ابن عباس رضي الله عنهماأن رسول اللهشهادة أن لاإله إلاالله، فإن هم أطاعوك لذلك فأعلمهم أنّ الله افترض عليهم خمس صلوات في كل يوم وليلة، فإن هم أطاعوك لذلكفأعلمهم أنّ الله افترض عليهم صدقةً تؤخذ من أغنيائهم وترد على فقرائهم)An karbo daga Ibn Abbas Allah ya }ara musu yarda yace: Lokacin da Annabi yaaika Mu’az i zuwa Yaman sai ya ce da shi :Za ka riski wasu mutane daga cikin ma’abota littafi (idan ka riske su) Farkon abinda zaka kira su zuwa gare shi shi ne su shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Idansun yi maka biyayya akan haka, To ka sanar da su cewaAllah ya farlanta musu salloliguda biyar a cikin kowanne dare da rana, Idan sun yi maka biyayya akan haka, to kagaya musu Allah ya wajabtamusu zakkar dukiyoyinsu wacce za’a rin}a amsa a wajanMasu ku]i daga cikinsu a bawa Talakawa. (33)SharhiA cikin wannan hadisin za mu ga Annabi ya umarci Mu’az ya fara kiran Mutane izuwa Tauhidi sannan Sallah daganan kuma sai Zakka, saboda haka hadisin yana nunamana cewa a fagen Da’awa ana farawa ne da abin da ya fi mahimmanci sannan wandayake binsa.Sannan Nana A’isha tana cewa ( farkon abin da ya farasauka a cikin alqur’ani shi negajerun surori a cikin su akwai ambaton aljanna da wuta, lokacin da mutane su ka rin}ashiga musulunci sai halal da haram su ka sauka, ta cigabada cewa idan da ace an gaya٣١ zumar aya ta 27(٣٢ ) kamar yadda su ka yi haka ake so mai wa’azi ya zama.(33) Bukhari da Muslim ne suka rawaito

