Latest posts

First Page  |  «  |  1  ...  7  |  8  |  9  |  10  |  11  ...  24  |  »  |  Last Search found 237 matches:


nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

neman ilimi a muslinci 1-7

from nuramuhd3 on 04/02/2015 10:09 AM

NEMAN ILIMI A MUSULUNCI1GABATARWAبِسْمِ اللَّھِ الرَّحْمَنِ الرَّحِیمِالحمد لله رب العلمین والصلاة والسلام على خیر خلق الله أجمعین، وعلى آلھ وأصحابھوالتابعین ومن تبعھم بإحسان إلى یوم الدین.Bayan haka, kamar yadda muka sani neman ilimi yana daga cikin manyanibadu, saboda mutum ba zai san addininsa ba sai ta hanyarsa, kuma dukwanda ya yi ilimi ya yi amfanida shi zai zamar masa hanyar shigaaljanna, kuma ya kasance masa jagora wajan rayuwarsa ta duniya, tayadda zai samu wayewa ya bambamta da sauran mutane, kamar yaddaAllah (s.w.t.) ya ke cewa (shinwa]anda su ka yi ilimi za su yidaidai dawa]anda ba su yi ilimi ba) (1)Kasancewar akwai littattafai da yawa na larabci da wasu yarirrikanwa]anda su ka yi magana akan neman ilimi, na ga ya kamata in rubutawani abu akan neman ilimi da Harshenmu na Hausa, babu mamaki Allah(s.w.t.) ya amfanar da}ananan ]alibai da shi, don haka sai na nemitaimakon Allah (s.w.t.) na rubuta wannan ta}aitaccen rubutu, wanda nake fatan Allah (s.w.t.) ya sanya ma sa albarka, kuma ya sanya shi sabodaneman yardar Allah (s.w.t.) amin.wannan ]an ta}aitaccen rubutu wanda na kira shi da sunan, NEMANILIMI A MUSULUNCI, in Allah(s.w.t.) ya yarda zai }unshi abubuwakamar haka:1. Falalar neman ilimi2. Hukuncin neman ilimi.3. .Abubuwan da suke taimakawa wurin neman ilmi.4. Abin da ya kamata ]alibi yafara da shi lokacin da zai faranemanilimi.5. Laduban neman ilimi.6. Alamomin ilimi mai amfani.7. Mafificiyar hanya wurin haddace al-qur’ani.8. Yadda ake yin muraja’ar al-qur’ani.9. ka’idojin haddar al-qur’ani.Ina fatan abin da muka fa]a na daidai a ciki Allah (s.w.t.) ya bamu lada,ya kuma amfanar da mutane da shi, abin da kuma mu ka fa]a na kuskureAllah (s.w.t.) ya gafarta mana.JAMILU YUSUF ZAREWA1861429 DAIDAI 2262008(١) Suratu Zumar aya ta 9NEMAN ILIMI A MUSULUNCI2NEMAN ILMI A MUSULUNCIFALALAR NEMAN ILIMINeman ilimi yana da daraja mai girma, saboda Allah (s.w.t.) ya ]aukaka masu ilimikuma ya bambamta su da ragowar mutane, kamar yadda Allah (s.w.t.) yake cewa:(shin wa]anda su ka yi ilimi za su yi daidai da wa]anda basu yi ilimi ba)(2) kumaAllah (s.w.t.) yana cewa: (wa]anda suka san Allah (s.w.t.) daga cikin bayinsa sunekawai suke jin tsoransa)(3) kuma yana cewa a cikin wata ayar: (Allah (s.w.t.) yana]aukaka wa]anda su ka yi imani daga cikinku da kuma masu ilimi darajoji) (4)Kuma ita ce hanyar Annabawa kamar yadda Annabi (s.aw.) yake cewa (Malamaimagada Annabawa ne, kumaAnnabawa ba su gadar da zinare ko dirhami ba, abin dasuka gadar shi ne ilimi duk wanda ya ri}e shi to ya yi rikogwaggwa~an rabo)(5) kumaAnnabi (s.aw.) yana cewa (wanda ya fita neman ilimi yana kan hanyar Allah (s.w.t.)har ya dawo) (6)kuma yana cewa (wanda ya bi hanya yana neman ilimi a cikinta Allah(s.w.t.) zai sawwa}e masa da ita hanyar shiga aljanna)(7) kuma yana cewa mala’ikusuna saukar da fika-fikansu ga mai neman ilimi saboda yarda da abin da yake yi) (8)Sayyidina Ali- Allah (s.w.t.) yayarda da shi- yana cewa (ya ishi ilimi ]aukaka wandabai iya shi ba yana da’awarsa, kuma yana farin ciki idan aka danganta shi i zuwa gareshi, kuma ya ishi jahilci}as}anci wanda yake cikinsa ba ya so a danganta shi da shi)(9) kuma Sufyan bn Uyaynah yana cewa (mafi ]aukakar daraja a cikin mutane shi newanda yake tsakanin Allah (s.w.t.) da bayinsa, wato Annabawa da malamai) (10)kumaSufyan Asthauri yana cewa (babu wata ibada bayan farillai da ta fi neman ilimi) (11)Kuma Ibn Abdulbar yana cewa ya ga wa}ar Ahmad bn sa’id-Abu Amr- a cikin littafinBabansa yana cewa:    Ma’ana: Naga ma’abocin ilimi ma]aukaki ne, ko da wa]andasu ka haife shi}as}antattu ne.(٢) Suratu Zumar aya ta 9(3) wannan ayar tana nuna mahimmancin ilimi, domin mutum idan bai yi ilimi ba ta yaya zai san Allah(s.w.t.) ? duba suratul fa]ir aya ta 28(4) mujadalah aya ta 11(5) Abu dawud ya fitar da shi a hadisi lamba ta 3641, da Ibn majah 223 kuma na ga Abul ashbalazzuhziri ya inganta shi a sahihi Jami’u bayanil ilmi wafadhlihi na Ibnu Abbdulbarr 39(6) ka ga idan ya mutu a wannan hanya ana fatan ya yi kyakykyawar cikawa(7) Tirmizi ne ya rawaito a babin falalar neman ilimi hadisi na 2645 kuma yace hadisi ne mai kyaukuma ingantacce.(8) Tirmizi ne ya rawaito a babin falalar neman ilimi hadisi na 2645 kuma yace hadisi ne mai kyaukuma ingantacce.(9) Duba tazkiratussaami’i na Ibnu jama’a, tah}i}in Ihsan abdulmannan shafi na 25(10) Duba tazkiratussaami’i na Ibnu jama’a, tah}i}in Ihsanabdulmannan shafi na 26(11) Duba tazkiratussaami’i na Ibnu jama’a, tah}i}in Ihsanabdulmannan shafi na 27NEMAN ILIMI A MUSULUNCI3 Kuma ilimi ba zai gushe yana ]aukaka shi ba, har sai manyan mutane sungirmama shi. Kuma a ]auki maganarsa a ko’ina, kai wanda ya zama Malami shi ne shugaba. Ba dan ilimi ba da wasu rayuka ba su ji da]i ba, kuma da ba’a tantancetsakanin halal da haram ba.(12)Daga cikin abin da yake nunamana mahimancin ilimi shi ne, ku]i idan kana kashe suraguwa suke yi amma ilimi duk lokacin da kake ba da shi}aruwa yake yi, sannandukiya Allah (s.w.t.) yana bada ita ga wanda yake so dawanda ba ya so, amma ilimimai amfani Allah (s.w.t.) ba ya ba da shi sai ga wanda ya nufe shi da alkairi, kamaryadda Annabi s.a.w yake cewa (wanda Allah (s.w.t.) ya nufi alkairi da shi sai yafahimtar da shi addini)(١٣)Kuma ilimi shi ne abin da ko da ka mutu Allah (s.w.t.) zai cigaba da rubuta makalada mutu}ar ana amfani da shi, Annabi (s.aw.) yana cewa(idan [an’adam ya rasuaikinsa yana yankewa sai abubuwa guda uku, daga cikiakwai ilimin da mutum yakoyar ake amfanuwa da shi)(14) kuma yana cewa (wanda ya kira mutane zuwa shiriyayana da kwatankwacin ladansu)(15) kuma yana cewa mutum ]aya ya shiryu tahanyarka ya fi maka a baka jajayen ra}uma) (16)HUKUNCIN NEMAN ILIMINeman ilimin shari’a ya kasu kashi biyu: akwai wanda yakefardhu kifaya, ma’anaidan wani adadi daga cikin mutane su ka nema ya saraya akan ragowar, akwai kumawanda yake wajibi akan kowa, wannan yana kasancewa a ilimin da mutum ba zai sanubangiji ba sai da shi, ko kuma ba zai iya aikata wata ibada da Allah (s.w.t.) yawajabta masa, ko wata mu’amala ba sai da shi, to anan sai neman ilimi ya zama wajibiakan kowanne musulmi.(17)ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WURIN NEMANILMI1. TSARKAKE NIYYANiyya ita ce }ashin bayan kowanne aiki, duk lokacin da niyya ta samu matsala gaba]ayan aiki sai ya samu matsala, Annabi (s.aw.) yana cewa (dukan ayyuka ba saingantuwa sai da niyya) (18) kuma Sufyan Asthauri yana cewa (babu abin da na yifama da shi irin da niyyata)(19)Don haka ya kamata mai neman ilmi ya zama yana karatunsa ne saboda neman yardarUbangiji, ya wajaba ya dage wurin ya}i da shai]an ya kuma yi }o}arin kautar da dukabin da zai kawo masa na neman shahara da son duniya.Idan ya zama niyyar [alibi shine neman suna da son duniya da kuma neman girma awurin mutane, to ha}i}a ya shigar da kansa cikin ha]ari, Annabi (s.aw.) yana cewa(farkon wanda za a yiwa hukunci ranar Alkiyama dagaciki akwai mutumin da ya(12) sahihi Jami’u bayanil ilmiwafadhlihi na ibnu abbdulbarr 49(13) Bukari da Muslim ne su ka rawaito(14) Muslim ne ya rawaito hadisin 1631(15) ka ga idan ka koyawa mutum dubu sAllah (s.w.t.) misali – kuma ka tsarkake niyyarka- kana da irinladan duk wanda ya yi sAllah (s.w.t.) a cikinsu, Muslim ne ya rawaito hadisin.(16) Duba sahihul Bukhari 2783, da sahihu Muslim 2406(17) Duba kitabu al-ilm na Ibn Uthaimin shafi na 23(18)Bukari da Muslim ne su ka rawaito(19) duba ma’alim fi [ariki]alabil ilmi na Abdulaziz Sadhan 12NEMAN ILIMI A MUSULUNCI4koyi ilimi ya koyar da shi, ya kuma karanta alqur’ani, sai a zo da shi sai Allah (s.w.t.)ya sanar da shi ni’imar da ya yi masa sai ya tabbatar da hakan, sai ya ce to me ka yi daita? Sai ya ce na yi ilimi kumana koyar da shi, na kuma karanta Al-qur’ani sabodakai, sai- Allah (s.w.t.)- ya ce masa ka yi }arya, sai dai kai ka yi ilimi don ace wanemalami ne, ka kuma karanta Al-qur’ani don ace wane makaranci ne, kuma ha}i}a anfa]a, sai a ja shi akan fuskarsa har a jefa shi cikin wuta) (20)Kuma wasu malaman sun fa]a cewa idan bawa ya zamaburinsa a neman ilimi shi nesamun yabon mutane da kuma su dinga yin mamaki ilimin da Allah (s.w.t.) ya ba shi,to ha}i}a ya bu]e wata}atuwar }ofa daga cikin}ofofin riya, Allah (s.w.t.) yakiyaye.Sai dai idan ya zama ya kasa samun tsarkakar niyya to ya cigaba da neman ilmin yanaaddu’a in Allah (s.w.t.) ya so sai ka ga niyyarsa ta tsarkaka, kamar yadda aka rawaitodaga DARA{UDNI ]aya daga cikin manyan malaman hadisi yake cewa (mun nemiilimi ba dan Allah (s.w.t.) ba amma ilimin ya }i sai da ya zama don Allah (s.w.t.))(21)Magabata sun kasance suna nisantar duk abin da zai kai su zuwa ga neman shahara awurin mutane, daga cikin abin da zai nuna mana haka akwai:1. Bishr bin Harith yana cewa(duk wanda yake neman shahara to bai ji tsoranAllah (s.w.t.) ba) (22)2. Akwai lokacin da Imamu Ahmad ya ji yabon da mutane suke yi masa sai yakecewa da ]alibinsa Abubakar, ya kai Abubakar idan mutum ya san kansa tomaganar mutane ba za ta amfane shi ba) (23)3. Akwai lokacin da UMAR Allah (s.w.t.) ya yarda da shi ya ga mutane suna binUbayyu bn ka’ab ]aya -daga cikin sahaban Annabi (s.aw.)