tadi

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nura

36, male

Posts: 124

tadi

from nura on 08/06/2014 02:21 PM

ZANCE TSAKANIN SAURAYI DA BUDURWA:SHIN YA HALATTA??Da sunan Allah mai rahma mai jinqai. Godiya da yabo sun tabbata ga Allah Ta'ala, muna neman taimakonsa da gafararsa. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Shugaban mu, Annabin rahma, da iyalansa, da Sahabbansa, da waxanda suka bi tafarkinsu, bisa kyautata koyi har ya zuwaranar qarshe.Bayan haka, lalle mu'amala tsakanin namiji da mace `yan'uwa na jini ko ta janibin `yan'uwantakar Musulunci, abu ne da malamai suka yawaita bayanai da rubuce-rubuce akan haqiqanin yadda shari'ar wannan kammalallen Addini ta tsara kuma take son a aiwatar, ba tare da bin son rai ba. Musamman abin da yakevanci kaxaicewa da macen da ba muharrama ba, wato macen da mutum zai iya aura,ba tare da wani shamaki ba.Al'ada ta gudana, cikin kowacce al'umma, akan yi abin da ake kira zance, ko hirako taxi, tsakanin saurayi da budurwa, ko bazawari da bazawara, sawa'un da zummar aure ko kuma hirar shirme da vata lokaci, alhali ba aure aka nufa ba. Kuma anriga an sani cewa, galibin zancen dake wakana tsakanin masoya a yau, ana yinsa ne a soraye, ko zaure, wasu cikin duhu, wasu a cikin haske, wasu a soron da ake iya hango su daga waje, kuma ana samun yawan masu shigada fita, wasu kam babu haka. Ala ayyi halin dai xaixaikun iyaye ne suke xabbaqa sharaxin haxa `yarsu da waniko wata, wato in zata fito zance da saurayin ta ko bazawrin ta. Wannan kam tamkar sakankancewa ce, tareda amintuwa daga fitinar Shaixana.Haka nan yana daga abin da yake daxa qona min rai, yadda galibin `yan'uwa matasa da zawarawa suke share awa xaya zuwa biyu, suna hira da mace, ba zasu faxa mata kalmomin da zasu amfane ta a duniya da lahira ba, sai baloqoqon shirme, shirbici, da kuma qarya. Koda yake wasu kance, ai matan ne basa son duk namijin da yake yi musu hirar gyaran Ibadah, mu'amala, da al'adu.Lalle na gamsu cewa mafi yawan `yan mata da zawarawa basa maraba-lale da namijin dake yi musu hira mai amfani da amfanarwa. Wannan kam rafkana ce da takurarren tunani, haka ne mana! Yo banda haka, ta yaya zasu dinga zaluntar kawunansu wajen mantawa da haqiqanin abin da suka zo yi a duniya, wato Ibadah, alhali shi Musulmi namiji da mace masu hankali lafiyayaye basa yin sakaci kan duk abin da zai amfane su a duniya da lahira.Amma tare da haka, ni na haqqaqe, akwai `yan mata da dama, waxanda suke jiran (dakon) karvar duk namijin daya zo musu da zancen da zasugyara Ibadar su, mu'amalarsu, da al'adunsu. Kaga kenan idan zuciyar ka dahankalinka suna neman irin waxannan `yan mata da zawarawa, to, ka dage da Addu'a, kuma ka bincika zaka samu da sannu.Tambaya anan ita ce: ZANCE TSAKANIN SAURAYI DA BUDURWA: SHIN YA HALATTA??Amsa ita ce; Ya halatta bisa sharuxxa. Ga abin da malamai masu tsantseni suka bayyana: Malam Abu Ubaida (Allah ya rahamshe shi) ya faxa a cikin littafinsa (Hidayatul Ursiyina shafi na 17) cewa “Babu laifi zuwa zance, amma zuwa zance bai zama abin lazimta ba, ace kullum sai anje zance, domin shi zance da ake zuwa ai ba xaura aure bane. A a so ake a samu fahimtar juna, na wani xan lokaci sai a xaura aure, kuma ya ce wannan maganar jamhurin (mafi yawan) malamai a kanta suke. Amma yana da kyau shi zuwa zancen a samu wasu sharuxxa kamarhaka:(1) Yardar iyaye(2) Rashin kaxaicewa a duhu ko a loko(3) Rashin jeruwa da juna(4) Tsayar da shawarar yarda ko rashinta.(Allah shi ne masani) na ciro wannan ne a littafin “Kyautar ma'aurata” shafi 19-20. wallafar xan'uwa Umar Al-hassan Sabo Wanzan sheka, Kano.Haka nan Malami na Abubakar Abbas Ibrahim R/Lemo a littafinsa “Albishirinku Manema Aure” shafi na 14-16. Ya yi gamsashshen bayani bisa hujja qarvavviya, ga abin da zan tsakuro. Ya ce “A shari'ance dai, Musulunci bai hana gudanar da misayar magana tsakanin namiji da mace ba, idan buqatar hakan ta taso. Sai dai kuma Musulunci bai bar damar yin hakan saka-kai, babu wani tsari ba. A'a sai da ya gindaya wasu sharuxxa da za a kiyaye dasu. Kamar haka:(1) A samu tabbacin babu wata fitina da zata faru a sakamakon gudanar musayar magana a tsakaninsu.(2) Kada su kaxai ce kaxaicewar da babu wani wanda zai iya fahimtar ko sanin abin da ya ke wakana a tsakaninsu.(3) A tabbata maganar da zatagudana a tsakaninsu ba wadda ta savawa shari'a bace.(4) Kada manufar namijin da zai zanta da mace ta zama ta ya ji daxin muryarta ne.(5) Kada macen da zata zanta da namiji ta rausayar, ko raurawar da muryar ta.(6) Kada kuma ta xagas muryarta fiye da qima.Dangane da ire-iren abubuwan da a sanadiyyarsu ake samun gudanar musayar magana tsakanin namiji da mace kuwa, a misalce akwai:(1) Yin Sallama, sai ta amsa(2) Yin fatawa (Tambaya) akanwata mas'ala ta Addini, da yin nasiha kan wani abu na kwaxaitarwa ko tsawatarwa, tare da umarni da kyakkyawan aiki, da hani ga mummunan aiki(3) Neman bayanin sanin watacuta domin magance ta, ga wanda ya san fannin.Imamu-Nawawi da Ibn Hajar (Allah ya rahamshe su) sun bayyana cewa, halal ne jin maganar matar da ba muharrama ba, idan buqatar hakan ta taso, matuqar an amince babu wata fitina da zata faru,” kamar dai yada bayani ya gabata a baya. Qarshen bayaninsa kenan.Saura dame? Ya xan'uwa da `yar'uwa, duba da bayanan da suka gabata cikin wannan maqala, na tabbatar ya bayyana cewa; dukkan namiji da macen da suke zance tsawon awa xaya ko biyu, ba tare da kawo bayanan da zasuamfane su ba, to, suna hasarar lokutansu ne a banza,kuma da wuya in basu sami zunubi ba. Kuma har yanzu dai zamu fahimci munin zuwazance barkatai, da kuma kwashe watanni da yawa, ko ma shekaru ana soyayya, ba tare da fara wani abu cikin matakan aure ba, irin hakan ne je janyo afkawa savon Allah da sunan an kusa zama xaya, Allah ya kiyashe mu afkawa iyakokin shari'a, amin summa amin.

Reply

« Back to forum