Latest posts
First Page | « | 1 ... 21 | 22 | 23 | 24
Search found 237 matches:
tadi
from nura on 08/06/2014 02:21 PMZANCE TSAKANIN SAURAYI DA BUDURWA:SHIN YA HALATTA??Da sunan Allah mai rahma mai jinqai. Godiya da yabo sun tabbata ga Allah Ta'ala, muna neman taimakonsa da gafararsa. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Shugaban mu, Annabin rahma, da iyalansa, da Sahabbansa, da waxanda suka bi tafarkinsu, bisa kyautata koyi har ya zuwaranar qarshe.Bayan haka, lalle mu'amala tsakanin namiji da mace `yan'uwa na jini ko ta janibin `yan'uwantakar Musulunci, abu ne da malamai suka yawaita bayanai da rubuce-rubuce akan haqiqanin yadda shari'ar wannan kammalallen Addini ta tsara kuma take son a aiwatar, ba tare da bin son rai ba. Musamman abin da yakevanci kaxaicewa da macen da ba muharrama ba, wato macen da mutum zai iya aura,ba tare da wani shamaki ba.Al'ada ta gudana, cikin kowacce al'umma, akan yi abin da ake kira zance, ko hirako taxi, tsakanin saurayi da budurwa, ko bazawari da bazawara, sawa'un da zummar aure ko kuma hirar shirme da vata lokaci, alhali ba aure aka nufa ba. Kuma anriga an sani cewa, galibin zancen dake wakana tsakanin masoya a yau, ana yinsa ne a soraye, ko zaure, wasu cikin duhu, wasu a cikin haske, wasu a soron da ake iya hango su daga waje, kuma ana samun yawan masu shigada fita, wasu kam babu haka. Ala ayyi halin dai xaixaikun iyaye ne suke xabbaqa sharaxin haxa `yarsu da waniko wata, wato in zata fito zance da saurayin ta ko bazawrin ta. Wannan kam tamkar sakankancewa ce, tareda amintuwa daga fitinar Shaixana.Haka nan yana daga abin da yake daxa qona min rai, yadda galibin `yan'uwa matasa da zawarawa suke share awa xaya zuwa biyu, suna hira da mace, ba zasu faxa mata kalmomin da zasu amfane ta a duniya da lahira ba, sai baloqoqon shirme, shirbici, da kuma qarya. Koda yake wasu kance, ai matan ne basa son duk namijin da yake yi musu hirar gyaran Ibadah, mu'amala, da al'adu.Lalle na gamsu cewa mafi yawan `yan mata da zawarawa basa maraba-lale da namijin dake yi musu hira mai amfani da amfanarwa. Wannan kam rafkana ce da takurarren tunani, haka ne mana! Yo banda haka, ta yaya zasu dinga zaluntar kawunansu wajen mantawa da haqiqanin abin da suka zo yi a duniya, wato Ibadah, alhali shi Musulmi namiji da mace masu hankali lafiyayaye basa yin sakaci kan duk abin da zai amfane su a duniya da lahira.Amma tare da haka, ni na haqqaqe, akwai `yan mata da dama, waxanda suke jiran (dakon) karvar duk namijin daya zo musu da zancen da zasugyara Ibadar su, mu'amalarsu, da al'adunsu. Kaga kenan idan zuciyar ka dahankalinka suna neman irin waxannan `yan mata da zawarawa, to, ka dage da Addu'a, kuma ka bincika zaka samu da sannu.Tambaya anan ita ce: ZANCE TSAKANIN SAURAYI DA BUDURWA: SHIN YA HALATTA??Amsa ita ce; Ya halatta bisa sharuxxa. Ga abin da malamai masu tsantseni suka bayyana: Malam Abu Ubaida (Allah ya rahamshe shi) ya faxa a cikin littafinsa (Hidayatul Ursiyina shafi na 17) cewa “Babu laifi zuwa zance, amma zuwa zance bai zama abin lazimta ba, ace kullum sai anje zance, domin shi zance da ake zuwa ai ba xaura aure bane. A a so ake a samu fahimtar juna, na wani xan lokaci sai a xaura aure, kuma ya ce wannan maganar jamhurin (mafi yawan) malamai a kanta suke. Amma yana da kyau shi zuwa zancen a samu wasu sharuxxa kamarhaka:(1) Yardar iyaye(2) Rashin kaxaicewa a duhu ko a loko(3) Rashin jeruwa da juna(4) Tsayar da shawarar yarda ko rashinta.