-sai ya dakawaUbayyu tsawa ya ce (ka dainawannan, saboda fitina ne ga wanda ake bi, kuma}as}anci ne ga wanda yake bi) (24)2. KURUCIYALokacin kuruciya lokaci ne muhimmi a rayuwar]an’adam wanda ya kamata mutumya yi amfani da shi wurin neman ilimi, saboda duk lokacin da mutum ya girmamatsaloli su ka yi masa yawasai ka ga ya kasa neman ilimiyadda ya kamata ko kumaidan ya haddace ya manta dawuri, amma idan yana yaro za ka ga duk abin da akakoya masa ya ri}e da wuri kuma ya zauna daram, Annabi (s.aw.) yana cewa (ka ribaciabubuwa biyar kafin abubuwa biyar, (25) samartakarka kafin tsufanka, lafiyarka kafinrashin lafiyarka, wadatarka kafin talaucinka, lokacin da ka sami dama kafin lakacin daabubuwa za su yi maka yawa,da rayuwarka kafin mutuwarka) (26) kuma an rawaitodaga Hasan yana cewa (neman hadisi mutum yana}arami kamar rubutu ne a kandutse)(27)(20) Hakim ya rawaito shi a Mustadrak 2120 kuma albani ya inganta shi a silsila sahiha 220, hadisi na508(21) ma’ana lokacin da s ka yiilimi ba su da cikakken iklasi, bayan sun yi ilimi sai Allah (s.w.t.) yasanya musu iklasi, Duba Taskiratussaami’i fi-Adabi Al’alim wal-muta’allim na IbnJama’a 42(22) duba siyar aalamin nubala’a na Zahbi 11216(23) duba siyar aalamin nubala’a na Zahbi 11211(24) duba ma’alim fi [ariki]alabil ilmi na Abdulaziz Sadhan 15(25) ma’ana kafin abubuwa biyar su hana ka ribatarsu(26) Hakim ya rawaito shi a mustadrak4306, kuma Albani ya inganta shi, duba sahihil jaami’i hadisi na1088(27) Duba Jami’u bayanil ilmi wafadhlihi na Ibnu Abdulbarr 99NEMAN ILIMI A MUSULUNCI5Magabata sun kasance suna bawa lokacin yarinta mahimmancin gaske, zaka gatunyaro yana ]an }arami ya haddace alqur’ani, misali irinsu imamul Bukhari ya haddace{ur’ani tun yana shekara bakwai, duk da cewa irin cigaban da mu ka samu a wannanzamanin su ba su same shi ba, kamar kaset da computerda talabijin da sauranabubuwan zamani wa]anda suke sawwake karatu, duk dawa]annan abubuwa za kaga wasu daga cikinmu suna sakaci da lokacin }uruciyar yaransu, har za ka ga wasusun fi damuwa yaro ya je ya yi wasa a mafi yawan lokutansa tare da yara a irinwannan lokaci mai mahimmanci, wani bawan Allah (s.w.t.) yana cewa:ومن فاتھ التعلیم وقت شبابھ فكبر علیھ أربعا لمماتھMa’ana: Duk wanda neman ilimi ya wuce shi lokacin da yake da kuruciya, to ka yimasa salllar gawa, saboda yariga ya mutu.Abu abdullahi nuk]awaihi kuma yana cewa:أراني أنسى ما تعلمت فيالكبر و لست بناس ما تعلمت في الصغرMa’ana: Nii naga duk abin da na koya bayan na girma sai na manta, amma duk abindana koya ina yaro bana mantawa.(28)Umar – Allah (s.w.t.) ya yardada shi- yana cewa (ku yi ilimi tun kafin a shugabantarda ku). (29)Ya kai ]an’uwana ka yi }o}ari wurin amfani da kuruciyarka tun kafin matsaloli su yimaka yawa, Imamush Shafi’i yana cewa (da an ]ora min siyan albasa da ban haddacekoda mas’ala ]aya ba) (30)kafin kuma ka yi nadama kamar yadda mutane da yawa suka yi nadama, kamar yaddawani bawan Allah (s.w.t.) yake cewa:مع الثمانین عاث الضعف في جسدي وساءني ضعفرجلي واضطراب یديإذاكتبت فخطي خط مضطرب كخط مرتعش الكفین مرتعدفاعجب لضعف یدي عن حملھا قلما من بعد حمل القنا في لبة الأسدفقل لمن یتمنى طول مد تھ ھذي عواقب طول العمر والمددMa’ana: Bayan shekara tamanin rauni ya game jikina, kuma raunin }afata da karkarwarhannuna ya ba}anta min rai. Idan na yi rubutu, sai ka garubutuna irin rubutun mai karkarwar hannu, sai kaga ya zama kamar rubutun mai karkarwar tafikan hannu Yi mamakin hannuna wurinkasa ]aukar al}alami, saboda rauninsa, bayan DAita ce take ]aukar mashi ta harba shi a wuyan zaki. Ka gayawa wanda yake sontsawon rayuwa, wannan shi ne }arshen tsawonrayuwa.Sai dai idan Allah (s.w.t.) ya sa ba ka samu ka yi karatun tun ka na }arami ba wannanba ya nuna yanke }auna daganeman ilimi, kamata yayi ka nemi taimakon Allah(28) Duba Jami’u bayanil ilmi wafadhlihi na Ibnu Abdulbarr 88(29) Duba Jami’u bayanil ilmi wafadhlihi na Ibnu Abdulbarr 89(30) Abin da yake nufi da ]oramasa matsalolin yau da kullum a kansa da bai iya yin karatu ba, Dubatazkiratussaami’i na Ibnu jama’a, tah}i}in Ihsan abdulmannan shafi na 81NEMAN ILIMI A MUSULUNCI6(s.w.t.) ka daure ka nema, kamar yadda wasu magabataba su fara neman ilimi ba saida su ka girma- kamar irin suALIYU BN HAZM- kuma suka zama manyan malamaiwa]anda musulmi suke ji da su.3. YIN AIKI DA ABIN DA MUTUM YA KARANTAYin aiki da ilimi yana daga cikin abubuwan da suke taimakawa wurin ri}e ilimi dakuma kiyaye shi, kamar yadda rashin aiki da shi yanadaga cikin abubuwan da sukekwashe albarkar ilimi.Saboda haka magabata su kakasance sun fi kowa kwa]ayi warin aiki da ilimi,Abdullahi ]an Mas’ud Allah (s.w.t.) ya }ara masa yarda yana cewa ( [aya dagacikinmu -sahaban Annabi (s.aw.)- ya kasance idan ya koyi ayoyi goma baya ketare suhar sai ya san ma’anoninsu kuma ya yi aiki da su.)Domin ilimi da aiki ‘yan’uwanjuna ne ko dai su ha]u gaba]aya ko kuma a ce babusu gaba ]aya, saboda idan aka samu ilimi babu aiki sai ilimi ya zama hujja akanwanda ya yi shi, kuma an rawaito daga Imamu Ahmad Allah (s.w.t.) ya yi masarahama yana cewa (ban ta~a haddace hadisi ba face sai nayi aiki da shi) shi ya sa zamu ga Imamu Ahmad yana daga cikin wa]anda su ka fi kowa hadda, kamar yaddaAbi Zur’a ya fa]a: imamu Ahmad ya haddace hadisai miliyan ]aya.Kuma Jundub bn Abdullahi yana cewa: (misalin wanda ya ke yiwa mutane wa’aziyana mantawa da kansa, kamar fitila ce ta }ona kanta, ta haskaka wani gurin) (31)Wannan ilimi da Allah (s.w.t.)ya bamu yana bu}atar zakka, zakkar ilimi ita ce yinaiki da shi, kuma gwargwadon yadda kake masa zakka gwargwadon yadda za kahaddace shi.4. NEMAN TAIMAKON ALLAH(S.W.T.) DA KUMA RASHIN YANKE{AUNAMai neman ilimi ya dinga tunawa cewa Allah (s.w.t.) shine MASANI kuma shine mai sanar da kowa, don haka ya dinga neman taimako a wurinsa yana rokonsaya bu]a masa basira, musamman a lokutan da akeamsa addu’a, daga cikinaddu’o’in da Annabi (s.aw.) yake yi da safe yana cewa:أللھم إني أسألك علما نافعا ورزقا طیبا وعملا متقبلاMa’ana:“Ya Allah (s.w.t.) ina ro}onKa ilimi mai amfani, da arziki mai kyau, da aiki”kar~a~~e.Kuma Allah (s.w.t.) ya umarcimanzonSa da ya ro}e shi}arin ilimi kamar yaddaAllah (s.w.t.) yake cewa a cikin alqur’ani:(وَقُلْ رَبِّ زِدْنِي عِلْماً)Ma’ana:“Ka ce Ubangijina ka }ara min ilimi” (32)sannan wasu daga cikin magabata sun kasance idan wata mas’ala ta yi musu wahalarfahimta sai su yi ta addu’a har Allah (s.w.t.) ya fahimtar da su, su cigaba da yi har susamu bu]i daga Allah (s.w.t.).Sannan kuma kar ka yanke}auna daga zama malami, ka dinga tuna cewa kowalokacin da Allah (s.w.t.) ya fito da shi daga cikin mahaifiyarsa bai san komai ba,kamar yadda Allah (s.w.t.) yake cewa:(31) Duba Jami’u bayanil ilmi wafadhlihi na ibnu abbdulbarr 236(32) suratu Dhaha aya ta 114NEMAN ILIMI A MUSULUNCI7( وَاللَّھُ أَخْرَجَكُمْ مِنْ بُطُونِ أُمَّھَاتِكُمْ لا تَعْلَمُونَ شَیْئاً)ma’ana:(Allah (s.w.t.) shi ne wanda ya fitar da ku daga cikin uwayenku ba ku san komaiba)(33)Yanke }auna na daga cikin abubuwan da suke hana samun ilimi yadda ya kamata, koda Allah (s.w.t.) ya jarrabe kada rauni wurin haddace abubuwa ka da ka yanke}auna, idan ka tsarkake niyyarka, sai ka ga Allah (s.w.t.) ya taimake ka, musammanidan Allah (s.w.t.) ya taimake ka da yawan maimaita abin da ka haddace, an tambayiImamul Bukhari cewa menene maganin mantuwa? Sai ya ce yawan karatu a cikinlittattafai.Daga cikin kuma abin da zai taimaka maka shi ne barin zunubai, Imamu Shafi’i yanacewa:شكوت إلى وكیع سوء حفظي فأرشدني إلى ترك المعاصيوقال اعلم بأن العلم نور ونورالله لا یؤتاه عاصيMa’ana: Na kai }arar munin haddata wurin waki’u, sai ya shiryar da ni zuwa barinzunubai. Kuma yace ka sani ilimin haske ne, hasken Allah (s.w.t.) ba’a bawa maisa~o.(34)Sannan kar ka jinkirta nemanilimi zuwa wani lokaci na musamman, kar ka ce sailokaci kaza zan fara, saboda ajalinka zai iya zuwa ba ka sani ba, kamar yaddawasu mutanen suke yi idan aka yi musu maganar nemanilimi sai ya ce misalishekara mai zuwa zan fara, wannan kuskure ne saboda shekarar za ta iya zuwa dawasu abubuwa wa]anda za su hana shi neman ilimin.Kuma wa]annan kwanakin, da suke zuwa su wuce ba za su ta~a dawowa ba,kamar yadda kowa ya sani, Hasanul Basari yana cewa (ya kai ]an Adam ba waniabu ba ne kai illa kwanaki, duk lokacin da kwanaki su ka tafi, to wani ~angarenkaya tafi).(35)Da fatan za mu yi amfani da lokutan wurin neman abin dazai amfane mu, kar mushagala da yawan ziyara da zantuttukan da ba za su amfane mu ba, kamar yaddaAnnabi (s.aw.) yake cewa (wanda ya yi imani da Allah (s.w.t.) da ranar lahira, toya fa]i alkhairi ko kuma ya yi shiru)(36)5. YAWAN MAIMAITAWAZarnuuji yana cewa: ya kamata ]alibin ilimi ya dinga maimaita karatun jiya sau biyar,karatun shekaran jiya sau hu]u, yinin da yake gabanin wannan kuma sau uku, wanda(33) suratun nahli aya ta78(34) wasu suna kokwanto danganta wa]annan baitika zuwa ga Shafi’i suna cewa ba ya cikin [alibanWaki’u , wannan maganar ba daidai ba ce saboda Shafi’i yarawaito daga WAKI’U kamar yadda za muga haka a cikin kitabussada}at a cikim AL-UMM, kuma wa]annan baitikan sun shahara daga Shafi’i,duba ma’alim fi [ariki ]alabil ilmi na Abdulaziz Sadhan shafi na 27(35) duba hilyatu Al-auliya’a na Asfahani 2147(36) duba Bukhari hadisi na 5672, da Muslim a babin dhiyafa hadisi na 48