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

jagoran wa azi 5-6

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:24 AM

JAGORAN MAI WA’AZI٥وغيرالتقي يأمرالناس بالتقى طبيب يداوي الناس وهو سقيمياأيها الرجل المعلم غيره هلا لنفسك كان ذاالتعليمفابدأ بنفسك فاها عن غيها فإذانتهت عنه فأنت حكيمفهناك يقبل إذاوعظت ويقتدى بالقول منك وينفع التعليملاتنه عن شيء وتأتي مثله عارعليك إذا فعلت عظيمMa’ana1-Yanzu mara tsoran Allah ne zai rin}a umartar Mutane da tsoran Allah ! In daihaka ne to ya zama Likitan dayake bada magani alhali shi ma ba shi da lafiya.2- Ya kai mai koyar da wani, ina ma da ka fara da koyar da kanka !3- Ka fara da hana kanka aikata sa~o, idan ka hanu to ka zama mai hikima .4- A lokacin sai ka ga an amshi wa’azinka an kuma yi ko yi da kai, kuma koyarwar ta yiamfani.5- kada ka hana abu ka zo ka aikata shi domin hakan aibu ne a gareka mai girma .Kuma Imamu IBN Shihab Azzuhuri yana cewa: ( Ba’a yarda da maganar Malamin daba ya aiki da ililiminsa.Saboda haka sai ka yi }o}ari wajan yin aiki da abin da kake fa]a don ka sami tsira awajan Allah, kuma mutane su yi amfani da wa’azinka.4- SIFFANTUWA DA HA{URIDa’awa ba zata yiwu ba sai da ha}uri, domin za ka ha]u da abubuwa iri-iri wani zai ceba ka san abin da ka ke yi ba,wani ma ya zage ka domin hakan shi ne sunnarAnnabawa, shi ya sa a gurareda yawa Allah yake bawa Annabi ha}uri akan}aryatawar da Mutanansa su ka yi masa kamar yadda Allah ya ke cewa:( فَإِنْ كَذَّبوك فَقَد ُ كذِّب  ر  س ٌ ل من قَبلك جاءُوا بِالْبينات والزبرِ والْكتابِ الْ  منِيرِ )Idan sun }aryata ka To ha}i}a an }aryata Annabawan da su ka zo gabaninka, sun zo daHujjoji da littattafai da kuma littafi mai haske. (٢٢)A wata ayar kuma Allah yana cewa:( كَذَلك ما أَتى الَّذين من قَبلهِم من ر  سولٍ إِلَّا قَاُلوا ساحر أَو مجنو ٌ ن )Hakanan babu wani Manzo da ya jewa wa]anda su ka zo gabaninsu fa ce sai sun cemasa mai sihiri ko Mahaukaci. (٢٣)Ba bu makawa ga mai wa’azi sai ya ha]u da abubuwa gudabiyu:1. sau da yawa wa]anda ya kira za su bijire masa, dominzai iya yin wa’azi ammaba za’a amsa masa ba, saidaiya ji shi kamar yana magana da Kurame, Babu abinda ya fi kamata a gareshi saidai ya yi ha}uri ya kuma yikoyi da fiyayyan halittadomin akwai lokacin da ya kira mutanansa babu abin dasu ka ce masa illa (kata~e yanzu don haka ka kira mu?)Sannan a cikin mutanansa akwai wanda ya tuhumce shi da hauka, wasu kuma dabokanci wasu kuma da }arya dadai sauransu.2. Zai ha]u da cututtuka daga wa]anda yake yi ma wa’azi, kai za’a iya ]ibandukiyarsa ko kuma a azabtar da shi ko aci mutuncinsa, abin ma zai iya kaiwa gakisa, saidai ya kamata kodayaushe mai wa’azi ya rin}a tuna fa]in Allah:لَتبلَ  ونَّ في أَموال ُ كم وأَنُفسِ ُ كم ولَتسمعن من الَّذين ُأوتوا الْكتاب من قَبل ُ كم ومن الَّذين أَشر ُ كوا أَذى كَثيراً وإِنْ تصبِروا وتُقوا فَإِنَّ ( آل عمران: ١٨٦ )  ذَلك من عزمِ الُْأمورِZa’a jarrabe ku a cikin dukiyoyinku da kuma kawunanku, kuma za ku ji dagawa]anda aka bawa littafi kafin ku da kuma wa]anda suka yi shirka cutarwa mai(٢٢) Ali-Imraana 184(23) Zariyat Aya ta 52JAGORAN MAI WA’AZI٦mai yawa (wannan ya ha]a da suka a cikin addini da kuma littafin da aka saukarwamumuinai kamar yadda Imamu Nasirussa’adi ya fassara) amma idan ku ka yi ha}uriku ka kuma ji tsoran Allah to wannan yana daga cikin abubuwa wa]anda akehimmatuwa wajan aikata su. (٢٤)Idan mu ka duba tarihin Annabi za mu ga yadda Mushrikai su ka cutar dashi saboda yana kira i zuwa ga Allah, Kai har su ka kusa kashe shi kamaryadda Bukhari da Ahmad su ka rawaito:عن  عروةَ ب  ن الزبيرِ قَالَ ُقلْ  ت لعبد اللَّه بنِ عمرِو بنِ الْعاصِ أَخبِرنِي بِأَشد ما صنع الْ  مشرِ ُ كونَ بِر  سولِ اللَّه صلَّى اللَّه علَيه وسلَّم قَالَ بينار  سو ُ ل اللَّه صلَّى اللَّه علَيه وسلَّم يصلِّي بِفناءِ الْكَعبة إِذْ أَقْبلَ  عقْبُة ب  ن أَبِي معيط فَأَخذَ بِمنكبِ ر  سولِ اللَّه صلَّى اللَّه علَيه وسلَّم ولَوى ثَوبهفي  عنقه فَخنقَه بِه خنقًا ش  ديدا فَأَقْبلَ أَبو بكْرٍ فَأَخذَ بِمنكبِه ودفَع عن ر  سولِ اللَّه صلَّى اللَّه علَيه وسلَّم وقَالَ أَتقْتُلونَ ر  جلًا أَنْ يُقولَ ربياللَّه وقَد جاءَ ُ كم بِالْبينات من ربُ كمMa’anaUrwatu ]an Zubair ya tambayi Abdullahi bn Amri bn Ass cewa, ka bani labarin mafimunin abin da Annabi ya fuskanta daga MUSHRIKAI sai ya ce:Akwai wani lokaci da Annabi yake yin sallah a filin ka’aba, sai U}batu ]an AbiMu’ai]in ya zo ya sha}e Annabi sha}a mai tsanani, sai Abubakar ya zo ya tunku]eshi ya ce (Ya za ku kashe Mutum don ya ce Allah shi ne Ubangijina, Ga shi kuma yazo da hujjoji bayyanannu daga Ubangijinku.Dubi yadda Annabi ya sha wahala ba don wani abu ba sai don yana kira zuwaga Allah, Idan ka karanta kissoshin Manzanni za ka ga irin wa]annan misalai dayawa, kamar Annabi Hudu mutanansa sun ce masa ma}aryaci, Don haka a matsayinkana mai da’awa dole ne ka fuskanci irin wa]annan, idan kuma ka yi ha}uri ka tabbataakan abin da ka ke kai kana da lada a gurin Allah, domin Allah zai sanya ka kazama shugaba a cikin addinin Allah kuma ka samu matsayi mai girma wanda Mutaneza su rin}a shiryuwa ta hanyarsa .Imamu Ibnul {ayyim yana cewa na ji Shaikul islam Ibn Taimiyya yana cewa (anasamun shugabanci ne a cikinaddini ta hanyar ha}uri da kuma sakankancewa (ya}ini)sai ya karanta fa]in Allah: وجعلْنا من  هم أَئمةً يه  دونَ بِأَمرِنا لَما صبروا وكَانوا بِآياتنا يوقنونَ Ma’ana:Mu ka sanya Shuwagabanni daga cikinsu lokacin da su kayi ha}uri suna shiyarwa(zuwa gaskiya) da umarninmu kuma sun kasance masu sakankancewa(ya}ini) daayoyinmu) Sajdat Aya ta 24Kuma ha}uri yana daga cikin abubuwan da su ke nuna cikar hankalin Mutum don hakaza mu ga Annabi ya fi kowa ha}uri don haka lokacin da mutanan [a’if su ka jefe shisai ya yi musu addu’a mai kyau ya ce: (Ya Allah ka shiryimutanena domin su ba su saniba ne ( (اللهم اهد قومي فإنهم لايعلمون) ( 25Ina so in tunatar da ‘yan’uwa masu wa’azi akan akan abubuwan da su ke taimakawawajan yin ha}uri a fagen Da’awa:1-ka zama mai koyi da Annabi da kuma masu ha}uri daga cikin Manzanni da kumaSahabai.2- ka ri}a tuna sakamakon daza ka samu a wajan Allah kamar yadda ya ke cewaAna cikawa masu ha}uri ladansu ba tare da }ididdiga ba٢٤ Ali-Imran aya ta 186٢٥ maana ba su san matsayinsa ba, shi yasa su kayi masa haka