(Allah shi ne masani) na ciro wannan ne a littafin “Kyautar ma'aurata” shafi 19-20. wallafar xan'uwa Umar Al-hassan Sabo Wanzan sheka, Kano.Haka nan Malami na Abubakar Abbas Ibrahim R/Lemo a littafinsa “Albishirinku Manema Aure” shafi na 14-16. Ya yi gamsashshen bayani bisa hujja qarvavviya, ga abin da zan tsakuro. Ya ce “A shari'ance dai, Musulunci bai hana gudanar da misayar magana tsakanin namiji da mace ba, idan buqatar hakan ta taso. Sai dai kuma Musulunci bai bar damar yin hakan saka-kai, babu wani tsari ba. A'a sai da ya gindaya wasu sharuxxa da za a kiyaye dasu. Kamar haka:(1) A samu tabbacin babu wata fitina da zata faru a sakamakon gudanar musayar magana a tsakaninsu.(2) Kada su kaxai ce kaxaicewar da babu wani wanda zai iya fahimtar ko sanin abin da ya ke wakana a tsakaninsu.(3) A tabbata maganar da zatagudana a tsakaninsu ba wadda ta savawa shari'a bace.(4) Kada manufar namijin da zai zanta da mace ta zama ta ya ji daxin muryarta ne.(5) Kada macen da zata zanta da namiji ta rausayar, ko raurawar da muryar ta.(6) Kada kuma ta xagas muryarta fiye da qima.Dangane da ire-iren abubuwan da a sanadiyyarsu ake samun gudanar musayar magana tsakanin namiji da mace kuwa, a misalce akwai:(1) Yin Sallama, sai ta amsa(2) Yin fatawa (Tambaya) akanwata mas'ala ta Addini, da yin nasiha kan wani abu na kwaxaitarwa ko tsawatarwa, tare da umarni da kyakkyawan aiki, da hani ga mummunan aiki(3) Neman bayanin sanin watacuta domin magance ta, ga wanda ya san fannin.Imamu-Nawawi da Ibn Hajar (Allah ya rahamshe su) sun bayyana cewa, halal ne jin maganar matar da ba muharrama ba, idan buqatar hakan ta taso, matuqar an amince babu wata fitina da zata faru,” kamar dai yada bayani ya gabata a baya. Qarshen bayaninsa kenan.Saura dame? Ya xan'uwa da `yar'uwa, duba da bayanan da suka gabata cikin wannan maqala, na tabbatar ya bayyana cewa; dukkan namiji da macen da suke zance tsawon awa xaya ko biyu, ba tare da kawo bayanan da zasuamfane su ba, to, suna hasarar lokutansu ne a banza,kuma da wuya in basu sami zunubi ba. Kuma har yanzu dai zamu fahimci munin zuwazance barkatai, da kuma kwashe watanni da yawa, ko ma shekaru ana soyayya, ba tare da fara wani abu cikin matakan aure ba, irin hakan ne je janyo afkawa savon Allah da sunan an kusa zama xaya, Allah ya kiyashe mu afkawa iyakokin shari'a, amin summa amin.
mutu a da matan aure
from nura on 08/06/2014 02:08 PMMUT’A DA MATAR AURE MAI MIJILalle kowa ya san mace mai miji tana daga cikin matan da Allah (Subhanahu Wata’ala) ya haramta aaura, har sai in mijinta ya sake ta kuma ta yi Idda, to babu laifi a aureta bayan Idda. Allah (Subhanahu Wata’ala) yana cewa “Da tsararrun wasu maza (wato an haramta muku matan aure masu maza matuqar mazansu basu sake su ba)Nisa’i 24.To amma abin ba haka yake ba a Shi’a `yan sha biyu, domin sun halatta mut’a da matar aure mai miji kamar yadda suka ruwaito daga Fadlu bararren bawan Muhammad Xan Rashid daga Abu Abdullahi (A.S.) ya ce nace: Lalle ni na auri mace auren mut’a, sai tunanin tana da miji ya auku a raina, sai na bincika haka, sai kuwana samu tana da miji? Sai ya ce: “Saboda me ka bincika?” Ka duba: Furu’ul kafi na Kulaini 5/1394 Hadisi na 9933. Da kuma Tahzhibul Ahkam 7/1003 Hadisi na 9300.NASIHATA GA MATAR MUT’AYa ke `yar’uwa! Kiji tsoron Allah ki kama kanki, wallahi auren mut’a baauren Sunnah ba ne, zina ce, ba irin auren da kakanninki suka yi ba ne, kuma ba da shi iyayenki suka samar dake ba. Saboda haka kada ki samar da `ya’yanki ta irin wannan aure, domin kawai buqatarwani, domin wallahi zaki tsaya a gaban Allah (Subhanahu Wata’ala) ke da wanda ya xauki hayarki, domin ki yi masa bayani, saboda haka kada ki bari a mayar dake karuwa da sunan Addini, ki yi mazaki tuba tun kafin mutuwa ta riske ki a lokacin da tuba ba ta da amfani. Wallahi baki da wata hanya ta tsira face ki rungumi Aqidar Sunnah, Aqidar da Manzon Allah (SallallahuAlaihi Wasallam) ya bar Sahabbansa da Ahlul baiti akanta, Aqidar tausayi, mutumci, kunya da kare `yancin mata.Xan’uwanki a Musulunci, mai tsananin tausayinki, da qaunarki dafatan alkhairi a gare ki:“Mawallafi”.