Reply Edited on 04/02/2015 10:09 AM.

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

amfanin ingan tacciyar aqida

from nuramuhd3 on 04/02/2015 09:19 AM

AMFANIN INGANTACCIYAR AQIDA TA IMANI A RAYUWAR BAWA: Allah (T) ya wajabta mana yinImani da shi, tare da qudrta Aqidu na Imanin wadanda duka asalinsu shi ne; Imani da Allah da abin da ya saukarwa Annabawa da Manzanninsa.Allah ya ce:{قُولُوا آمَنَّا بِاللَّهِ وَمَا أُنْزِلَ إِلَيْنَا وَمَا أُنْزِلَ إِلَى إِبْرَاهِيمَوَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَالْأَسْبَاطِ وَمَا أُوتِيَ مُوسَى وَعِيسَى وَمَا أُوتِيَ النَّبِيُّونَ مِنْ رَبِّهِمْ لَانُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِنْهُمْ وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ } [البقرة: 136]“Ku ce: mun yi imani da Allahda abin da ya saukar zuwa garemu, da abin da ya saukar zuwa ga Annabi Ibrahim, da Isma’il, da Ishaq,da Ya’aqub, da Asbat (‘ya’yan Annabi Ya’aqub) da abin da aka bai wa Annabi Musa da Isa, da abin da aka bai wa Annabawa daga wajen Ubangijinsu, ba za mu banbace tsakanin daya daga cikinsu ba, kuma mu masu mika wuya ne gare shi (Allah)”.A cikin Al- Qur’ani mai girma akwai ayoyi masu yawa da suka zo suna sharhin wadannan rukunnai na Imani, da kuma bayaninsu dalla – dalla, ayoyin sun zo suna bayanin Sunayen Allah da Siffofinsa da aiyukansa dani’imominsa, kuma sun zo suna bayanin yanayin ranar Qiyama da abin da yake cikinta na hisabi da adalcin Allah da falalarsa da sakamakon lada da na azaba,kuma sun zo suna bayanin halayen Manzanni da siffofinsu da shiryarwansu da bayanin abin da suka yi kira zuwa gare shi, da bayanin littatafan da aka saukar musu, da abin da ke cikinsu na ilimummuka masuamfani da shiryarwa nau’i daban – daban.Lallai a cikin wannar ayar Allah ya hada umurni da aka fiskantar da shi ga zahiri da kuma badini, na zahiri shi ne fadin imani da yin ikrari da shi a baki, na badini kuwa shine tabbatar da dukkan wadannan ginshikai na imania cikin zuciya. Kuma a cikin ayar ya hada da umurni da kaskantar da kai ma Allah da mika wuya gare shi a bayyane da boye; a zahiri da badini, da kuma cikakken Ikhlasi ga Allah a dukkan hakkokin Addini.Wadannan Aqidu Ingantattu masu matukar amfani, suna cika zukatan muminai da aminci da imani da yakini da haske da shiriya, da kuma bautar Allah da komawa gareshi a dukkan halaye, da fakewa da shi a dukkan bala’ida masifa, da kuma samun nitsuwa ta hanyar saninsa dasamun kwanciyar hankali ta hanyar ambatonsa da yabo agare shi.Kuma wannan Aqida ta Imani tana bai wa bawa karfin tawakkali ga Allah da cikakken dogaro gare shi, da neman taimakonsa wajen aikata aiyukan duniya da na Addini.Lallai wannan Imani na gaskiya da yaqini ingantacce yana sa bawa ya samu karfi da izza da jarumtaka a Magana da aiki, saboda duk lokacin da bawa ya samu yaqinin Allah ne kawai mai amfanarwa kuma mai cutarwa, kuma mai bayarwa mai hanawa, kuma ya san cewa; wanda ya nemi daukaka da shi shi ne madaukaki, wanda kuma ya dogara ga waninsa shi ne makaskanci, kuma ya san cewa; lallai halitta gaba daya mabukata ne zuwa ga Allah, ba sa iya amfanar da wani bare su cutar da shi, wannanzai sa masa jin karfi da Allah,da kuma dogaro gare shi, kuma ba zai ji tsoron komai ba sai Allah, kuma ba zai yi tsammanin wani alheri ba sai a wajensa, kuma ba zai yi kwadayin komai ba sai daga falalarsa.Daga littafin Sheikh Ibnu Sa’adiy (r): Al- Riyadhun Nadhirah.

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

shi a da kafieta musulmi

from nuramuhd3 on 04/02/2015 09:18 AM

SHI’A DA KAFIRTA MUSULMI!!!Bismillahi, wa sallallahu a’la nabiyyina Muhammad, wa a’la Alihi wa Ashabihi.Duk mai bibiyar tattaunawar da ake yi tsakanin ‘yan shi’a yan sha biyu da yan uwa Ahlus-Sunnah a kafofin sada zumunci ( kamar ; facebook )zai ga yadda yan shi’a suke yawan tuhumar Ahlussunnahda cewa suna kafirta musulmi, wani lokacinma ba a kan wannan abu ake tattaunawar ba, amma sai sun san yadda suka lankwaso zance, suka karkatar da hankulan mutanezuwa ga waccan tuhuma ta karya, maras asali a cikin littattafan Sunnah.Amma abin da zai baka mamaki shi ne a duk cikin kungiyoyin addini babu kungiyar da ta kai shi’a kafirta musulmi, tare da zagi da cin mutuncin bayin Allah, wannan abu ne da yake kunshe a cikin manya-manyan littattafansu, ba wai tuhuma ba ce ta karya marasasali irin wadda suke wa Ahlus-Sunnah, don haka ma bari mu kawo kadan daga cikin irin dimbin riwayoyinsuda suke tabbatar da haka, watakila wasu daga cikinsu wadanda aka rude su da karya da takiyya su sake nazari, su fahimci gaskiya.1- Babban malaminsu al-Kulainiy ya kawo riwaya a cikin littafinsa mai suna (al-Kafi 8/246) daga limaminsu muhammad Al-bakir yana cewa, “Mutane sun yi ridda bayan Annabi s.a.w sai mutum uku, al-Mikdad ‘dan Aswad, da Salman al-Farisiy, da Abu Zarril Gifari”.2 – hakanan dai ya zo a cikin (al-Kafi 1/233) Imaminsu ar-Ridha yana cewa “Babu wanda yake kan addinin Musulunci wanda ba mu ba kuma ba ‘dan shi’armu ba”.3 – A wata riwayar a cikin (ar-Raudatu Minal Kafi 8/2109) daga limaminsu Abu Ja’afar yana cewa, “Ya kai Abu Hamza wallahi dukkan mutane gabadayansu yan zina ne banda yan shi’armu”.4- Babban Malaminsu Ni’imatullahi al-Jaza’iriy yana bayanin hukuncin Nawasib – wato a nufinsu Ahlussunnah – ya ce ” Kafirai ne su, najasace da IJMA’IN DUKKAN MALAMAN SHI’A IMAMIYYAH, sun fi yahudu da nasara sharri. Alamar Nasibi kuwa ita ce gabatar dawanin Aliyyu a wajen khalifanci”. Duba : (al-Anwarun Nu’umaniyya 2/206 – 207).Wannan kadan kenan daga cikin irin riwayoyi da dimbin maganganun malaman shi’a a kan kafirta duk wanda ba dan shi’a ba. kuma wannan ita ce akidar duk wani ‘dan shi’a na gaskiya, shi ne yana ganin kafircin wanda duk ba shi’a ba ne, kai yana ganinsa ‘dan zina ne, kamar yadda muke gani suna rubutawa a kafafe kamar facebook yayin tattaunawa da su.A bangare guda kuma baza ka samu irin wannan kafirtawar ba a litattafan Sunnah, kai hatta shehun Musulunci Ibnu Taimiyyah da Shehun musulunci Muhammad Bin Abdulwahhab, wadanda kullum ake tuhuma, hadi da yi musu karyar cewa su suka kawo kafirta musulmi, ba za ka taba samun irin wannan acikin litattafansu ba, sai dai alankwasa musu magana ko a yi mata mummunar fahimta.Allah Ka tsare mu daga bata, Ka dora mu akan madaidaiciyar hanya.

