tonan silili akan salatil fati 2

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


nura

36, male

Posts: 124

tonan silili akan salatil fati 2

from nura on 09/16/2014 08:54 AM

**TONON SILILI GAMEDA SALATUL FAATIH**(2)Assalamu alaikum, A rubutuna na 1, nayi bayanin yanda salatulFaatih ta samo asali bisa Fadin Shehu Tijjani ta bakin Babban Haadiminsa Aliyu Harazimi, acikin JAWAHIRUL MA'ANI 1/94 da kuma 1/138, da kuma yanda Shehu ya baiyana Falalarta da romonta da cewar Tafi Sauqar Qur'ani sau 6000! Har Qarshe shi MUHAMMADUL BAKARI (wanda yace wai an masa wahayin salatul faati) yace: Duk wanda ya karanta salatul Faati, sai a lahira ya shiga Wuta, to ya shaqe shi gaban Allah yace ya cuceshi!! Ku duba jawahirul Ma'aani:1/138!TONON ASIRI:Yan uwa, Wallahi Tallahi Salatul Faatihi ta girme Shehu Tijjani daMuhammadul Bakari, ta Girmesu da sama da shekaru 1000! Qarya suke sun sace ta nesai sukai mata kwaskwarima don su Kautar da jama'a daga TAFARKIN MANZON ALLAH s.a.w!!!!!Bari kuga dalilaina don kauda shakku, kunsan bama Magana sai da Dalili:::"An Karbo daga Muhammad bnFadl, daga Abdullahil Asdiy, daga wani mutum daga Sayyidnaa Aliyyu, (mutumin shine Salaamatal kindiy) yace, Sayyadi Aliy r.a ya kasance yanacewa:((Allahumma yaa daahil mad'huwaat, wa yaa baanil mabniyaat, wa yaa mursil mursiyaat, wa ya jabbaaral Qulub lil muttaqiyn, ij'al sharaa'ifa salawaatika wa nawaamiy barakaatika, wa ra'afaati tahiyyatuka, wa awaatifu zawaakiy rahmatika alaMuhammadin, Abduka wa rasuluka ALFAATIHI LIMAA UGLIQA, WAL KHAATIMI LIMAA SABAQA, WA FAATIHIL HAQQI BIL HAQQI........))Ku duba wadannan littafai don ganewa idonku Gaskiya:1: MUSANNAF IBN ABIY SHAYBAH: Hadisi mai lamba 29520, 6/66. (littafin Abubakar bn Abiy Shaybah Al-abasiy, wanda ya mutu a shekara ta 235H)2: GARIYBUL HADIYS LIBNI QUTAYBAH: 2/143 (littafin da Abu-Muhammad Abdullahi bn Muslim bn Qutaybah Addaynuriy ya rubuta, ya mutu a shekara ta 276H)3: TAHZHIYBUL AATHAAR: 1/222.4: Mu'ujamul Ausat: Hadisi mai Lamba 9089, 9/42.5: Al-faa'iq fiy Gariybul Hadis: 1/416.6: Tafsir IBN KATHIYR: Qarqashin: Suratul Ahzaab, Aaya ta 56.7: Addurrul Manduwd fissalaati ala saahibil Maqaamul Mahmud: 1/92.8: Kanzul Ummaal: 2/270.9: Silsulatul ahaadiysudda'iyfah wal maudu'ah: 1/174.10: Mahabbatur-rasul baynal Itbaa'I walibtidaa: a Babin Salatotin Bidi'a ga Manzon Allahs.a.w: 1/285.11: Ash-shafaa bi Ta'ariyfi huququl Mustafaa: 2/164.*Daya Ruwayar da tazo da cikon: WA'ALAA AALIHI HAQQA QADRIHI WA MIQDAARIHIL AZIYM kuwa, sai ku duba:Al-Fasl fil milali wal ahwaa'I wannihali, na Abu Muhammad Aliyyu bn Ahmad bn Sa'iyd bn hazm Al-anadalasiy Alqurtabi azzaahiri, wanda ya mutu a shekara ta 456Hijriyyah, 5/91.Wannan Hadisi yazo ta Hanyoyi da yawa, amma dukkansu MAUQUFAI Ne, dayawan Malaman Hadisi sun sanya hadisin a layin MAUD'I! Domin baida inganci kwata-kwata! Gabaki daya hadisin na tuqewane kan cewa Imam Ali r.a, akan cewar Shi Imam Ali r.l shine yake koyawa Jama'a wannan Salaati! Kunga Bazai Yiwu Sayyadi Ali r.a yabar karantarwar Annabi s.a.w yakoma ya qirqiri wani abu sabanin na Annabi kuma ace wai har ya dinga koyawa Jama'a wannan salati na Shirmen ba! Hankalima ba zai dauka ba wlh! Kai kodama Hadisin nan ya Inganta, to ai Ba Sayyadi Ali aka aiko mana ba, ba shi akace mu bi ba, Annabi s.a.w aka ako mana kuma akace muyiwa biyayya!Idan kuma Akwai wanda ya isa, to yazo ya inganta wannan hadisi, ko ya wanke Shehu da Baqari daga wannan Abin kunyada suka Tafka!Mu hadu a kashi na 3!!!!!

Reply

« Back to forum