kawarda shubuha
from nura on 08/06/2014 02:05 PMKAWAR DA SHUBHACi gaba daga bugun baya7- Raddi ga maqaryata a dunqule da kuma rarrabeNi zan ambata maka abubuwan da Allah ya ambata cikin littafinsa, jawabi ga maganganun da mushrikai suka yi hujja da shi akan mu a wannan zamanin namu, sai muce jawabin maqaryata ta hanya biyu ne: a dunqule da kuma a rarrabe.Amma wanda yake a dunqule, to al’amari ne mai girma, kuma fa’ida ce mai girma ga wanda ya hankalceta, wannan kuwa ita ce maganar Allah:“Shi ne wanda ya saukar maka da littafi, a cikinsa akwai Ayoyi mabayyanan ma’anoni, sune asalinlittafin, da kuma wasu masu kama da juna. Amma waxanda suke da karkata a cikin zuqatansu, sai suna bin masu kama da juna daga cikinsa, domin neman fitina da neman fassararsa. Kuma babu maisanin fassararsa sai Allah”. Kuma haqiqa Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa ya ce: “Idan kuma ga waxanda suke bin wanda ya yi kama da juna daga cikin (Alqur’ani), to waxannan su ne waxanda Allah ya ambata ku guje su”. Misali, idan wani mushriki ya ce maka: “Ku saurara! Lalle waliyyan Allah babu tsoro gare su kuma basa yin baqin ciki”. Kuma ceto gaskiya ne, kuma waliyyan su na da alfarma a wajen Allah; ko kuma ya ambaci wani hukunci dagamaganar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana kafa hujja dashi akan wani abu na qaryarsa, kai kuma baka san ma’anar zancen da ya ambata ba, to ka amsa masa da cewa: Allah ya ambata a cikin littafinsa cewa waxanda suke akwaikarkara a cikin zuciyarsu suna barin Ayoyin bayyananmu, bin masu kama da juna (waxanda ma’anoninsu suke rikitarwa); abin da na ambata maka kuwa na cewa Allah ya ambaci mushrikai cewa suna iqirari da rububiyyar Allah, kum kafircinsu sabosa ratayarsu da mala’iku da Annabwa da waliyyai ne tare da faxinsu “Waxannan su ne masu cetonmu a wajen Allah….” Suratu Yunus, Aya ta 18. wannan al’amari ne bayyanan ne, babu wanda yake da ikon musanya ma’anarsa.Abin da ka ambata mini kuwa ya kai mushriki daga Alqurani da maganar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ban san ma’anarsa ba, amma ni na tabbatar cewa lalle zancen Allah ba ya savawa juna, kuma wannan jawabi ne mai kyau kuma daidai ne. Amma babu wanda zai fahimce shi sai wanda Allah ya yi ma gamdakatar, dan haka kada ka raina shi, domin shi kamar yadda Allah ya ce ne: “Kumaba za a cusa wa kowa wannan hali ba sai waxanda suka yi haquri, kuma ba za’a cusa shi ba sai ga maibabban rabo”. Suratul Fussilat, aya ta 35.Amma jawabi a dunqule, sai mu ce: Lalle maqiyan Allah suna da soke soke akan Musulunci, AddininManzanni waxanda suke kawar da mutane dasu daga bin Addinin Allah. Daga ciki akwai faxinsu cewamu ba ma yin shirka da Allah; muna shaidawa babu mai halitta da azurtawa, kuma babu mai amfanarwa ko cutarwa sai Allah shikaxai, bashi da abokin tarayya, kuma lallle Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba ya mallaka wa kansa wani amfani ko cuta, ballantana ma Shehu Abdulqadir ko waninsa, sai dai ni mai zunubi ne kuma salihai suna da makami a gurin Allah kuma ni ina nema gurin Allah ne ta hanyarsu. To, jawabinsa shi ne abin da ya gabata, wato shi ne cewa lalle waxanda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yaqe su suna tabbatar da abin da ka amtaba, kuma suna iqirarin cewa lalle gumakansu basa gudanar da komai, kawai suna neman alfarma dasu ne da ceto.Sannan kuma ka karanta masa abinda Allah ya faxa cikin littafinsa kuma ka qara masa bayaninsa. Idan ya ce ai waxannan Ayoyin sun sauka ne akan masu bautar gunki, ta yaya kuke sanya salihai kamar gumaka? Ko yaya kuke sanya Annabawa kamar gumaka? To, ka ba shi jawabi da abin da ya gabata, idan