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

aqidan shi'a 3

from nuramuhd3 on 04/02/2015 09:15 AM

AK’IDUN SHI’A IMAMIYYA AL-ITHNAI ASHARIYYA A SAUK’AK’E (KA SAN GASKIYA DA ‘BATA) (3)بسم الله الرحمن الرحيماللهم صل على محمد وعلى آله وسلم-TAMBAYA TA 17:SHIN ‘YAN SHI’A SUNA DA ILMIN MUS’DALAHUL HADISIKUWA, WATO ILMIN TANTANCE HADISAI DON SANIN INGANTACCEN HADISI DA HASAN DA DA’IF?AMSA: WANNAN ILMI NA MUS’DALAHUL HADIS, SABO NE A WAJENSU. SUN KWAFO SHI NE DAGA LITTATAFAN AHLUS SUNNA. SUKA CE:( ﻭﺍﻟﻔﺎﺋﺪﺓ ﻓﻲ ﺫﻛﺮﻩ -ﺃﻱ ﺍﻟﺴﻨﺪ- ﺩﻓﻊ ﺗﻌﻴﻴﺮ ﺍﻟﻌﺎﻣﺔ -ﺃﻱ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ- ﻟﻠﺸﻴﻌﺔ، ﺑﺄﻥ ﺃﺣﺎﺩﻳﺜﻬﻢ ﻏﻴﺮ ﻣﻌﻨﻌﻨﺔ، ﺑﻞ ﻣﻨﻘﻮﻟﺔ ﻣﻦ ﺃﺻﻮﻝ ﻗﺪﻣﺎﺋﻬﻢ ).SUKA CE: FA’IDAR AMBATON ISNADI SHI NE; DON KAWAR DA AIBANTAWAR AHLUS SUNNA NE GA ‘YAN SHI’A. AHLUS SUNNAN ZA SU CE; HADISANSU BA MASU “AN’ANA” BA NE, (MARASA HA’DADDEN ISNADI). SAI DAISUN ‘DAUKOSU NE DAGA LITTATAFAN MAGABATANSU”. (SA’BANIN NA ‘YAN SHI’A DA BA SU DA ISNADI, SAI DAI KA JI ANCE: DAGA ABI ABDILLAHI … KAWAI BA TARE DA ISNADI BA”.KUMA DU SUKA CE:( ﻭﺍﻻﺻﻄﻼﺡ ﺍﻟﺠﺪﻳﺪ ﻣﻮﺍﻓﻖ ﻻﻋﺘﻘﺎﺩ ﺍﻟﻌﺎﻣﺔ ﻭﺍﺻﻄﻼﺣﻬﻢ، ﺑﻞ ﻫﻮ ﻣﺄﺧﻮﺫ ﻣﻦ ﻛﺘﺒﻬﻢ ﻛﻤﺎ ﻫﻮ ﻇﺎﻫﺮ ﺑﺎﻟﺘﺘﺒﻊ ).“SABON IS’DILAHI (WATO MUS’DALAHUL HADIS), YA DACE DA AK’IDAR AHLUS SUNNA, DA IS’DILAHINSU. KAI, BAYAN AN YI BINCIKE YA BAYYANA CEWA; DAGALITTATAFANSU MA AKA ‘DAUKO SHI”.DUBA : WASA’ILUSH SHI’A 20/ 100.WANNAN YAKE NUNA MAKACEWA; ‘YAN SHI’A BA SU DA WANI MIZANI NA TANTANCERUWAYOYI, DON HAKA KOWANE MAK’ARYACI SAI YAZO YA CE: ABU ABDILLAHI YACE: KAZA… SU KUMA YUU DAGUDU DA RAWAR JIKI SU RIK’A A MATSAYIN ADDINI. SHI YA SA ADDININ SHI’A, YASA’BA MA HANKALI BARE KUMA ADDININ MUSLUNCI, SABODA ADDINI NE DA ZINDIK’AI SUKA K’IRK’IRE SHI!-TAMBAYA TA 18:MENENE AK’IDAR MALAMANSHI’A GAME DA TAUHIDUL ULUHIYYA, (KA’DAITA ALLAH DA BAUTA)?AMSA: MALAMAN SHI’A SUNA GANIN CEWA: -WAI- BA DON IMAMANSU BA, DA KWATA-KWATA BA A BAUTA MA ALLAH BA. SUKA CE -WAI- ABU ABDILLAHI YA CE:( ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺧﻠﻘﻨﺎ ﻭﺻﻮﺭﻧﺎ ﻓﺄﺣﺴﻦ ﺻﻮﺭﻧﺎ، ﻭﺟﻌﻠﻨﺎ ﻋﻴﻨﻪ ﻓﻲ ﻋﺒﺎﺩﻩ، ﻭﻟﺴﺎﻧﻪ ﺍﻟﻨﺎﻃﻖ ﻓﻲ ﺧﻠﻘﻪ، ﻭﻳﺪﻩ ﺍﻟﻤﺒﺴﻮﻃﺔ ﻋﻠﻰ ﻋﺒﺎﺩﻩ ﺑﺎﻟﺮﺃﻓﺔ ﻭﺍﻟﺮﺣﻤﺔ، ﻭﻭﺟﻬﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺆﺗﻰ ﻣﻨﻪ، ﻭﺑﺎﺑﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻴﻪ، ﻭﺧﺰﺍﻧﻪ ﻓﻲ ﺳﻤﺎﺋﻪ ﻭﺃﺭﺿﻪ، ﺑﻨﺎ ﺃﺛﻤﺮﺕ ﺍﻷﺷﺠﺎﺭ ﻭﺃﻳﻨﻌﺖ ﺍﻟﺜﻤﺎﺭ، ﻭﺟﺮﺕ ﺍﻷﻧﻬﺎﺭ، ﻭﺑﻨﺎ ﻳﻨﺰﻝ ﻏﻴﺚ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ، ﻭﻳﻨﺒﺖ ﻋﺸﺐ ﺍﻷﺭﺽ، ﻭﺑﻌﺒﺎﺩﺗﻨﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻟﻮﻻﻧﺎ ﻧﺤﻦ ﻣﺎﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ).YA CE: LALLAI ALLAH YA HALICCE MU, YA SURANTAMU, YA KUMA KYAUTATA SURAR TA MU, SAI YA SA MU MUKA ZAMA IDONSA A CIKIN BAYINSA, MUKA ZAMA HARSHENSA MAI MAGANA A CIKIN HALITTANSA, HANUNSA BU’DA’D’DE DA TAUSAYI DA RAHAMA A KAN BAYINSA DAFISKARSA DA AKE ZUWA TA WURINSA, DA K’OFARSA DA YAKE NUNI ZUWA GARE SHI, KUMA MASU KULA DA TASKOKINSA A CIKIN SAMANSA DA CIKIN K’ASANSA, DA MU NE BISHIYOYI SUKE YIN ‘YA’YA, DA MU NE ‘YA’YAN BISHIYA SUKE NUNA, DA MU NE RAFUKA SUKE GUDANA, DA MU NE RAWAN SAMA YAKE SAUK’A DAGA SAMAN, KUMACIYAYI SUKE TSIROWA, DA BAUTARMU AKA BAUTA MA ALLAH, KUMA BA DON MU BA DA BA A BAUTA MA ALLAH BA!!!”.DUBA : USULUL KAFIY 1/ 144.TIR DA WANNAR MUGUNYAR MAGANA!INA MASU HANKALI DAGA CIKIN ‘YAN SHI’A???-TAMBAYA TA 19:SHIN MALAMAN SHI’A SUNA DA AK’IDAR HULULI DA ITTIHADI, (MA’ANA; ALLAH YA SHIGA JIKIN IMAMAI. KO KUMA YA HA’DE DA SU. KAMAR AK’IDAR KIRISTOCI)?AMSA: LALLAI SUNA DA WANNAR AK’IDA TA HA’DUWAR ALLAH DA IMAMAI, BAYAN AK’IDAR SHIGANSA JIKIN ALIYU (RA).SUKA CE: – WAI- ABU ABDILLAHI YA CE:( ﺛﻢ ﻣﺴﺤﻨﺎ ﺑﻴﻤﻴﻨﻪ ﻓﺄﻓﻀﻰ ﻧﻮﺭﻩ ﻓﻴﻨﺎ ).YA CE: -WAI- SA’ANNAN ALLAH YA SHAFEMU DA HANUNSA NA DAMA, SAI YA SHIGAR DA HASKENSA A CIKINMU”,DUBA : USULUL KAFIY 1/ 440.A WATA RUWAYAR:( ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺧﻠﻄﻨﺎ ﺑﻨﻔﺴﻪ ).– WAI- YA CE: ALLAH YA HA’DU/ YA CAKU’DU DA MU DA KANSA”,DUBA : USULUL KAFIY 1/435.AS-SADIK’ – WAI- YA CE:( ﻟﻨﺎ ﻣﻊ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﺎﻻﺕ: ﻧﺤﻦ ﻓﻴﻬﺎ ﻫﻮ، ﻭﻫﻮ ﻧﺤﻦ، ﺇﻻ ﺃﻧﻪ ﻫﻮ ﻫﻮ، ﻭﻧﺤﻦ ﻧﺤﻦ ).YA CE: MUNA DA WASU YANAYI TARE DA ALLAH; A CIKINSU MU SHI NE, SHI KUMA MU NE. SAI DAI SHI SHI NE, MU KUMA MU NE”.DUBA : SHARHU ZIYARATIL JAMI’ATIL KABIRA NA AYATULLAHI KHU’IY, SHAFI NA 107.WANNAR ITA CE AK’IDAR ITTIHADI (CUKU’DUWAN ZATIN ALLAH A CIKIN ZATIN IMAMAI) A WAJEN MALAMAN SHI’A.JAMA’A KO SHAKKA BABU, WANNAR AK’IDA KAFIRA CE!-TAMBAYA TA 20:MENENE MA’ANAR AYOYIN TAUHIDI DA SHIRKA A WAJEN MALAMAN SHI’A?AMSA: ABIN DA AYOYIN SUKE NUFI A WAJEN MALAMAN SHI’A, SHI NE TABBATAR DA IMAMANCI ALIYU (RA).GA K’A’IDARSU A WANNAN BABIN:( ﺃﻥ ﺍﻷﺧﺒﺎﺭ ﻣﺘﻀﺎﻓﺮﺓ ﻓﻲ ﺗﺄﻭﻳﻞ ﺍﻟﺸﺮﻙ ﺑﺎﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﺸﺮﻙ ﺑﻌﺒﺎﺩﺗﻪ: ﺑﺎﻟﺸﺮﻙ ﻓﻲ ﺍﻟﻮﻻﻳﺔ ﻭﺍﻹﻣﺎﻣﺔ، ﺃﻱ : ﻳﺸﺮﻙ ﻣﻊ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻣﻦ ﻟﻴﺲ ﻣﻦ ﺃﻫﻞ ﺍﻹﻣﺎﻣﺔ، ﻭﺃﻥ ﻳﺘﺨﺬ ﻣﻊ ﻭﻻﻳﺔ ﺁﻝ ﻣﺤﻤﺪ ﻉ ﻭﻻﻳﺔ ﻏﻴﺮﻫﻢ )SUKA CE: LALLAI RUWAYOYI SUN ZO DA YAWAN GASKE DA TAWILIN SHIRKA MA ALLAH, DA SHIRKA A CIKIN BAUTARSA. ANA TAWILINSU DA SHIRKA A WILAYA DA IMAMA, MA’ANA; YA HA’DA WANDA BAI CANCANCI IMAMANCI BA TARE DA IMAMI. KUMA YA KAR’BI WILAYAR WANIN IYALAN MUH’D TARE DA NASU”.DUBA : MIR’ATUL ANWAR NAAMILIY, SHAFI NA 202.JAMA’AR MUSULMI KU DUBAYADDA SHI’A SUKE WARGI DA KALAMAIN ALLAH DA TAWILIN SHIRKAN DA ALLAHYA AMBATA A CIKIN K’UR’ANI. DON HAKA SHIRKAA WAJENSU SHI NE HA’DA IMAMI DA WANI WANDA BAI CANCANCI IMAMANCIN BA A WURINSU BA A MUSULUNCI BA. MISALAN TAWILIN NA SU GA AYOYIN K’UR’ANIN, FADIN ALLAH TA’ALAH:(( ﻭﻟﻘﺪ ﺃﻭﺣﻲ ﺇﻟﻴﻚ ﻭﺇﻟﻰ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻚ ﻟﺌﻦ ﺃﺷﺮﻛﺖ ﻟﻴﺤﺒﻄﻦ ﻋﻤﻠﻚ ﻭﻟﺘﻜﻮﻧﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﺎﺳﺮﻳﻦ)).“HAK’IK’A AN YI WAHAYI ZUWA GAREKA DA WA’DANDA SUKA GABACEKA; INA RANTSUWA IDAN KA YI SHIRKA MA ALLAH, LALLAI AIKINKA ZAI ZUBE KUMA LALLAI ZAKA KASANCE A CIKIN MASU HASARA”.MA’ANAR WANNAR AYAR A WAJENSU ITA CE:* ( ﻟﺌﻦ ﺃﻣﺮﺕ ﺑﻮﻻﻳﺔ ﺃﺣﺪ ﻣﻊ ﻭﻻﻳﺔﻋﻠﻲ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻙ، ﻟﻴﺤﺒﻄﻦ ﻋﻤﻠﻚ )-WAI- “IDAN KA YI UMURNI DA SHUGABANCIN WANI TARE DA SHUGABANCIN ALIYU (RA) A BAYANKA, LALLAI AIKINKA ZAI ‘BACI ….”DUBA : USULUL KAFIY 1/ 427.*SUN CE: – WAI- ABU ABDILLAHI YA CE A FA’DIN ALLAH (T):(( ﺃﺀﻟﻪ ﻣﻊ ﺍﻟﻠﻪ (( ﺃﻱ : ﺇﻣﺎﻡ ﻫﺪﻯﻣﻊ ﺇﻣﺎﻡ ﺿﻼﻝ ).“SHIN AKWAI WANI ABIN BAUTA A TARE DA ALLAH? -WAI- MA’ANAR ITA CE: IMAMIN SHIRIYA TARE DA IMAMIN ‘BATA”DUBA : BIHARUL ANWAR 23/ 391. DA KANZU JAMI’IL FAWA’ID SHAFI NA 207.TO JAMA’A, KUN GA FA YADDA BATATTU SUKE WASADA AYOYIN ALLAH, SABODA ASALI DA MA BA SU YI IMANI NA HAKIKA DA SU BA.HATTARA DAI MA SU HANKALI DAGA CIKIN ‘YAN SHI’A!-TAMBAYA TA 21:MENENE K’A’IDAR KAR’BAN AIKI A AK’IDAR MALAMAN SHI’A?AMSA: KA’IDAR KAR’BAN AIKIN BAWA A WURINSU ITACE; IMANI DA IMAMANCIN IMAMANSU.MA’ANA; DUK WANDA BAI YIIMANI DA IMAMANCIN IMAMANSU BA, TO BA ZA A KAR’BI AIYUKANSA BA.SUN RUWAITO CEWA:( ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ﻧﺼﺐ ﻋﻠﻴﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻋﻠﻤﺎ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ ﺧﻠﻘﻪ، ﻓﻤﻦ ﻋﺮﻓﻪ ﻛﺎﻥ ﻣﺆﻣﻨﺎ، ﻭﻣﻦ ﺃﻧﻜﺮﻩ ﻛﺎﻥ ﻛﺎﻓﺮﺍ، ﻭﻣﻦ ﺟﻬﻠﻪ ﻛﺎﻥﺿﺎﻻ، ﻭﻣﻦ ﻧﺼﺐ ﻣﻌﻪ ﺷﻴﺌﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﺸﺮﻛﺎ، ﻭﻣﻦ ﺟﺎﺀ ﺑﻮﻻﻳﺘﻪ ﺩﺧﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ ).“SUKA CE -WAI- LALLAI ALLAH YA KAFA ALIYU (RA) A MATSAYIN ALAMA A TSAKANINSA DA BAYINSA, DUK WANDA YA SAN SHI TO YA ZAMA MUMINI, WANDA KUMAYA YI INKARINSA TO YA ZAMA KAFIRI, WANDA YA JAHILCE SHI YA ZAMA ‘BATACCE, DUK WANDA YA TSAYAR DA WANI ABU TARE DA SHI TO YA ZAMA MUSHRIKI, DUK WANDA YA ZO DA WILAYARSA KUMA, ZAI SHIGA ALJANNA”.DUBA : USULUL KAFIY 1/ 437.KUMA DAI SUKA RUWAITO:( ﻓﺈﻥ ﻣﻦ ﺃﻗﺮ ﺑﻮﻻﻳﺘﻨﺎ ﺛﻢ ﻣﺎﺕ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﻗﺒﻠﺖ ﻣﻨﻪ ﺻﻼﺗﻪ، ﻭﺻﻮﻣﻪ ﻭﺯﻛﺎﺗﻪ ﻭﺣﺠﻪ، ﻭﺇﻥ ﻟﻢ ﻳﻘﺮ ﺑﻮﻻﻳﺘﻨﺎﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻠﻪ ﺟﻞ ﺟﻼﻟﻪ ﻟﻢ ﻳﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ﺷﻴﺌﺎ ﻣﻦ ﺃﻋﻤﺎﻟﻪ ).SUKA CE, “DUK WANDA YA YARDA DA WILAYARMU (SHUGABANCI) , SA’ANNAN SAI YA MUTU A KANTA AN KAR’BI SALLARSA DA AZUMINSA DA ZAKKARSA DAHAJJINSA. IN KUMA BAI YI IK’RARI DA ITA BA A GABAN ALLAH, ALLAH BA ZAI KAR’BI WANI ABU NA AIKINSA BA”.DUBA : AL- AMALIY NA IBNU BABAWAIHIL K’UMMIY, SHAFI NA 154 – 155.TO JAMA’AR MUSULMI KU LURA DA KYAU KU GANI, ANAN ‘YAN SHI’A SUN SANYA SHARA’DI NE WA ALLAH AKAN KARBAN AIYUKAN BAYINSA, WATO SHARAD’IN KAR’BAN AIYUKA SHI NE “YARDA DA IMAMANCIN IMAMANSU”, WANDA WANNAN AK’IDAR MUSULUNCI BAI KARANTAR DA SHI BA!-TAMBAYA TA 22:MENENE AK’IDAR MALAMANSHI’A GAME DA SAMUWAR TSANI A TSAKANIN ALLAH DA BAYINSA?AMSA: MALAMAN SHI’A SUNYI IMANIN CEWA; IMAMAI SU NE SHAMAKI DA TSANI A TSAKANIN ALLAH DA BAYINSA, SABODA HAKA NE ALMAJLISIY YA CE:( ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻻ ﻳﻬﺘﺪﻭﻥ ﺇﻻ ﺑﻬﻢ، ﻭﺃﻧﻬﻢ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺤﻠﻖ ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺃﻧﻪ ﻻ ﻳﺪﺧﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﺇﻻ ﻣﻦ ﻋﺮﻓﻬﻢ ).YA CE: LALLAI MUTANE BA ZA SU SHIRYU BA SAI DA IMAMAI, KUMA SU NE TSANIA TSAKANIN HALITTA DA ALLAH. KUMA BA WANDA ZAI SHIGA ALJANNA SAI WANDA YA SANSU”.KUMA YA RUWAITO:( ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺹ ﻟﻌﻠﻲ ﻉ: ﺛﻼﺙ ﺃﻗﺴﻢ ﺃﻧﻬﻦ ﺣﻖ : ﺃﻧﻚ ﻭﺍﻷﻭﺻﻴﺎﺀ، ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻙ ﻋﺮﻓﺎﺀ، ﻻ ﻳﻌﺮﻑ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻻ ﺑﺴﺒﻴﻞ ﻣﻌﺮﻓﺘﻜﻢ، ﻭﻋﺮﻓﺎﺀ ﻻ ﻳﺪﺧﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﺇﻻ ﻣﻦ ﻋﺮﻓﻜﻢ ﻭﻋﺮﻓﺘﻤﻮﻩ، ﻭﻋﺮﻓﺎﺀ ﻻ ﻳﺪﺧﻞ ﺍﻟﻨﺎﺭ ﺇﻻ ﻣﻦ ﺃﻧﻜﺮﻛﻢ ﻭﺃﻧﻜﺮﺗﻤﻮﻩ ).-WAI- MANZON ALLAH (SAW)YA CE WA ALIYU (RA): ABUBUWA 3, INA RANTSUWA LALLAI SU GASKIYA NE, KAI DA WASIYYAI A BAYANKA WAKILAI (SANANNU) NE, BA A SANIN ALLAH SAI TA HANYAR SANINKU, KUMA WAKILAN DA BA MAI SHIGA ALJANNA SAI WANDA YA SANKU, KUMA KUKA SAN SHI. KUMA WAKILAI BA WANDA ZAI SHIGA WUTA SAI WANDA BAI SANKU BA, KUMA KUKA NUNA BA KU SAN SHI BA”.A WATA RUWAYAR YA CE:( ﻓﺈﻧﻬﻢ ﺣﺠﺐ ﺍﻟﺮﺏ، ﻭﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻂ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﺨﻠﻖ ).“LALLAI SU NE SHAMAKIN UBANGIJI, KUMA TSANI A TSAKANINSA DA BAYI”.DUBA : BIHARUL ANWAR, 23/97 – 99.MA’ANAN TSANI A TSAKANIN ALLAH DA BAYINSA, SHI NE; BA A IYA SAMUN WANI ABU HAR SAI AN BI TA HANUNSU, KO TA HANYARSU, ALHALI ALLAH YA CE:” ﻭﺇﺫﺍ ﺳﺄﻟﻚ ﻋﺒﺎﺩﻱ ﻋﻨﻲ ﻓﺈﻧﻲ ﻗﺮﻳﺐ ﺃﺟﻴﺐ ﺩﻋﻮﺓ ﺍﻟﺪﺍﻉ ﺇﺫﺍ ﺩﻋﺎﻥ ﻓﻠﻴﺴﺘﺠﻴﺒﻮﺍ ﻟﻲ ﻭﻟﻴﺆﻣﻨﻮﺍ ﺑﻲ ﻟﻌﻠﻬﻢ ﻳﺮﺷﺪﻭﻥ “.“IDAN BAYINA SUKA TAMBAYEKA GAME DA NI, KA CE: LALLAI NI MAKUSACI NE, INA AMSA ADDU’AR MAI ADDU’A IDAN YA ROK’ENI, DON HAKA SU NEMI AMSAWATA, KUMA SU YI IMANI DA NI, DA FATAN ZA SU SHIRYU”.-TAMBAYA TA 23:TA YAYA ANNABAWA SUKA SAMU FALALARSU A WAJEN ALLAH, KUMA MENENE HANYAR SAMUN GANIN ALLAH A BISA AK’IDAR MALAMAN SHI’A?AMSA: MALAMAN SHI’A SUNCE -WAI- ABU ABDILLAHI YA CE:( ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﺍﺳﺘﻮﺟﺐ ﺁﺩﻡ ﺃﻥ ﻳﺨﻠﻘﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻴﺪﻩ ﻭﻳﻨﻔﺦ ﻓﻴﻪ ﻣﻦ ﺭﻭﺣﻪ ﺇﻻ ﺑﻮﻻﻳﺔ ﻋﻠﻲ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ، ﻭﻣﺎ ﻛﻠﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻮﺳﻰ ﺗﻜﻠﻴﻤﺎ ﺇﻻ ﺑﻮﻻﻳﺔ ﻋﻠﻲ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ، ﻭﻻ ﺃﻗﺎﻡ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻴﺴﻰ ﺍﺑﻦ ﻣﺮﻳﻢ ﺁﻳﺔ ﻟﻠﻌﺎﻣﻴﻦ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﺨﻀﻮﻉ ﻟﻌﻠﻲ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ. ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ﺃﺟﻤﻞ ﺍﻷﻣﺮ: ﻣﺎ ﺍﺳﺘﺄﻫﻞ ﺧﻠﻖ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻨﻈﺮ ﺇﻟﻴﻪ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻌﺒﻮﺩﻳﺔ ﻟﻨﺎ )“YA CE: NA RANTSE DA ALLAH, ANNABI ADAMU (AS)BAI CANCANCI ALLAH YA HALICCE SHI DA HANUNSA BA, KUMA YA HURA MA SA RUHI DAGA CIKIN RUHINSA, SAI DA WILAYAR ALIYU (RA). (WATO YARDA DA SHUGABANCINSA), KUMA ALLAH BAI YI MAGANA WA ANNABI MUSA (AS) BA SAI DA WILAYAR ALIYU (RA), KUMA ALLAH BAI TSAYAR WA ANNABI ISA (AS) WATA AYA GA MAKAFI BA, SAI DA K’ASK’ANTAR DA KAI WA ALIYU (RA). SA’ANNAN SAI YA CE: ZAN DUNK’ULA LAMARIN DUKA; BAYI BA SU CANCANCI KALLON ALLAH A WAJENSA BA FACE DA BAUTARSU GAREMU”.DUBA : AL-IKHTISAS NA AL-MUFEED, SHAFI NA 250 DA BIHARUL ANWAR, 26/ 294.-TAMBAYA TA 24:TA YAYA AKA BAUTA MA ALLAH, KUMA AKA SAN SHI, AKA KA’DAITA SHI A WAJEN MALAMAN SHI’A?AMSA: DUKA DA IMAMANSUNE, KAMAR YADDA SUKA CE -WAI- JA’AFARUS SADIK’ YA CE:( ﺑﻨﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺑﻨﺎ ﻋﺮﻑ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺑﻨﺎ ﻭﺣﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﺒﺎﺭﻙ ﻭﺗﻌﺎﻟﻰ ).“YA CE: DA MU AKA BAUTA MA ALLAH, DA MU AKA SAN ALLAH, DA MU AKA KA’DAITAALLAH TA’ALAH”,MA’ANA; IDAN BA SU KA BI BA TO BA KA BAUTA MA ALLAH BA, KUMA BA KA SANSHI BA, KUMA BA KA KA’DAITA SHI BA.DUBA : AL-KAFIY 1/ 145. DA BIHARUL ANWAR, 23/ 103. DA AL -TAUHEED NA IBNU BABAWAIHI, SHAFI NA 152.A WATA RUWAYAR:( ﻭﻧﺤﻦ ﺍﻟﺴﺒﻴﻞ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ).“KUMA MU NE HANYA ZUWAGA ALLAH”,DUBA : IRSHADUL K’ULUBI NA DAILAMIY, 2/ 414.A WATA RUWAYAR:( ﻧﺤﻦ ﻭﻻﺓ ﺃﻣﺮ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺧﺰﻧﺔ ﻋﻠﻢ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻋﻴﺒﺔ ﻭﺣﻲ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺃﻫﻞ ﺩﻳﻦﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻋﻠﻴﻨﺎ ﻧﺰﻝ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺑﻨﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻟﻮﻻﻧﺎ ﻣﺎ ﻋﺮﻑ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻧﺤﻦ ﻭﺭﺛﺔ ﻧﺒﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻋﺘﺮﺗﻪ ).“MU NE MAJI’BANTAR AL’AMARIN ALLAH, KUMA MU NE TASKOKIN ILMIN ALLAH, KUMA MU NE MAZUBIN WAHAYIN ALLAH, KUMA MU NE MA’ABOTA ADDININ ALLAH, LITTAFIN ALLAH A GAREMU YA SAUK’A. KUMA DA MU AKA BAUTA MA ALLAH, BA DON MU BA DA BA A BAUTA MA ALLAH BA. KUMA MU NE MAGADA ANNABIN ALLAH, KUMA ZURRIYARSA”.DUBA : BASA’IRUD DARAJATIL KUBRA NA AL- SAFFAR, SHAFI NA 61.ALLAH YA SAUWAKA, YA SHIRYI MABIYA SHI’A SU TUBA SU DAWO KAN TAFARKIN KWARAI, KUMA YATSARE AL’UMMAR MUSULMI DAGA AUKAWA CIKIN SHI’A.