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

jagoran wa azi 1-4

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:22 AM

JAGORAN MAI WA’AZI١DA’AWA DA SIFFOFIN MAI WA’AZI A CIKIN ADDININMUSULUNCIبسم الله الرحمن الرحيموصلى الله على النبي الكريمHa}i}a kira i zuwa addinin Allah tana da mahimmanci mai girma domin Annabi yafa]a a cikin hadisin da Bukhari da muslim su ka rawaito cewa (Allah ya shiryar daMutum ]aya ta hanyarka ya fimaka alkairi akan a baka jajayan ra}uma) hakananAllah ya fa]a a cikin Alqur’ani cewa (Ha}i}a ku ne fiyayyun al’umma wa]anda akafitar daga cikin mutane, kunaumarni da kyakykyawa kuna kuma hani daga barinmummuna) (1) sannan Annabi yana cewa (wanda ya kira Mutane zuwa shiriya yanada ladan duk wanda ya bishi ba tare da an rage musu wani abu ba) (2)Ha}i}a wa]annan dalilai suna nuna mana mahimmancin kira i zuwa ga addininAllah saidai kafin mu cigabayana da kyau mu yi bayani akan menene Da’awa?MENENE DA’AWA?Abin da ake nufi da Da’awa shi ne (kwa]aitar da mutane izuwa hanyar alkhairi dakuma umarninsu da kyakykyawa da hana su aikata mummuna don su samu arzikinduniya dana Lahira). (3)Sheik Ibn Taimiyya kuwa cewa ya yi: ( Da’awa ita ce kira i zuwa Imani da Allah dakuma abin da manzanni su ka zo da shi ta hanyar gaskata su cikin abin da su ka badalabari da shi da kuma yi musu biyayya a cikin abin da su kai umarni da shi. (4)wa]annan ma’anoni guda biyu suna nuna mana cewa Da’awa ta }unshi Dukkan~angarori na addini gaba]aya.Kamar yadda mu ka sani wajibi ne a cikin Al’uma a samu wa]anda za su rin}a yinkira i zuwa ga addinin Allah kamar yadda Allah yake cewa a cikin Alqur’ani maigirma:{ولْت ُ كن من ُ كم ُأمٌة يد  عونَ إِلَى الْخيرِ ويأْمرونَ بِالْمع روف وينهونَ عنِ الْ  منكَرِ وُأولَئك  ه  م الْ  مفْل  حونَ)Ma’anaLailai ne a samu wata Al’umadaga cikinku wa]anda za su rin}a kira zuwaalkhairi suna umarni da abu mai kyau suna kuma hani ga barin mummuna, wa]annansu ne ma su babban rabo. (5)Sannan Annabi yana cewa :(والذي نفسي بيده لتأمرنّ بالمعروف ولتنهونّ عن المنكر أوليوشكن الله أن يبعث عليكم عقابا ثم لتدعنه فلا يستجيب لكم)Ma’anaNa rantse da wanda raina yake a hannunsa ko dai ku yi umarni da kyakykyawan aikikuma ku yi hani da mummuna ko Allah ya aiko mu ku da wata azaba sannanku rokeshi ya }i amsa muku. (6)Sannan kuma Hadisai sun nuna mana cewa babu wani aiki a duniya wanda ya fiDa’awa mahimmamnci Annabi yana cewa:(لأن يهدي الله بك رجلاواحدا خير لك من حمر النعم)Ma’ana(١)Ali-IMRANA Aya ta 110(2) ma’ana duk wanda ya yi aiki da wa’azinsa ALLAH zai ba shi irin ladansa muslim ne ya rawaito(٣) Duba Hidaayatul murshidina na Aliyu Mahfuz shafi 18(4) Majmu’ul fataawa kashi na 15 shafi na 157(٥) Ali-Imrana Aya ta 110(٦) Tirmizi ne ya rawaito ya ce kuma mai kyau neJAGORAN MAI WA’AZI٢Allah ya shiryar da Mutum]aya ta hanyarka ya fi maka a baka jajayan ra}uma (7)Kuma akwai wani hadisi wanda zai }ara nuna mana mahimmancin wannan aiki hadisinshi ne:وهوعلى المنبر فقال يا رسول الله أي الناس خ ير؟ قال خيرالناس أقرأهم وأتقاهم لله،  (عن درة بنت لهب قالت قام رجل إلى النبيوآمرهم بالمعروف وأاهم عن المنكر).Ma’ana:An kar~o daga Durrata ‘yar Lahabin ta ce: wani mutum ya ce da Annabi a lokacinAnnabi yana kan Minbari, wanene ya fi Alkhairi a cikin Mutane ? sai ya ce : (wandaya fi kowa a cikin Mutane shi ne wanda ya fi su iya karatunAlqur’ani kuma ya fi sutsoran Allah ya kuma fi umarni da kykykyawa da kuma hani da mummuna. (8)SIFFOFIN DA YA KAMATA MAI WA’A ZI YA SIFFANTADA SUSaidai akwai wasu sharu]]a ko siffofi wa]anda ya kamata mai Da’awa ya sifantu da sukuma gwargwadon siffantuwarsa da wa]annan siffofi gwargwadon nasarar da zai samua da’awarsa da taimakon Allah .A cikin wannan littafi nawa zan fa]i wasu daga ciki da yardar Allah .1-TSARKAKE NIYYAKamar yadda mu ka sani cewa }ashin bayan kowanne aiki shi ne niyya kamar yaddaAnnabi yake cewa Dukkan ayyuka ba sa ingantuwa sai da niyya (9) kuma Allahyana cewa: وما ُأمروا إِلَّا ليعب  دوا اللَّه مخلصين لَه الدين Ba’a umarce su ba saidai su bautawa Allah sunamasu tsarkake addini zuwa gare shi (١٠)A matsayinka na mai kira i zuwa ga Allah ya zama dole ka tsarkake niyyarka yazama kana yi don Allah ne