ya tabbatar da cewa lalle kafirai suna shaidar da Rububiyya dukanta ga Allah, kuma nufinsu daga waxanda suka fuskanta bai kasance ba face neman ceto, amma duk da haka yana so ya bambanta aikinsa da nasu da irin gurguwar hujjar da aka ambata, to sai ka ce masa: lalle kafirai cikinsu akwai mai kiran (roqon) gumaka, daga ciki kuma akwai masu kiran waliyyai, waxanda Allah ya ce a kansu: “Waxancan waxanda suke kiran suna neman tsani zuwa ga Ubangijinsu, waxannan ne mafifita a kusanci?” Suratul Isra’i, Aya ta 57.kuma suna roqon Isah xan Maryama da uwarsa, kuma Allah Ta’ala ya ce “Masihu xan Maryama bai kasance ba face Manzon Allah da mazanni suka wuce gabaninsa; kuma uwarsa Siddiqa (mai yawan ba da gaskiya) ce; sun kasance (Isah da Maryama) suna cin abin ci, ka duba yadda ake bayyana musu ayoyi sanann kuma ka duba yadda bijirewa gaskiya”. Ka ce: Shinkuna bautawa wanin Allah abin da ba zai mallaki cuta ko amfani a gare ku ba. Allah shi ne mai ji masani”. (Suratul Ma’ida, aya ta 75-76). Kuma ka ambata masa faxin Allah Ta’ala: Kuma ranar da Allah yake tara su gaba xaya, sannan ya cewa mala’iku: Shin waxannan ku suka kasance suna bautawa? Suka ce tsarki ya tabbata gare ka kai ne majivincinmu basu ba. A’a sun kasance suna bautawa aljanu ne; mafi yawansu dasu (aljanun) suka yi imani.” (Suratul Saba’i, aya ta 40-41).Da faxin Allah Ta’ala “Ka ambata lokacin da Allah ya ce; ya Isah xan Maryama! Shin kaine kace da mutane ku xauke ni da uwata abin buta biyu ba Allah ba? Ya ce tsarki ya tabbata gare ka, ba ya kasancewa a gare in faxi abin da bani da haqqinsa. Idan na faxe shi, to haqiqa ka sani; ka san abin da yake cikin raina amma ban san abin da yake cikin ranka ba. Lalle kaine mai yawan sanin abin da yake voye”. (Suratul Ma’idah, aya ta116).Ka ce masa shin ka san Allah ya kafirta wanda ya nufi gumaka? Kuma ya kafirta wanda ya nufi salihai (da sanin sa), kuma ManzonAllah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yaqe su. Idan ya ce: Ai kafirai suna nufin bauta musu ne, ni kumaina shaida wa lalle Allah shi ne maiamfanarwa kuma shi ne mai cutarwa kuma shi ne mai shirya al’amura, bana neman komai face gare shi. Su kuma salihai basu iya yin komai sai dai ina nufinsu don fatan cetonsu da Allah? To amsa itace: Lalle wannan irin maganar kafirai ce daidai da daidai. Sai ka karanta masa maganar Allah “Waxanda suka riqi wasu majivinta ba shi ba, (suna cewa) ai bama bauta musu sai domin kawai su kusanta mu zuwa ga Allah kusantawa….” (Zumar, Aya 3). Da kuma faxarsa: “Kuma suna cewa waxannan su ne masu ceton mu gurin Allah.” (Yunus Aya 18).Ka sani cewa waxannan shubhohi guda uku sne mafi girman abin da yake gare su. To idan ka san cewa Allah ya bayyana mana su cikin littafinsa kuma ka fahimta mai kyauto abin da yake bayansu ya fi sauqi.Ci gaba zai zo a bugu na gaba inshaAllah.
sahabbai daqaryan da akayimusu
from nura on 08/05/2014 11:51 PM"SAHABA )RAA(, SON KOWA 'KIN WANDA YA RASA")1()MUTACCIYA, KUMA TSINKAKKIYAR SALSALA WACCEHAR KIYAMA TA TSAYA BA ZA KULLU BA(بسم اللهﺍﻟﺤﻤﺪ لله ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﻟﺴﻼﻡ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ص، ﻭﺑﻌﺪ:Kasantuwar maudu'inmu ya shafi 'daya daga cikin manya manyan mazajen Musulunci, wato dayan cikin khalifofin Musulunci, Aliyu bn Abiy Talib r.a wanda bisa kirkira wasu ke kokarin nasabta masa abubuwan da shi ke ya barrantaga barinsu, hakan ya samuka ga dacewa/muhimmancin bayyana gaskiyar lamarin, tare da nuna rashin tabbatar wannan 'barna da masu mafarki ke jingina masa ta hanyar rakkaba kirkirarriyar isnadi izuwa gare shi, da sunar cewa wai ita ce silarsu na abinda suka rika a matsayin