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

menene matsayin maganar limamai awajan malamanau

from nuramuhd3 on 04/02/2015 08:59 AM

MENENE MATSAYIN MAGANGANUN IMAMAN SHI’A A WAJEN MALAMANSU?AMSA: SUKA CE: MATSAYINSU KAMAR MAGANAR ALLAH NE. SUKA CE:( ﺇﻥ ﺣﺪﻳﺚ ﻛﻞ ﻭﺍﺣﺪ ﻣﻦ ﺍﻷﺋﻤﺔ ﺍﻟﻄﺎﻫﺮﻳﻦ ﻗﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ، ﻭﻻ ﺍﺧﺘﻼﻑ ﻓﻲ ﺃﻗﻮﺍﻟﻬﻢ ﻛﻤﺎ ﻻ ﺍﺧﺘﻼﻑ ﻓﻲ ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ).“LALLAI HADISIN KOWANE ‘DAYA DAGA CIKIN IMAMAI TSARKAKA MAGANAR ALLAHNE. KUMA BABU WANI SA’BANI A MAGANARSU KAMAR YADDA BABU SA’BANI A MAGANAR ALLAH TA’ALAH.” KAI HAR MA SUN CE:( ﻳﺠﻮﺯ ﻣﻦ ﺳﻤﻊ ﺣﺪﻳﺜﺎ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻉ، ﺃﻥ ﻳﺮﻭﻳﻪ ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﺃﻭ ﻋﻦ ﺃﺣﺪ ﺃﺟﺪﺍﺩﻩ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ، ﺑﻞ ﻳﺠﻮﺯ ﺃﻥ ﻳﻘﻮﻝ : ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ).“YA HALATTA GA WANDA YA JI HADISI DAGA BABAN ABDULLAH, YA RUWAITO SHIDAGA BABANSA, KO DAGA ‘DAYA DAGA CIKIN KAKANINSA (AS), KAI, YA HALATTA YA CE: ALLAH NE YA CE”.DUBA: (SHARHUN JAMI’U NA ALMAZANDARANIY, 2/ 272).KUMA SUN CE:( ﺑﺄﻥ ﺍﻹﻣﺎﻣﺔ ﺍﺳﺘﻤﺮﺍﺭ ﻟﻠﻨﺒﻮﺓ )WAI “IMAMA CIGABA NE NA ANNABTA”!DUBA: (AK’A’IDUL IMAMIYYA NA MUZAFFAR, PG. 66).KHUMAINIY YA CE:( ﺇﻥ ﺗﻌﺎﻟﻴﻢ ﺍﻷﺋﻤﺔ ﻛﺘﻌﺎﻟﻴﻢ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥﻳﺠﺐ ﺗﻨﻔﻴﺬﻫﺎ ﻭﺍﺗﺒﺎﻋﻬﺎ )“LALLAI KOYARWAR IMAMAI KAMAR KOYARWAR AL-K’UR’ANI NE. YA WAJABA A ZARTAR DA SU KUMA A BI SU”.DUBA: (AL-HUKUMATUL ISLAMIYYA, PG. 13)TO JAMA’A, KUN GA FA YADDA ‘YAN SHI’A SUKE SO SU RABA MUSULMI DA ALLAH DA MAGANARSA. A RIK’E MAGANGANUNSU DA SUKA K’IRK’IRA SUKA JINGINASU GA AHLUL BAITI.LALLAI KO SHAKKA BABU DAIDAITA MAGANAR WANI DA MAGANAR ALLAH KAFIRCI NE.” ﺇﻥ ﻫﺬﺍ ﺇﻻ ﻗﻮﻝ ﺍﻟﺒﺸﺮ ﺳﺄﺻﻠﻴﻪ ﺳﻘﺮ “.KUMA YA CE:” ﻭﻣﻦ ﺃﻇﻠﻢ ﻣﻤﻦ ﺍﻓﺘﺮﻯ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻛﺬﺑﺎ ﺃﻭ ﻗﺎﻝ ﺃﻭﺣﻲ ﺇﻟﻲ ﻭﻟﻢ ﻳﻮﺡ ﺇﻟﻴﻪ ﺷﻲﺀ ﻭﻣﻦ ﻗﺎﻝ ﺳﺄﻧﺰﻝ ﻣﺜﻞ ﻣﺎ ﺃﻧﺰﻝ ﺍﻟﻠﻪ “.YA CE:” ﻭﻣﻦ ﺃﻇﻠﻢ ﻣﻤﻦ ﺍﻓﺘﺮﻯ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻛﺬﺑﺎ ﺃﻭﻟﺌﻚ ﻳﻌﺮﺿﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺭﺑﻬﻢ ﻭﻳﻘﻮﻝ ﺍﻷﺷﻬﺎﺩ ﻫﺆﻻﺀ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻛﺬﺑﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺭﺑﻬﻢ ﺃﻻ ﻟﻌﻨﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻈﺎﻟﻤﻴﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺼﺪﻭﻥﻋﻦ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻳﺒﻐﻮﻧﻬﺎ ﻋﻮﺟﺎ ﻭﻫﻢ ﺑﺎﻵﺧﺮﺓ ﻫﻢ ﻛﺎﻓﺮﻭﻥ “.DON HAKA, WANNAR AK’IDATA ‘YAN SHI’A KAFIRCI CE.KUMA WANNAR AK’IDA CE TA YAHUDAWA, ALLAH YA CE:” ﻓﻮﻳﻞ ﻟﻠﺬﻳﻦ ﻳﻜﺘﺒﻮﻥ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺑﺄﻳﺪﻳﻬﻢ ﺛﻢ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﻫﺬﺍ ﻣﻦ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻴﺸﺘﺮﻭﺍ ﺑﻪ ﺛﻤﻨﺎ ﻗﻠﻴﻼ ﻓﻮﻳﻞ ﻟﻬﻢ ﻣﻤﺎ ﻛﺘﺒﺖ ﺃﻳﺪﻳﻬﻢ ﻭﻭﻳﻞ ﻟﻬﻢ ﻣﻤﺎ ﻳﻜﺴﺒﻮﻥ “.KUMA DAI YA CE:” ﻭﺇﻥ ﻣﻨﻬﻢ ﻟﻔﺮﻳﻘﺎ ﻳﻠﻮﻭﻥ ﺃﻟﺴﻨﺘﻬﻢ ﺑﺎﻟﻜﺘﺎﺏ ﻟﺘﺤﺴﺒﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﻣﺎ ﻫﻮ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﻫﻮ ﻣﻦ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﺎ ﻫﻮ ﻣﻦ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻜﺬﺏ ﻭﻫﻢ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ ” .WANNAN BA ABIN MAMAKI BA NE, SABODA MALAMINSU NA FARKO BAYAHUDE NE!

