shi a da sayyidina umar
[ Go to bottom | Go to latest post | Subscribe to this topic | Latest posts first ]
shi a da sayyidina umar
from nura on 09/07/2014 11:53 AMTATSUNIYAR `YAN SHI’A `YAN SHA BIYU`Yan Shi’a `yan sha biyu sun ci mutuncin Umar xan Khaxxab (R.A.) kamar yadda suka saba, sun qirqiri wasu tatsuniyoyi da suke nuna dalilin da yasa Umar xan Khaxxab ya haramta mut’a da mata, daga cikin irin waxannan tatsuniyoyi suna cewa:1- “Wai wata rana Umar xan Khaxxab (R.A.) ya shiga wurin `yar’uwarsa mai suna Afra’u, sai ya ga jariri a cinyarta mai shan mama, sai ya yi fushi, fushi mai tsanani, sannan sai yakarve yaron daga hannunta, sai ya fita, har ya zo Masallaci ya tara mutane ba a lokacin Sallah ba, sai ya ba mutane labarin abin da `yar’uwarsa ta aikata nahaihuwar yaro daga mut’a (alhali ba ta da miji), sannan saiya tsoratar da mutane, ya yi masu qyace yana mai tabatar da haramcin mut’a.” Ka duba “Buharul Anwar” na Majlisi (Babban Malaminsu da aka Haifa a shekara ta (1037H). 35/28, 29 da kuma 100/303,304 daga littafin dana ambata.2- Sannan kuma irin wannan tatsuniya ta sake bayyana a cikin littafin “Had’iqul Unsi” na Ibrahimul Musawi ba tare da isnadi ba.Yana cewa “Dalilin da yasa Umar xan Khaxxab ya hana mut’a: wai wata rana Umar xan Khaxxab ya ga wani jariri mai shan mama a wurin `yar’uwarsa mai suna “Khadra’u” a lokacin da ya tambaye ta game da shi, alhali ba ta da miji, sai ta ce “Ai shi xan mut’a ne” sai ya yi fushi, fushi mai tsanani, kuma daga nan ne sai ya hana mut’a”. Ka duba “Asshi’atu wal mut’a” na Muhammadu Malul lahi” shafi na 28. daga littafin Hada’iqul unsi” na Ibrahimul Musawi da “Azzanjani” shafi na 210 daga littafin dana ambata.3- Shi kuma babban Malamin sudashi ma bai kunyar qarya cewaya yi:“Dalilin da yasa Umar xan Khaxxab (R.A.) ya haramta mut’a, shi ne, wata rana ya gayyaci Aliyyu xan Abi Xalib (R.A.) gidansa, ya yin da wani yanki na dare ya wuce sai ya nisanta, (Aliyyu) sai (Umar) ya neme shi da ya yi barci a wurinsa, sai ya yi barci, a lokacin da (Aliyyu) ya wayi gari, sai Umar xan Khaxxab (R.A.) ya fito daga cikin gidasa yana mai jayayya da Amirul Muminina cewa ka ce “Lalle ba ya kamata ga Mumini ya kwana a dare yana gwauro idan ya kasance a gari, sai gashi a wannan daren ka kwana kana gwauro? Sai Amirul Muminina (A.S.) ya ce: Me ya sanar da kai na kwana gwauro? Alhali ni wannan darenhaqiqa na yi mut’a da `yar’uwarka wance, sai ya voye a zuciyarsa har sai da ya samu daman haramtawa sai ya haramta. Ka duba “Al’anwarun Nu’umaniyyah” na NI’imatullahi Jaza’iri 2/320 daga littafin dana ambata.Abubuwan fahimta daga waxannan tatsuniyoyi.1- Irin tsananin qiyayyar `yan Shi’a `yan sha biyu ga Umar xan Khaxxab (R.A.).2- Sun qirqirowa Umar xan Khaxxab (R.A.) `yar’uwa da ba ta.3- Wani lokaci su ce mata Afra’u, ko Khadra’u, wani lokaci ma ba ta da suna.4- Wajen sukar Umar xan Khaxxab (R.A.) sun tuhumci Aliyyu (R.A.) da cin amana.BABI NA GOMA`YAN SHI’A `YAN SHA BIYU DA UMAR XAN KHAXXABDuk wanda ke lura da aqidar Shi’a `yan sha biyu yasan ta ginu ne akan sukar musamman khalifofin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) uku, musamman Umar xan Khaxxab (R.A.). Kuma ita wannan muguwar aqida ta sukar wasu daga Sahabbai, `yan Shi’a `yan sha biyu kaxai ne suka kaxaita da ita tun daga Allah ya yi duniya, domin ba a tava samun al’ummar da ta tsine wa wasu daga sahabban Annabinta ba, sai `yan Shi’a `yan sha biyu. Shin me yasa qiyayyar `yan Shi’a `yan sha biyu ta fi tsanani akan Umar xan Khaxxab (R.A), surukin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), kuma surukin Aliyyuda Faxima (R.A.)?BABI NA SHA XAYASHIN KO KA SAN WANE NE XANKHAXXAB?A- Umar Xan Khaxxab (R.A.) shi ne wanda ya Musulunta da Addu’ar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam).B- Yana daga cikin “Sabiqunal Awwalin” (Waxanda suka riga shiga Musulunci) tarihi ya nun shi ne na 40 a Musulunci. Kai kuma xan Shi’a xan sha biyu mai zagin Umar kaine na nawa a Musulunci?C- Da Shi ne Allah ya xaukaka Musulunci.D- Shi ne ya ce a fito fili a bautawa Allah bayan da ana bauta masa a voye.E- Shi ne mutumin da shexan ketsoro in ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam).F- Shi ne kaxai mutumin da ya yiHijrah a bayyane a lokacin kowayana voyewa.G- Shi ne kaxai mutumin da Allah (Subhanahu Wata’ala) yake yi masa ilhama a cikin al’ummar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam).H- Yana daga cikin mutane goma da aka yi musu bushara da Aljannah, tun anan duniya.

Reply