addini."TSINKAKKIYAR SALSALA"Mai magana yace:Daga malam ..... shi kuma daga malam .... shi kuma daga Sayyadiy an-Ni'imatu, daga Mustafa Ma'ul Ainayn, daga Muhammad al-Fadhil, daga Maamin, daga Muhammad at-Talib, daga Akhyaaru, daga Il-Jiyhu, daga Muhammad al-Habib, daga Talib Ali, Muhammad bn Yahya as-Sagir, daga Yahya as-Sagir, daga Ahmad Zarruq, daga Ahmad bn Uqbah al-Hadhramiy, daga Abu al-Fathi il-Wafa'iy, daga Shihabuddeen bn Wafa, daga Yahya al-Kabir Ilqadiriy, daga Aliyu Wafa, daga Muhammad Wafa, daga Ibnu Baakhila, daga Ibnu Ata'illah al-Iskandariy, daga Abul Abbas Ahmad al-Mursiy, daga Abul Aqtab Hassan Aliyu ash-Shaziliy, daga AbdusSalam bn Mashish, daga Muhyiddeen Muh'd bn BN Arabiy al-Hatimiy, daga Abul Najib AbdulQadir as-Suhrawardiy,daga Aliyu bn al-Hiytiy, daga Shugaban Waliyyai AbdulQadir al-Jiylaniy, daga Tajul Arifiyna Muhammad Kaakis, daga Muhammad ash-Shanbakiy, daga Abubakar ash-Shibliy, daga Sayyudut-Ta'ifah Sa'id al-Qawaririy)Junaidu(, daga Sarriyyu Mugallisas-Saqtiy, daga**Dawud at-Ta'iy, daga Habib al-Ajamiy, daga al-Hassan al-Basriy, shi kuma daga Shaihinsa Abul Hasanayn, Aliyu bn Abi Talib)ra(.)Dagalittafin: Majmu'u al-Auraad ... pg 46-47(.Allah Ya kyauta, shi dai wannan kirkirarren isnadi an rakkaba shi domin wani dalili, wanda insha Allahu a gaba zamu ambace shi.SAI DAI MAFI DACEWAR SUNARWANNAN DA'AWAR ITA CE"MUTACCIYA, KUMA TSINKAKKIYAR SALSALA, WACCE HAR KIYAMA TA TSAYA BA ZA TA KULLU BA".BAYANAI ZA SU FARO NE DAGA KAN MUTUMIN DA AKA JINGINA MASA DALIBCI WA ALIYU )RA(, WACCE TSINKEWAR TA FARO DAGA BANGARENSA, WANNAN MUTUM SHINE:)1(. AL-HASSAN AL-BASRIY R.H)mutumin kirki(SUNARSA: al-Hassan bn Abiy al-Hassan, Abu Sa'id al-BasriyMAHAIFI: Abu al-Hassan, Yassar)'yan taccen baiwan Zaid bn Thabit al-Ansariy(MAHAIFIYA: Khairah,)'yan tacciyar baiwar Ummu Salamahr.a.a Matar Annabi s.a.w(GARIN HAIHUWA: Madinatul MunawwarahSHEKARAR HAIHUWA: 21 AH)shekaru biyun karshen khalifancin Umarbn al-Khattab r.a(SHEKARA MUTUWA: 1st/Rajab/110 AHGARIN MUTUWA: Basrah, Iraqi.MATSAYI: Tabi'iBAIWARSA: Kasantuwar jatumarsa 'yan tacciyar baiwar Ummul Muminina Ummu Salamah r.a.a ne, idan ta aiketa i zuwa ga wata bukatar da tayi nisa, ya kanyi ke kuka, saboda tausayi Ummu Salamah r.a ta kan dauke shi ta rarrashe shi danononta. Akan hakan, wasu malamai suke ganin albarkacin wannan rarrashi da Ummul Muminina r.a take masa a halin yarantarsa, ya sanya Allah Yayi masa baiwar ilmi mai amfani dazalaqar harshe.Haka kuma, jatumarsa ta kasance ta kan fitoda shi wa Sahabban Annabi)saw( su yi masa addu'a. Daga cikin wadanda ya rabauta da samun addu'arsu, akwai Khalifan Musulunci na biyu Umar 'Dan Khattab )ra(, wanda yayi masa addu'a irinta Waliyyen Allah da fadinsa:" اللهم فقهه في الدين وحببه إلى الناس ".Kuma cikin yardar Allah, wannan du'aina babban waliyyita karbu akan wannan bawan Allah.RAYUWARSA: Babban bawan Allah mutumin kirki, wanda shi ke malami masani, kuma ma'aikaci, kana kuma abin koyi, jagora a zamaninsa. Abu Qatadah al-Adawiy )rh( yace,"ban taba ganin mutum mafi kamanni da Umar )ra( ba kamarHassan".TSINKEWAR SALSALA DA RASHIN TABBATARKARBARSA)....( KAI TSAYE DAGAALIYU)RA(:Tabbas wannan isnadi a wurin managartan maluman Musulunci tsinkakke ne, domin mafi ingancin magana, ita ce duk wata hadisi ko magana da aka riwaito daga Hassanul Basriy r.h kai tsaye zuwa daga Aliyu r.a riwaya ce rarrauna, wacce kai tsaye ka iyakiranta tsinkakkiya. Domin dadai Hassanul Basriy bai taba zamowa daya daga cikin almajiransa wadanda suka karbi ilmi baka-da-baka a wurinsa ba, hasali ma malamai suka ce gani ne kawai tsakaninsu!Hakika maganganu akan riwayarsa daga Aliyu )ra( awurin maluma masana hadisi/mazaje suna shaida hakan, misali:}1{. AL-HAFIZ ABUISA, IMAM AL-TIRMIDHIY R.H :)SUNAAN AL-TIRMIDHIY( wanda bayan ya kawo hadisin a Kitab al-Hudud, sai yace:" ﻭﻻ ﻧﻌﺮﻑ ﻟﻠﺤﺴﻦ ﺳﻤﺎﻋﺎ ﻣﻦ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ رضي الله عنه ... قال أبو عيسى : قد كان الحسن في زمان علي وقد أدركه ولكنا لا نعرف له سماعا منه")DA SHARHIN TUHFATUL AHWADHIY, 4/577-578(.