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

menene sunnah a wajan malaman shi a

from nuramuhd3 on 04/02/2015 08:52 AM

MECECE SUNNA A WAJEN MALAMAN SHI’A?AMSA: SUNNA A WAJEN MALAMAN SHI’A ITA CE SUNNAR MA’ASUMAI BA TA MANZON ALLAH (SAW) BA.SUKA CE:( ﻷﻧﻬﻢ ﻫﻢ ﺍﻟﻤﻨﺼﻮﺑﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻋﻠﻰ ﻟﺴﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ، ﻟﺘﺒﻠﻴﻎ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻮﺍﻗﻌﻴﺔ، ﻓﻼ ﻳﺤﻜﻤﻮﻥ ﺇﻻ ﻋﻦ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻮﺍﻗﻌﻴﺔ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻛﻤﺎ ﻫﻲ ).MA’ANA; SABODA SU NE WA’DANDA AKA NA’DA DAGA WAJEN ALLAH (T) A BISA HARSHEN ANNABI. DON ISAR DA HUKUNCE – HUKUNCEN MASU FARUWA (ABUBUWAN DA SUKE GUDANA A CIKIN HALITTA). BA SA YIN HUKUNCIN SAI A HUKUNCE – HUKUNCE MASUAUKUWA KAMAR YADDA SUKE A WAJEN ALLAH”.DUBA: USULUL FIK’HIL MUK’ARAN NA MUH’D RIDA AL- MUZAFFAR, 3/ 51.WANNAR AK’IDA, TANA NUNA ABUBUWA GUDA BIYU:(1) TANA NUNA CEWA; IMAMAI SUN SAN GAIBI. ALHALI BABU WANDA YA SAN GAIBI SAI ALLAH.ALLAH YA CE:” ﻗﻞ ﻻ ﻳﻌﻠﻢ ﻣﻦ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻤﺎﻭﺍﺕ ﻭﺍﻷﺭﺽ ﺍﻟﻐﻴﺐ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﺎ ﻳﺸﻌﺮﻭﻥ ﺃﻳﺎﻥ ﻳﺒﻌﺜﻮﻥ “.ANNABI (SAW) MA BAI SAN GAIBI BA, BARE KUMA WANIKOMA BAYANSA. ALLAH YA CE:” ﻗﻞ ﻻ ﺃﻗﻮﻝ ﻟﻜﻢ ﻋﻨﺪﻱ ﺧﺰﺍﺋﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﺃﻋﻠﻢ ﺍﻟﻐﻴﺐ ﻭﻻ ﺃﻗﻮﻝ ﻟﻜﻢ ﺇﻧﻲ ﻣﻠﻚ ﺇﻥ ﺃﺗﺒﻊ ﺇﻻ ﻣﺎ ﻳﻮﺣﻰ ﺇﻟﻲ “.KUMA DU YA CE:” ﻗﻞ ﻻ ﺃﻣﻠﻚ ﻟﻨﻔﺴﻲ ﻧﻔﻌﺎ ﻭﻻ ﺿﺮﺍ ﺇﻻ ﻣﺎ ﺷﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻟﻮ ﻛﻨﺖ ﺃﻋﻠﻢﺍﻟﻐﻴﺐ ﻻﺳﺘﻜﺜﺮﺕ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻭﻣﺎ ﻣﺴﻨﻲ ﺍﻟﺴﻮﺀ ﺇﻥ ﺃﻧﺎ ﺇﻻ ﻧﺬﻳﺮ ﻭﺑﺸﻴﺮ ﻟﻘﻮﻡ ﻳﺆﻣﻨﻮﻥ “.DON HAKA, DUK WANDA YACE WANI YA SAN GAIBI WANDA BA ALLAH BA, TO YAFI KOWA JAHILCI.(2) KUMA DAI TANA NUNA CEWA; IMAMAI ANA YI MUSU WAHAYI, IMMA TA HANYAR MALA’IKA, KO KAI TSAYE, ALHALI WAHAYI YA RIGA DA YA YANKE DA RASUWAR ANNABI (SAW). DON HAKA WANNAN K’ARYANE TARE DA KUMA K’ARYATAALLAH NE, INDA YAKE CEWA:” ﻭﻣﻦ ﺃﻇﻠﻢ ﻣﻤﻦ ﺍﻓﺘﺮﻯ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻛﺬﺑﺎ ﺃﻭ ﻗﺎﻝ ﺃﻭﺣﻲ ﺇﻟﻲ ﻭﻟﻢ ﻳﻮﺡ ﺇﻟﻴﻪ ﺷﻲﺀ ﻭﻣﻦ ﻗﺎﻝ ﺳﺄﻧﺰﻝ ﻣﺜﻞ ﻣﺎ ﺃﻧﺰﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻟﻮ ﺗﺮﻯ ﺇﺫ ﺍﻟﻈﺎﻟﻤﻮﻥ ﻓﻲ ﻏﻤﺮﺍﺕ ﺍﻟﻤﻮﺕ ﻭﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﺑﺎﺳﻄﻮ ﺃﻳﺪﻳﻬﻢ ﺃﺧﺮﺟﻮﺍﺃﻧﻔﺴﻜﻢ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺗﺠﺰﻭﻥ ﻋﺬﺍﺏ ﺍﻟﻬﻮﻥ ﺑﻤﺎ ﻛﻨﺘﻢ ﺗﻘﻮﻟﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﺤﻖ ﻭﻛﻨﺘﻢ ﻋﻦ ﺁﻳﺎﺗﻪ ﺗﺴﺘﻜﺒﺮﻭﻥ “.

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

shin annabi yacika manzanci ashi anci

from nuramuhd3 on 04/02/2015 08:51 AM

A AK’IDAR MALAMAN SHI’A, SHIN ANNABI (SAW) YA GAMA ISAR DA SHARI’A GABA ‘DAYANTA KAFIN RASUWARSA, KO KUMA A’A?!AMSA: A’A! KAWAI YA ISAR DA WANI SASHE NE NA SHARI’AR, YA AJIYE SAURAN SASHEN KUMA WA ALIYU (RA).AYATULLAHI AN-NAJAFIY YA CE:( ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺿﺎﻗﺖ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﻔﺮﺻﺔ، ﻭﻟﻢ ﻳﺴﻌﻪ ﺍﻟﻤﺠﺎﻝ ﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺟﻤﻴﻊ ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﺪﻳﻦ.. ﻭﻗﺪ ﻗﺪﻡ ﺍﻻﺷﺘﻐﺎﻝ ﺑﺎﻟﺤﺮﻭﺏ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺘﻤﺤﺺ ﺑﺒﻴﺎﻥ ﺗﻔﺎﺻﻴﻞ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ… ﻻﺳﻴﻤﺎ ﻓﻲ ﻋﺪﻡ ﻛﻔﺎﻳﺔ ﺍﺳﺘﻌﺪﺍﺩ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺯﻣﻨﻪ ﻟﺘﻠﻘﻲ ﺟﻤﻴﻊ ﻣﺎ ﻳﺤﺘﺎﺝ ﺇﻟﻴﻪ ﻃﻮﻝ ﻗﺮﻭﻥ ).YA CE: LALLAI ANNABI (SAW)LOKACI YA YI MASA K’UNCI, BAI SAMU DAMAR KARANTAR DA DUKKAN HUKUNCE-HUKUNCEN ADDINI BA… YA GABATAR DA SHAGALTUWA DA YAK’UK’UWA NE AKAN KE’BANTUWA DA BAYANIN HUKUNCE – HUKUNCE DALLA-DALLA… MUSAMMANSABODA RASHIN CIKAKKIYAR TANADIN MUTANE A ZAMANINSA DON KAR’BAR DUKKAN ABINDA AKE BUK’ATA A TSAWON ZAMUNA”.DUBA : TA’ALIK’IN AN-NAJAFIN A IHK’AK’UL HAK’ NA AL- TASTURIY 2/ 288– 289.AL- KHOMAINIY YA CE:( ﻭﻧﻘﻮﻝ: ﺑﺄﻥ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ ﻟﻢ ﻳﻮﻓﻘﻮﺍ ﻓﻲ ﺗﻨﻔﻴﺬ ﻣﻘﺎﺻﺪﻫﻢ، ﻭﺃﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺳﻴﺒﻌﺚ ﻓﻲ ﺁﺧﺮ ﺍﻟﺰﻣﺎﻥ ﺷﺨﺼﺎ ﻳﻘﻮﻡ ﺑﺘﻨﻔﻴﺬ ﻣﺴﺎﺋﻞ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ ..)YA CE: KUMA MUKE CEWA; LALLAI ANNABAWA BA SU CINASARA BA WAJEN GUDANAR DA MANUFOFINSU, LALLAI ALLAH ZAI TAYAR DA WANI MUTUM A K’ARSHEN ZAMANI, WANDA ZAI GUDANAR DA MAS’ALOLIN ANNABAWAN…DUBA : MAS’ALATUL MAHDIY, SHAFI NA 22.WANNAR AK’IDA KO SHAKKABABU, K’ARYATA ALLAH NE, INDA YA CE:” ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺃﻛﻤﻠﺖ ﻟﻜﻢ ﺩﻳﻨﻜﻢ ﻭﺃﺗﻤﻤﺖ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻧﻌﻤﺘﻲ ﻭﺭﺿﻴﺖ ﻟﻜﻢ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺩﻳﻨﺎ “.YA CE: A YAU NA CIKA MUKUADDININKU, KUMA NA CIKA NI’IMOMINA GAREKU, KUMANA YARDA MUSLUNCI YA ZAMA MUKU ADDINI”.KUMA DAI YA CE:” ﻭﻟﻘﺪ ﺟﺎﺀﺗﻬﻢ ﺭﺳﻠﻨﺎ ﺑﺎﻟﺒﻴﻨﺎﺕ ﺛﻢﺇﻥ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﻣﻨﻬﻢ ﺑﻌﺪ ﺫﻟﻚ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻟﻤﺴﺮﻓﻮﻥ “.“HAK’IKA MANZANNINMU SUN ZO MUSU DA HUJJOJI BAYYANANNU, SA’ANNAN DA YAWA DAGA CIKINSU, BAYAN HAKA MASU ‘BARNA NE A BAYAN K’ASA”.KUMA YA CE:ﻓﺈﻥ ﻛﺬﺑﻮﻙ ﻓﻘﺪ ﻛﺬﺏ ﺭﺳﻞ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻚ ﺟﺎﺀﻭﺍ ﺑﺎﻟﺒﻴﻨﺎﺕ ﻭﺍﻟﺰﺑﺮ ﻭﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻤﻨﻴﺮ“IN SUN K’ARYATAKA, TO HAK’IK’A SUN K’ARYATA MANZANNI KAFINKA, WA’DANDA SUN ZO DA AYOYI BAYYANANNU DA TAKARDU DA LITTAFI MAI HASKE”.KUMA YA CE:” ﻭﻫﺬﺍ ﺻﺮﺍﻁ ﺭﺑﻚ ﻣﺴﺘﻘﻴﻤﺎ ﻗﺪ ﻓﺼﻠﻨﺎ ﺍﻵﻳﺎﺕ ﻟﻘﻮﻡ ﻳﺬﻛﺮﻭﻥ “.“WANNAR HANYAR UBANGIJINKA CE MADAIDAICIYA, HAK’IK’A MUN YI BAYANIN AYOYI DALLA-DALLA GA MUTANE MASU FA’DAKUWA”.YAKE CEWA GAME DA MANZANNI :” ﻟﻴﻌﻠﻢ ﺃﻥ ﻗﺪ ﺃﺑﻠﻐﻮﺍ ﺭﺳﺎﻻﺕ ﺭﺑﻬﻢ “.“DOMIN ALLAH YA SAN CEWA; MANZANNIN SUN ISAR DA SAK’ONNIN UBANGIJINSU …”.DON HAKA DUK WANDA YA CE; ANNABAWA BA SU ISAR DA SAK’ON ALLAH GABA ‘DAYA BA, KUMA FILLA – FILLA, LALLAI YA K’ARYATA ALLAH, KUMA BAI YI IMANI DA MANZANNIN ALLAH BA. KOWANNE ‘DAYA DAGA CIKIN WA’DANNAN K’ARYATAWA BIYUN KAFIRCI NE!