kawai ba don wani abu ba.Sannan ka ji tsoron yin RIYA Abin da ake kira riya shi ne ka yi aiki don mutane su yaba maka, saboda ita riya tana~ata aiki kuma ba za ka samulada a wajan Allah ba,domin Allah yana cewa a cikin hadisil }udsi:(أناأغنى الشركاء عن الشرك، من عمل عملا أشرك فيه معي غيري تركته وشركه) ٠Allah ya ke cewa a cikin wannan hadisin, (Ni ne ma fi wadatar masu yin tarayya dagabarin tarayya, wanda ya aikata wani aiki ya ha]a ni da wani sai in bar shi da wanda yaha]a ni da shi.) (11)Daga cikin mهsalan da su ke nuna rahin Iklasi :1- Tsawaita sallah da kuma bayyana tsoran Allah a cikinta don Mutane su gani, ko kuma cinabinci a gaban Mutane idan ya kai azumi ko bayyana yawan hajjin da ya yi a rayuwarsa don yanunawa mutane ya yi ibada da yawa .2- Ya zama cewa ba ya son yin Lacca ko darasi sai gurin da Mutane su ka cika.3- Ya zama yana sonj mutanesu yabe shi.4- Idan zagin da mitane suke yi masa yasa ya daina yin wa’azi.5- Yawan yin alfakhari da ilmin da Allah ya ba shi a wajan wa’azi..(7) kamar kuma yanzun za’a iya cewa ya fi a ba ka Bibut da Banbalasta da sauran abubuwan hawa na morewa(٨) Ahmad ne ya rawaito kuma Haithami ya ce wa]anda su ka rawaito shi Amintattu ne(9) Bukhari da muslim ne su ka rawaito(١٠) suratul Bayyinaat Aya ta 5(11) ma’a’na ba zai saka masa, Muslim ne rawaitoJAGORAN MAI WA’AZI٣Amma idan Mutane su ka yabe shi ko su ka zama suna halattar darusansa wannan ba zai ta~a Iklasinsa ba,domin ya tabbata a hadisi ingantacce wanda muslim yarawaito cewa (wani Mutum ya cewa Annabi ya manzon Allah, kaba ni labari idan Mutum yana aikata alkairi mutane suna gode masa ?Sai ya ce wannan BUSHARA ce ta kusa ga mumini)Ma’ana wannan ba zai ta~a Iklasinsa ba, Allah yana masa bushara ne tun a duniya kafin ya je lahira.Don haka ya kamata ga mai wa’azi ya kiyaye wa]annan abubuwan da zan fa]a :1-Ya zama yana yin wa’azinsane don neman yardar Allah da kuma neman lada a gurinsa.2-Ya yi }o}ari wajan tsayawa da wa’azinsa yadda ya kamata.3-Aiyukansa su zama daidai da wa’azinsa.4-Ya yi }o}ari wajan neman tsari daga sharrin Shai]an dakuma riya.5-Kar ya manta da neman taimako a wajan Allah.Don haka ya [an’uwa musulmi sai ka yi }o}ari wajan gyara niyyarka.2- YA ZAMA YANA YIN WA’AZINSA DA ILMIShara]i babba daga cikin sharu]an da’awa shi ne ya zama mai da’awa yana da ilmiakan abin da ya ke kira akai kamar yadda Allah ya ke cewa: ُقلْ هذه سبِيلي أَد  عو إِلَى اللَّه علَى بصيرة أَنا ومنِ اتبعنِي Ma’anaKa ce, wannan ita ce hanya ta, ina kira i zuwa ga Allah abisa ilmi Ni da wanda yabini (12)Sharhi :Wannan Aya tana nuna manacewa ya zama dole mai wa’azi ya san abin da Allah yashara’anta da kuma abin da Allah bai shara’anta ba, ta yadda zai bambance tsakaninHalal da Haram da sunna da bidi’a ya kuma san Shirka da kuma Tauhidi, domin ta hakane zai iya magance matsalolin da suke damun jama’ar da ya ke yiwa wa’azi.Kuma lallai Ka ji tsoron koyarda mutane abin da ba ka da ilmi domin za ka iya fa]awahalakar da ba za ka iya fita daga cikin ta ba saboda zai iya saka ka yiwa Annabi}arya, kuma Annabi yana cewa (Duk wanda ya yi mini}arya da gangan ya tana jigurin zamansa a wuta. (13)Baban misali akan haka shi ne hadisin da Bukhari da Musim su ka rawaito cewa (wani MUTUM ya kashemutane casa’in da tara sai yatambayi wani Malami shin ina da tuba ?Sai Malamin ya ce ba ka da tuba sai ya kashe malamin yacikashe ]ari da shi, sai ya je ya tambayi waniMalamin sai ya ce da shi kana da tuba, sai ya umarce shi da ya yi hijira i zuwa wata}asa ta salihanmutane……………. har zuwa}arshen hadisin. (14)Abin da za mu fahimta a cikin wannan hadisin, malamin farkon ya yi fatawa bada ilmi ba mun kuma gasakamakonta, wannan ya ke nuna mana cewa bai halatta ba mutum ya yi fatawa ba da ilmi ba.Kuma duk abin da baka sani ba, to lailai ka ce ban sani ba kamar yadda Muhmmad ]anAjlan yake cewa:من فقد لا أدري فقد أصيب في مقاتله.Ma’anaDuk wanda ya rasa (kalmar) ban sani ba to ha}i}a an sokeshi a makasarsa.Mai wa’azi ya yi }o}ari wajan haddace alqu’ani da farko da kuma karanta wasu dagalittattafan A}ida kamar كتابالتوحيد da أصول الثلاثةda kuma littattafan fiqhu kamar الأخضري daرسالة أبي زيد القيروا