}2{. AL-HAFIZ ABUL HAJJAJ AL-MIZZIY R.H )TAHDHIB AL-KAMAL( :a. Yace:"رأى علي بن أبي طالب وطلحة بن عبيد الله وعائشة، ولم يصح له سماع من أحد منهم"."Ya ga Aliyu bn Abiy Talib da 'Dalha bn Ubaidillahi da A'isha r.a.a, amma bai tabbata ya ji wani abu daga 'dayansu ba".)6/97, trj no; 1216(.b. Ya kawo maganar Hammam bn Yahya:"وقال همامبن يحيى عن قتادة: والله ماحدثنا الحسن عن بدرى مشافهة"."Yace, daga Qatada, yace : Wallahi al-Hassan bai riwaito mana hadisi )da ya ji( baka-da-baka ba daga wani da ya halarciBadr".)6/122(.}3a{. ABU SA'ID, SALAHUDDEENKHALIL BN KAIKALDIY R.H)JAMI'U AL-TAHSIL FI AHKAM AL-MARASIL, Pg 67, trj no: 135( Yace:"فروايته عن أبي بكر وعمر وعثمان رضي الله عنهم من مرساة بلا شك وكذلك عن علي رضي الله عنه ..."}b{. A gaba kadan ya qara da riwayar Imam Ahmad bn Hanbal r.h:"قال شعبة سمعت قتادة يقول : ما شافه الحسن أحد من البدريين الحديث، رواه أحمد عن مؤمل بن إسمائيل عن شعبة..."".... Qatadah yace: al-Hassan bairiwaito hadisi baka-da-baka daga ko mutum daya daga cikin wadanda suka halarci Badr ba,...".}4a{. DHAHABIY R.H )SIYAR( :"وروى عن : عمران بن حصين والمغيرة بن شعبة وعبد الرحمن بن سمرة وسمرة بن جندب وأبي بكرة الثقفي والنعمان بن بشير وجندب البجلي وابن عباس وعمرو ابن تغلب ومعقل بن يسار والأسود بن سريع وأنس وخلق من الصحابة".)4/304(A shafi na gaba ya kara da cewa:"وقد روى بالإرسال عن طائفة : كعلي وأم سلمة ولم يسمع منهما ....""Hakika yayi riwaya da irsali daga wasu jama'a, kamarsu : ALIYU da Ummu Salamah r.a.a alhali sambai ji )wani zance( daga 'dayan biyun ba ....")4/305(Ya kara da fadin:"قال يعقوب بن شيبة: قلت لإبن المديني: يقال عن الحسن: أخذت بحجزةسبعين بدريا. فقال : هذا باطل، أحصيت أهل بدر الذين يُرْوى عنهم، فلم يبلغوا خمسين، منهم المهاجرين أربعة وعشريون".)4/305(}b{. AL-TALKHIS )8/2903(:Bayan Hakeem ya kawo athar din رجم المجنونة na Umar r.a, kafin yakawo hadisin Hassan r.h na رفعالقلم عن ثلاث sai Dhahabiy yace :"صحيح فيه إرسال".}5{. IBN HAJR R.H)TAHDHIB( :"رأى عليا وطلحة وعائشة، وكتب للربيع بن زياد وإلى خراسان في عهد معاوية"."Ya ga Aliyu bn Abiy Talib r.a da'Dalha da A'isha r.a.a....".)2/24(A wani shafin kuma yakarkare zancen da fadinsa:"قلت : سئل أبو زرعة هل سمع الحسن أحد من البدريين؟ قال : رآهم رؤية، رأى عثمان وعليا. قيل: هل سمع منهما حديثا؟ قال : لا، رأى عليا بالمدينة وخرج عليّإلى الكوفة والبصرة، ولم يلقه الحسن بعد ذلك. وقال الحسن : رأيت الزبير يبايععليا. وقال علي بن المديني : لم ير عليا إلا إنكان بالمدينة وهو غلام....")Ibn Hajr( Nace : an tambayi Abu Zur'ah, shin al-Hassan ya ji)wani abu( daga wani daga cikinwadanda suka halartar Badr? Sai yace: ya dai gansu, ya ga Usman da ALIYU. Sai aka ce :Shin ya ji wani hadisi daga gare su? Yace : A'A, Ya dai ga ALIYU aMadina, ALIYU ya fita daga izuwa Kufah da Basrah, kuma bayan wannan lokaci al-Hassan bai sake gamuwa da shi ba. al-Hassan yace : Na ga Zubair yana mubaya'a wa ALIYU. Aliyu bn Madiniy yace : )al-Hassan( bai ta ba ganin ALIYU ba, sai a Madina a lokacin yana 'dan yaro....")2/26(.