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

menene matsayin malaman shi a gameda hadisan annabi

from nuramuhd3 on 04/02/2015 08:49 AM

MENENE MATSAYIN MALAMAN SHI’A GAME DA HADISAN ANNABI (SAW) WA’DANDA SAHABBAI SUKA RUWAITO?AMSA: WAK’A A BAKIN MAI ITA TAFI DA’DI:ALU KASHIFUL GHI’DA’I YAKE CEWA:( ﻻ ﻳﻌﺘﺒﺮﻭﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺇﻻ ﻣﺎ ﺻﺢ ﻟﻬﻢ ﻣﻦ ﻃﺮﻳﻖ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﻴﺖ … ﺃﻣﺎ ﻣﺎ ﻳﺮﻭﻳﻪ ﻣﺜﻞ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﻭﺳﻤﺮﺓ ﺑﻦ ﺟﻨﺪﺏ … ﻓﻠﻴﺲ ﻟﻪ ﻋﻨﺪ ﺍﻹﻣﺎﻣﻴﺔ ﻣﻘﺪﺍﺭ ﺑﻌﻮﺿﺔ ).YA CE: SU ‘YAN SHI’A, BA SA LA’AKARI DA HADISI SAI WANDA YA INGANTA MUSU TA HANYAR AHLUL BAITI… AMMA ABIN DA ABU HURAIRA, DA SAMURATU BIN JUNDUB … SUKE RUWAITOWA, BA SHI DA KO DA MATSAYIN SAURO NE A WAJEN IMAMIYYA”.DUBA : ASLUSH-SHI’A WA USULUHA, SHAFI NA 79.DALILINSU A KAN HAKA SHI NE ABIN DA KULAINIY YA FA’DA:( ﻛﻞ ﻣﺎ ﻟﻢ ﻳﺨﺮﺝ ﻣﻦ ﻋﻨﺪ ﺍﻷﺋﻤﺔ ﻓﻬﻮ ﺑﺎﻃﻞ )“DUKKAN ABIN DA BAI FITO DAGA WAJEN IMAMAI BA, TO ‘BATACCE NE”.DUBA : USULUL KAFIY, 1/ 399.TO JAMA’A, KUN GA WANNAN SHI YAKE NUNA MANA CEWA; MANUFAR SHI’A SHI NE;RUSHE ADDININ MUSLUNCI. SABODA BABU WANDA ZAI SAMU ILMIN ANNABI (SAW) SAI TA HANYAR SAHABBANSA.LALLAI K’IN YARDA DA WA’DANDA ALLAH YA YARDADA SU, ZAI KAI MUTUM ZUWA GA K’ARYATA ALLAH, INDA YAKE NUNA YARDARSAGA SAHABBAI:” ﻭﺍﻟﺴﺎﺑﻘﻮﻥ ﺍﻷﻭﻟﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻳﻦ ﻭﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﺗﺒﻌﻮﻫﻢ ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ ﻭﺭﺿﻮﺍ ﻋﻨﻪ ﻭﺃﻋﺪ ﻟﻬﻢ ﺟﻨﺎﺕ ﺗﺠﺮﻱ ﺗﺤﺘﻬﺎ ﺍﻷﻧﻬﺎﺭ ﺧﺎﻟﺪﻳﻦ ﻓﻴﻬﺎ ﺃﺑﺪﺍ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻔﻮﺯ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ “.LALLAI ABU ZUR’ATAR RAZIY (R) YA YI GASKIYA, INDA YAKE CEWA:” ﺇﺫﺍ ﺭﺃﻳﺖ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻳﻨﺘﻘﺺ ﺃﺣﺪﺍ ﻣﻦ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ , ﻓﺎﻋﻠﻢ ﺍﻧﻪ ﺯﻧﺪﻳﻖ. ﻭﺫﻟﻚ ﺃﻥ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ ﻋﻨﺪﻧﺎ ﺣﻖ , ﻭﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺣﻖ , ﻭﺍﻧﻤﺎ ﺃﺩﻯ ﺇﻟﻴﻨﺎ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻭﺍﻟﺴﻨﻦ ; ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ. ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻳﺮﻳﺪﻭﻥ ﺍﻥ ﻳﺠﺮﺣﻮﺍ ﺷﻬﻮﺩﻧﺎ ﻟﻴﺒﻄﻠﻮﺍ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ , ﻭﺍﻟﺠﺮﺡ ﺑﻬﻢ ﺃﻭﻟﻰ ﻭﻫﻢ ﺯﻧﺎﺩﻗﺔ “.“IDAN KA GA MUTUM YANA NAK’ASA (AIBANTAWA) ‘DAYA DAGA CIKIN SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW), TO KA SANI; SHI ZINDIK’I NE. DALILI; SABODALALLAI MANZON ALLAH (SAW) A WAJENMU GASKIYA NE, ALK’UR’ANI MA GASKIYA NE. KUMA WA’DANDA SUKA KAWO MANA WANNAN ALK’UR’ANIN, DA SUNNONINMANZON ALLAH (SAW) KAWAI SU NE; SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW). KAWAI SUNA SO NE, SU YI ‘BATANCI GA SHAIDUNMU (SAHABBAI) DON SU RUSA LITTAFIN ALLAH, DA SUNNAR MANZON ALLAH (SAW). LALLAI SU NE SUKA CANCANCI ‘BATANCI, KUMA SU ZINDIK’AI NE (MASU ZAGON K’ASA MA ADDININ MUSLUNCI)”.DUBA : AL- KIFAYAH NA AL-KHA’DIBUL BAGHDADIY, 1/ 188.GASKIYA TA YI HALINTA; ‘YAN SHI’A SUN SA’BAWA IMAMANSU A WANNAR AK’IDAR.AL-KULAININ YA RUWAITO DAGA IBNU HAZIM YA CE;( ﻗﻠﺖ ﻷﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ .. ﻓﺄﺧﺒﺮﻧﻲ ﻋﻦ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺻﺪﻗﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ، ﺃﻡ ﻛﺬﺑﻮﺍ؟ ﻗﺎﻝ : ﺑﻞ ﺻﺪﻗﻮﺍ ).“NA CE MA BABAN ABDULLAHI; KA BA NI LABARI GAME DA SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW), SUN FA’DI GASKIYA DAGA MUH’D NE, KO KUMA K’ARYA SUKA YI MASA? YA CE; A’A SUN YI GASKIYA!”.DUBA : USULUL KAFIY, 1/ 65.WANNAN YANA NUNA CEWAAHLUL BAITI DA SAHABBAI TIF DA TAYA NE, SA’BANIN K’ARERAYIN DA ‘YAN SHI’AN SUKE YI NA NUNA SA’BANI ATSAKANINSU.

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

manyan littattafai nahadisin shia

from nuramuhd3 on 04/02/2015 08:47 AM

WA’DANNE NE MANYAN LITTATAFAN SHI’A NA HADISI, WA’DANDA SUKE DOGARA DA SU??AMSA: MALAMAN SHI’A SUNA DOGARA A KAN WASULITTATAFAI GUDA HU’DU WAJEN ‘DAUKAR ADDININSU.LITTAFAN SU NE; AL-KAFIY, AL-TAHZEEB, AL- ISTIBSAR, DA MAN LA YAHDURUHUL FAK’IHU.MALAMANSU NA ZAMANI SUN TABBATAR DA HAKAN, KAMAR AGHA BARZAK AL-TEHRANIY, A CIKIN LITTAFINSA AL-ZARIY’AH, 17/ 245. DA MUHSIN AMEEN AL-AMILIY A CIKIN LITTAFINSA A’AYANUSH SHI’A, 1/ 280

Reply

nuramuhd3
Admin

36, male

Posts: 118

menene matsayin littattafai hudu na yanshi a

from nuramuhd3 on 04/02/2015 08:46 AM

MENENE MATSAYIN WA’DANNAN LITTATAFAI GUDA HU’DU A WAJEN MALAMAN SHI’A?AMSA: WA’DANNAN LITTATAFAI GUDA HU’DU INGANTATTU NE A WAJEN MALAMAN SHI’A, HAKA MA ABIN DA KE CIKINSU.GA ABIN DA WANI AYATULLAHIN SHI’A MAISUNA “ABDUL HUSAIN ALMUSAWIY” YAKE CEWA:( ﻭﻫﻲ ﻣﺘﻮﺍﺗﺮﺓ، ﻭﻣﻀﺎﻣﻴﻨﻬﺎ ﻣﻘﻄﻮﻉ ﺑﺼﺤﺘﻬﺎ، ﻭﺍﻟﻜﺎﻓﻲ ﺃﻗﺪﻣﻬﺎ، ﻭﺃﺣﺴﻨﻬﺎ، ﻭﺃﺗﻘﻨﻬﺎ ).YA CE: LITTATAFAN MUTAWATIRAI NE, KUMA ABIN DA SUKA K’UNSA INGANCINSA TABBATACCE NE YANKE. AL-KAFIY SHI NE MAFI DA’DEWANSU, KUMA MAFI KYAWUNSU, KUMA MAFI INGANCINSU”.DUBA : AL-MURAJA’AT NA ABDUL HUSAINI AL-MUSAWIY, A MURAJA’A TA 110, SHAFI NA 311

Reply
First Page  |  «  |  1  ...  7  |  8  |  9  |  10  |  11  ...  24  |  »  |  Last

« Back to previous page