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

ina yakamata inkalla ajikin budurwata

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:10 AM

To dan’uwa ya halatta ka kallimacen da kake so ka aura, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa : “Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan” Abu dawud a hadisi mai lamba ta : 2082. Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure : 1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai, saboda tafin hannu yana nuna ni’imar jikin mace,kamar yadda fuska take nunakyau, don haka sai a takaita akan su, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai. 2. Zai kalli duk abinyake bayyana a jikin mace, don haka bayan fuska da hannu zai iya kallon duga-dugai da wuya. 3. Wasumalaman sun tafi akan cewa: zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juyabaya ya kalleta. Wannan ra’ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura, yadda ya kamata . Saidai ba’a son yawaita kallon saboda duk abin da aka halatta saboda bukata, toya wajaba a tsaya a gwargwadonta, wannan yasayawaita zuwa zance da yawaita yin waya, zai iya zama haramun saboda yana iya tayar da sha’awa, sha’awatana iya kaiwa zuwa barna Allah ne mafi sani Don neman Karin bayani, duba : Al’insaf 815 da Muhallah 9161.

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

hukuncin shan nonon matarka

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:07 AM

To dan’uwa Allah madaukakin sarki ya halatta maka jin dadi da dukkkan bangarorin jikin matarka, in ban da dubura ko kuma saduwa da ita lokacin da takehaila, don haka ya halatta ka tsotsi nononta mutukar baburuwa a ciki, amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani akan halaccin hakan zuwa maganganu guda biyu :1. Ya halatta, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. “Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacceyaro ya sha saboda yunwa” , Bukhari lamba ta : 5102, ma’ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai .2. Bai halatta ya sha ba, saboda ko da yaushe mutumya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi s.aw. ya umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure .Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta miji ya sha nonon matarsa, saidai rashin shan shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai yana da kyau, don neman Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid 267

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

hukuncin jan carbi

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:06 AM

jan carbi ba bidi’a ba ne, saboda duk da cewa babu shi a zamanin Annabi s.a.w. hakan ba zai saya zama bidi’a ba, saboda wanda yake amfani da shi baya nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, yana amfani dashi ne, don ya kiyaye adadin zikirinsa. Yin amfani da ‘yan yatsu shi ne yafi, saboda hadisi ya yi nuni cewa : za’a ba su dama su yi magana, ranar alkiyama, kamar yaddaTirmizi ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a hadisimai lamba ta: 3486, don hakaza su yi maka shaidar abin da ka yi na alkairi, sabanin carbi. Sannan sau da yawa zaka ga mutum yana jan carbi amma hankalisa yana wani wajen, sabanin idan da hannu yake yi. Jan carbi yakan iya sanya wasu su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne. Annabi s.aw. yana yin tasbihi da hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya inganta, saidai wasu malaman suna cewa in ya yi da hagu ma yayi, tare da cewa yi da dama shi ne ya fi. Saidai duk da dalilan da sukagabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, balle ace ya zama bidi’a, ga shi kuma ba’a samu wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi da hannu shi ne yafi .Don neman Karin bayani duba : Majmu’ul fataawa 22187. da Lika’ul maftuh na Ibnu-uthaimin 330. Allah ne mafi sani