***WARE ZARE DAGA ABAYAMai karatu zai iya riskar riwayarda al-Hafiz al-Mizziy r.h ya hakaito daga al-Hassan r.h, wacce take nuni da kai tsaye ya karbi ilminsa ne daga Aliyu bn Abiy Talib r.a, wannan riwaya ita ce mafi karfi a wurin masu dogaro da riwayarsa ta bangaren Aliyu r.a.Hikayar kamar yadda tazo a cikin)Tahdhib al-Kamal, 6/124( mai isnadi/matni kamar haka:"وقال ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻣﻮﺳﻰ ﺍﻟﺤﺮﺷﻲ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺛﻤﺎﻣﺔ ﺑﻦ ﻋﺒﻴﺪﺓ, ﻗﺎﻝ: ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﻄﻴﺔ ﺑﻦ ﻣﺤﺎﺭﺏ, ﻋﻦ ﻳﻮﻧﺲ ﺑﻦ ﻋﺒﻴﺪ,ﻗﺎﻝ: ﺳﺄﻟﺖ ﺍﻟﺤﺴﻦ؛ ﻗﻠﺖ : ﻳﺎ ﺃﺑﺎ ﺳﻌﻴﺪ! ﺇﻧﻚ ﺗﻘﻮﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ, ﻭﺇﻧﻚ ﻟﻢ ﺗﺪﺭﻛﻪ? ﻗﺎﻝ : ﻳﺎ ﺍﺑﻦ ﺃﺧﻲ ﻟﻘﺪ ﺳﺄﻟﺘﻨﻲ ﻋﻦ ﺷﻲﺀ ﻣﺎ ﺳﺄﻟﻨﻲ ﻋﻨﻪ ﺃﺣﺪ ﻗﺒﻠﻚ, ﻭﻟﻮﻻ ﻣﻨﺰﻟﺘﻚ ﻣﻨﻲ ﻣﺎﺃﺧﺒﺮﺗﻚ؛ ﺇﻧﻲ ﻓﻲ ﺯﻣﺎﻥ ﻛﻤﺎ ﺗﺮﻯ -ﻭﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺤﺠﺎﺝ - ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﺳﻤﻌﺘﻨﻲ ﺃﻗﻮﻝ ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ؛ ﻓﻬﻮ ﻋﻦ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ, ﻏﻴﺮ ﺃﻧﻲ ﻓﻲ ﺯﻣﺎﻥ ﻻ ﺃﺳﺘﻄﻴﻊ ﺃﻥ ﺃﺫﻛﺮ ﻋﻠﻴﺎ".Sai dai wannan labari yana dauke da illoli, wanda zamu iya daukarbiyu kawai daga ciki mu haska su. Wadannan illoli guda biyu sun hada da :أ. عطية بن محاربWannan mutum da sunarsa haka, ba shi da tarjamaa cikin littafan tarajum na mazaje, domin haka ba za ayi aiki da isnadinsa ba.ب. ثمامة بن عبيدةImam al-Bukhari ya hakaito malaminsa Aliyu bn Madiniy r.hya nasabta shi qarya, a cikin littafinsa )Tarikh al-Kabir, 2/160( a karkashin tarjamar mutum mailamba ta : 2120, yace:ثمامة بن عبيدة العدوى : ضعفه علي، ونسبه إلى الكذب ..."".... Aliyu ya raunan shi, kuma ya nasabta daQARYA ..."Ka ga kuwa riwayar wannan akajefe shi da qarya ba za ayi aiki da ita ba. Wadannan illoli biyu kadai sun ishi mai neman gaskiya ya gane raunin wannan maganar.Insha Allahu a karo na gaba, zamu kara fitar da wasu abubuwa da suke da alaka da wannan qadiyar, tare da kawo sharhi daga maluman kwarai.Wa sallahu ala khairil bariyyati, Nabiyyina Muhammad wa ala Alihi wa Sahbihi Ajma'in.
tarihin maulidi
from nura on 08/05/2014 11:25 PMTARIHIN MAULIDI: Maulidi dai shine taronda ake yi a duk shekara domintunawa daranar da aka haifi Annabi (S.A.W)wandaaka fara shi a karshen Qarni na 6ko kumafarkon qarni na 7, wato shekaru600-700Bayan Hijira, Ma'ana bayanSahabbai da tabi'ai, databi'ittabi'ina! Wadanda sukafara Maulidi sune YanFADIMIYYUN watoYan shi'a a kasar Masar, wadandasukakashe Malamai Ahlus sunnahsama da4000, saboda kawai suna cewaSahaabbai(R.A). Daga nan sai sarkin IRBILAl- Mudhaffar Abu Sa'eedKawkaboory. Dalilinrashin asali na shari'a da Maulidiyake da shi a Addini shi yasa dayawa dagacikin Malamai suka yi Inkari da shi,kadandaga cikin Malaman MALIKIYYAakwai:1-Abu Ishaq Asshadibi (Al-i'itisam)2-Imamu Tajuddeenil Fakheehani(Al-maurid fil kalami alal Maulid)3-Abu Abdullahi Muhammad Illish(FathulAliyil Malik)4-Muhammad Ibn Ali Abu Abdullahal-affar5-Shehu Usman Bn Fodio. Da daisauran su. Wanda ya bashi kariyama shine ImamuSuyidi, wanda ya ce BID'AH ceamma maikyau, sai dai shima Malamai ba susallamamasa ba domin Annabi yace"DukkaninBID'AH bata ce" Haka a cikinlittafinIbrahim Nyass mai sunaTAFSIRUL ANAM FI ANNAL ILMIHUWAL IMAM yayi bayani indaya ce ba wata BID'AH hasana akarshenlittafin. MENENE SON ANNABI?Shin yinMaulidishine alamar Son Annabi??? Kokadan bazai zama haka ba, dalili kuwashine kowa ya yarda cewaSahabbai da magabataNagarisun fi mu son Annabi nesaba kusaba. Amma sunyi maulidi? Hasalimadukkanin mafiya alkhairin al-ummawadanda suka rayu a Qurunulmufaddhalaba su ma san shi ba balle su yi shi,Shin Addinin su ya cika ko ko dasaura tunda basu yi maulidi ba? Sannan awannan zamanibabu littafin damuke ji da shi wanda ya bayyanaso dakauna na manzon Allah kamarlittafinAshafa na Alkadhi Iyadh shin yayiBABI a kan Maulud?KAMMALAWA: Duk litattafanda muke dasu Ban taba gani ko ji cewa gaBABI akanMaulidi ba. Shin sun sani ne sukaboye?Shin Ilimin su ne bai kai ba?Shin Maulidi ba Addini ba ne?
tarihin maulidi
from nura on 08/05/2014 11:24 PMTARIHIN MAULIDI: Maulidi dai shine taronda ake yi a duk shekara domintunawa daranar da aka haifi Annabi (S.A.W)wandaaka fara shi a karshen Qarni na 6ko kumafarkon qarni na 7, wato shekaru600-700Bayan Hijira, Ma'ana bayanSahabbai da tabi'ai, databi'ittabi'ina! Wadanda sukafara Maulidi sune YanFADIMIYYUN watoYan shi'a a kasar Masar, wadandasukakashe Malamai Ahlus sunnahsama da4000, saboda kawai suna cewaSahaabbai(R.A). Daga nan sai sarkin IRBILAl- Mudhaffar Abu Sa'eedKawkaboory. Dalilinrashin asali na shari'a da Maulidiyake da shi a Addini shi yasa dayawa dagacikin Malamai suka yi Inkari da shi,kadandaga cikin Malaman MALIKIYYAakwai:1-Abu Ishaq Asshadibi (Al-i'itisam)2-Imamu Tajuddeenil Fakheehani(Al-maurid fil kalami alal Maulid)3-Abu Abdullahi Muhammad Illish(FathulAliyil Malik)4-Muhammad Ibn Ali Abu Abdullahal-affar5-Shehu Usman Bn Fodio. Da daisauran su. Wanda ya bashi kariyama shine ImamuSuyidi, wanda ya ce BID'AH ceamma maikyau, sai dai shima Malamai ba susallamamasa ba domin Annabi yace"DukkaninBID'AH bata ce" Haka a cikinlittafinIbrahim Nyass mai sunaTAFSIRUL ANAM FI ANNAL ILMIHUWAL IMAM yayi bayani indaya ce ba wata BID'AH hasana akarshenlittafin. MENENE SON ANNABI?Shin yinMaulidishine alamar Son Annabi??? Kokadan bazai zama haka ba, dalili kuwashine kowa ya yarda cewaSahabbai da magabataNagarisun fi mu son Annabi nesaba kusaba. Amma sunyi maulidi? Hasalimadukkanin mafiya alkhairin al-ummawadanda suka rayu a Qurunulmufaddhalaba su ma san shi ba balle su yi shi,Shin Addinin su ya cika ko ko dasaura tunda basu yi maulidi ba? Sannan awannan zamanibabu littafin damuke ji da shi wanda ya bayyanaso dakauna na manzon Allah kamarlittafinAshafa na Alkadhi Iyadh shin yayiBABI a kan Maulud?KAMMALAWA: Duk litattafanda muke dasu Ban taba gani ko ji cewa gaBABI akanMaulidi ba. Shin sun sani ne sukaboye?Shin Ilimin su ne bai kai ba?Shin Maulidi ba Addini ba ne?
ya mahadi
from nura on 08/02/2014 10:11 AMYA MAHDI!!!!!!!!!************************Wannan itace Kalmar da ta RiqaFitowa daga Bakin Masu Zanga-Zanga Mabiya Addinin Shi'a.Abin Lura anan Shine Wanene ya Bude Musu Wuta??Mahdin nan nasu dai dama DanDa'adda ne domin Ruwayoyin Addinin Shi'a Sun tabbata Cewa;Da Mutane Sun San Sharrinsa da bazasu Ta6a Fatan Baiyanar Shi ba,An Sami Ruwaya Daga Limamin Shi'a Jafarus Sadiq cewa:لو يعلم الناس ما يصنع القائم إذا خرج لأحب أكثرهم أن لا يروه مما يقتل من الناس، أما إنه لا يبدأ إلا بقريش فلا يأخذ منها إلا السيف ولا يعطيها إلا السيف حتى يقول كثير من الناس: ليسهذا من آل محمد لو كان من آل محمد لرحمWallahi da Mutane Sun San irin)Ta'addancin( Da Kisan Qare dangi da Mahdi zai aikata Idan ya Baiyana Da Mutane Basu yi Gurin Baiyanarshi ba. Kuma bazai fara da kowa na Sai da Kuraishawa )Dangin Annabi(, Babu abinda Zai Shiga tsakaninsu Sai Tokobi Har Mutane zasu Rinka cewa: Kai wannan dai baya Cikin Iyalan Annabi da yana Cikin Iyalan Annabi da ya tausaya.Duba Ilzamun-nasib 2/247.Don Haka Mahdin nan Dai Shine yazo a Sifar Sojoji ya budema 'ya'yan Zakzaki Wuta.Ina Gauga'un da ake Yaudara ana Rabasu da Kiran Allah a Wajen Neman Agaji?Ku kiyayi Kiran Wannan Mugun Kungani da irin Halinda ya Jefa Zakzaki.

Reply