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

shin ja afar assadiq danshiane

from nuramuhd3 on 04/02/2015 11:02 AM

Tambaya : Don Allah malam wai Imamussadiq dan shi’a ne, kuma ba zan dau wani abu daga iliminsa, wanda nake da tabbacin gaskiya ne, na yi amfani da shi ba, dan yana dan shi’a ?Amsa : To ‘yar’uwa Ja’afar Assadiq ba shi da alaka da shi’a , yana cikin Ahlul-baiti, ya barranta kansa daga ayyukan shi’a a wurare da dama, ga abin da yake cewa akan mutu’a, “Ba wanda yakeaikata mutu’a a cikinmu sai fajirai” duba biharul anwar shafi na 318 saidai yana dagacikin limaman shi’a guda goma sha biyu, wadanda suke riyawa, duk a cikin limaman guda goma sha biyu, babu wanda suka yiwa karya kuma suka kirkiri hadisai suka danganta masa kamar shi, wannan yasa sai manyan manazarta ne za su iya gano hadisan gaskiya daga na karya a cikin littattafan shi’a wadanda suke dangantawa wannan babban malami kuma jinin anabta, kuma hatta malamanshi’a sun tabbatar da hakan amaganganunsu, kamar yadda ahlussunnah suka tabbatar, ga wasu daga cikin bayanai akan haka :Kisshi ya rawaito hadisi daga Yunus yana cewa : Naje Irak sai naga sahabban Ja’afar Assadiq sun taru, sai na ji hadisai daga wajansu bayan na gama ji sai na dauki littatafansu na je na nunawa Aliyu Arridha, (daya daga cikin Ahlul-baiti) sai ya musa da yawa daga cikin hadisan, ya ce ba zai yiwu ace Ja’afarassadiq ne ya fade su ba, sannan ya ce Abul-kaddab ya yiwa Ja’afar Assadiq karya, Allah ya tsinewa Abul-khaddab, kamar yadda ka gani haka almajiran Abul-khaddab suke shigar da karya a cikin littattafanmu, suna cewa Ja’afar Assadiq ne ya fada, don haka duk abin dasuka gaya muku daga wajanmu kar ku amsa in har ba Qur’ani ba ne” Rijalu- Allkishhi 3298. 2. Sannan Majlisi ya fada a cikin Bihar Al’anwar cewa “Abu-abdillah –wato Ja’afarAssadiq- yana cewa : Mutane sun zurfafa wajan yi mana karya” Bihar Al’anwar :2246. 3. Ja’afar Assadiq yana cewa : ” Allahya jikan wanda ya sanyawa mutane son mu, bai yi abinda mutane za su ki mu ba, amma za ka ga daya daga cikinsu zai ji kalma daya a wajanmu, sai ka ji ya kara guda goma na karya” Al-kafy 8192.WADANNAN DALILAI NE DAGA MANYAN LITTATTAFAN ‘YAN SHIA WADANDA SUKE NUNA CEWA : ‘YAN SHIA SUNA YIWA JA’AFAR ASSADIQ KARYA..Wannan yasa Ibnu Taimiyya yake cewa : “Babu wanda akayiwa karya kamar Ja’afar Assadiq” Duba Minhaj assunnah 7391Saboda dalilan da suka gabata ina baki shawarar cewa kada ki dauki maganar da kika gani daga Ja’afar Assadiq a cikin littattafan shi’a ko kuma kananan littatafan Ahlussunah wadanda ake siyarwa a kasuwa, mutukar ba ki tabbatar da tabbatuwar malamin a ilimin sunna da sanin isnadi ba, saboda yawan karyar aka yi masaAllah ne mafi sani

Reply
First Page  |  «  |  1  ...  5  |  6  |  7  |  8  |  9  ...  24  |  »  |  Last

« Back to previous page